YouVersion Logo
Search Icon

Mat 15

15
Al'adun Shugabanni
(Mar 7.1-13)
1Waɗansu Farisiyawa da malaman Attaura suka zo wurin Yesu daga Urushalima, suka ce, 2“Don me almajiranka suke keta al'adun shugabanni? Domin ba sa wanke hannu kafin su ci abinci.” 3Sai ya amsa musu ya ce, “Ku kuma don me kuke keta umarnin Allah saboda al'adunku? 4#Fit 20.12; M.Sh 5.16; Fit 21.17; L.Fir 20.9 Domin Allah ya yi umarni ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa lalle a kashe shi.’ 5Amma ku kukan ce, ‘Kowa ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni an ba Allah,” to, ba lalle ya girmama ubansa ba ke nan.’ 6Wato, saboda al'adunku kun bazanta Maganar Allah. 7Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, da ya ce,
8 # Ish 29.13 “ ‘Al'ummar nan a baka kawai suke girmama ni,
Amma a zuci nesa suke da ni.
9A banza suke bauta mini,
Don ka'idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.’ ”
Abubuwan da Suke Ƙazantarwa
(Mar 7.14-23)
10Ya kira taro ya ce musu, “Ku saurara, ku fahimta. 11Ba abin da yake shiga mutum ta baka ne yake ƙazanta shi ba, abin da yake fita ta baka yake ƙazanta mutum.” 12Sai almajiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisiyawa sun ji haushi da suka ji maganan nan?” 13Ya amsa ya ce, “Duk dashen da ba Ubana da yake Sama ne ya dasa ba, za a tumɓuke shi. 14#Luk 6.39 Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.” 15Amma Bitrus ya ce masa, “A yi mana fassarar misalin nan.” 16Yesu ya ce, “Ku ma, ashe, har yanzu ba ku fahimta? 17Ashe, ba ku gane ba, kome ya shiga mutum ta baka, cikinsa ya shiga, ta haka kuma zai fice? 18#Mat 12.34 Amma abin da ya fito ta baka, daga zuci yake, shi ne kuwa yake ƙazantar da mutum. 19Don daga zuci mugayen tunani suke fitowa, kamar su kisankai, da zina, da fasikanci, da sata, da shaidar zur, da yanke. 20Waɗannan suke ƙazantar da mutum. Amma a ci da hannu marar wanki ba ya ƙazantar da mutum.”
Bangaskiyar Mace Bakan'aniya
(Mar 7.24-30)
21Yesu ya tashi daga nan, ya tafi zuwa ƙasar Taya da Sidon. 22Ga wata Bakan'aniya mutuniyar ƙasar, ta zo, ta ɗaga murya ta ce, “Ya Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina. Wani aljani ya bugi 'yata, ba yadda take.” 23Amma bai ce da ita kanzil ba. Sai almajiransa suka zo suka roƙe shi, suka ce, “Sallame ta mana, tana binmu tana cika mana kunne da kuka.” 24Ya amsa ya ce, “Ni wurin ɓatattun tumakin jama'ar Isra'ila kaɗai aka aiko ni.” 25Amma ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ya Ubangiji, ka taimake ni mana!” 26Ya amsa ya ce, “Ai, bai kyautu a bai wa karnuka abincin 'ya'ya ba.” 27Sai ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.” 28Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Kai, uwargida, bangaskiyarki da yawa take! Yă zamar miki yadda kike so.” Nan take 'ya tata ta warke.
Yesu Ya Warkar da Mutane Masu Yawa
29Yesu ya tashi daga nan, ya bi ta bakin Tekun Galili. Sai ya hau dutse ya zauna a can. 30Taro masu yawan gaske suka zo wurinsa, suka zazzo da guragu, da masu dungu, da makafi, da bebaye, da kuma waɗansu da yawa, suka ajiye su a gabansa, ya kuwa warkar da su. 31Har jama'ar suka yi ta al'ajabi da ganin bebaye suna magana, masu dungu sun sami gaɓoɓinsu, guragu na tafiya, makafi kuma suna gani, duk suka ɗaukaka Allah na Isra'ila.
Ciyar da Mutum Dubu Huɗu
(Mar 8.1-10)
32Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa so in sallame su da yunwa haka, kada su kasa a hanya.” 33Sai almajiran suka ce masa, “Ina za mu samo gurasa a jeji haka da za ta isa ciyar da ƙasaitaccen taro haka?” 34Yesu ya ce musu, “Gurasa nawa suke gare ku?” Suka ce, “Bakwai, da ƙananan kifaye kaɗan.” 35Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa. 36Da ya ɗauki gurasa bakwai ɗin da kifayen nan, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiran, almajiran kuma na, bai wa jama'a. 37Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai. 38Waɗanda suka ci kuwa maza dubu huɗu ne, banda mata da yara. 39Da ya sallami taron ya shiga jirgi ya tafi ƙasar Magadan.

Currently Selected:

Mat 15: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in