YouVersion Logo
Search Icon

Nah 2

2
1Wanda yake farfashewa ya auko
maka,
Sai ka sa mutane a kagara, a yi
tsaron hanya,
Ka yi ɗamara, ka tattaro ƙarfinka
duka.
2Gama Ubangiji zai mayar wa
Yakubu da darajarsa kamar ta
Isra'ila.
Ko da masu washewa sun washe su,
Sun kuma lalatar da rassan inabinsu.
3Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne,
Sojojinsa kuma suna saye da mulufi.
Da ya shirya tafiya,
Karusai suna walƙiya kamar
harshen wuta,
Ana kaɗa mashi da bantsoro.
4Karusai sun zabura a tituna a
haukace.
Suna kai da kawowa a dandali,
Suna walwal kamar jiniya,
Suna sheƙawa a guje kamar
walƙiya.
5Sai aka kira shugabanni,
Suka zo a guje suna tuntuɓe,
Suka gaggauta zuwa garu,
Suka kafa kagara.
6An buɗe ƙofofin kogi,
Fāda ta rikice.
7An tsiraita sarauniya, an tafi da ita,
'Yan matanta suna makoki, suna
kuka kamar kurciyoyi,
Suna bugun ƙirjinsu.
8Nineba tana kama da tafki wanda
ruwansa yake zurarewa,
Suna cewa, “Tsaya, tsaya,”
Amma ba wanda ya waiga.
9A washe azurfa!
A washe zinariya!
Dukiyar ba ta da adadi,
Akwai dukiya ta kowane iri.
10Nineba ta halaka! ta lalace, ta zama
kufai!
Zukata sun narke, gwiwoyi suna
kaɗuwa!
Kwankwaso yana ciwo,
Fuskoki duka sun kwantsare!
11Ina kogon nan na zakoki,
Inda aka ciyar da 'ya'yan zaki,
Inda zaki da zakanya da
kwiyakwiyansu sukan tafi,
Su tsere daga fitina?
12Zaki ya kashe abin da ya ishi
kwiyakwiyansa.
Ya kaso wa zakanyarsa abin da ya
ishe ta.
Ya cika kogonsa da ganima.
Ragargajewar Nineba
13“Ga shi, ina gāba da ke. Ni Ubangiji
Allah Mai Runduna na faɗa.
Zan ƙone karusanki,
Takobi kuwa zai karkashe sagarun
zakokinki,
Zan hana miki ganima a duniya.
Ba za a ƙara jin muryoyin jakadunki
ba.”

Currently Selected:

Nah 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in