MAL 4
HAU
4
Ranar Ubangiji Mai Zuwa
1 # Yow 2.31; Ish 5.24; Oba 1.18 “Duba rana tana zuwa, sa'ad da dukan masu girmankai, da mugaye za su ƙone kamar tattaka, a ran nan za su ƙone ƙurmus ba abin da zai ragu, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa. 2#Luk 1.78; Afi 5.14; Ish 30.26; Ish 35.6 Amma ku da kuke yi mini biyayya, ikon cetona zai fito muku kamar rana. Zai kawo warkarwa kamar hasken rana. Za ku fita kuna tsalle kamar 'yan maruƙan da aka fisshe su daga garke. 3#Ayu 40.12; Eze 28.18 Za ku tattake mugaye, gama za su zama kamar ƙura a ƙarƙashin ƙafafunku, a ranan nan da zan aikata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
4 # Zab 147.19 “Ku tuna da koyarwar bawana Musa, da dokoki, da umarnai waɗanda na ba shi a kan Dutsen Horeb, domin dukan jama'ar Isra'ila su kiyaye.
5 # Mat 11.14; Yow 2.31 “Ga shi, zan aiko muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji ta zo. 6#Luk 1.17; Ish 11.4; W.Yah 19.15; Zak 5.3 Zai sāke kawo iyaye da 'ya'ya wuri ɗaya, da ba don haka ba, da sai in zo in hallaka ƙasar.”

Bible Society of Nigeria © 1932/2010

Learn More About Littafi Mai Tsarki