YouVersion Logo
Search Icon

L.Fir 9

9
Haruna ya Miƙa Hadayu
1A kan rana ta takwas, Musa ya kirawo Haruna, da 'ya'yansa maza, da dattawan Isra'ila. 2Sai ya ce wa Haruna, “Kawo ɗan maraƙi marar lahani na yin hadaya don zunubi, da rago marar lahani don hadaya ta ƙonawa, ka miƙa su ga Ubangiji. 3Ka faɗa wa Isra'ilawa su ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi, da ɗan maraƙi bana ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya marasa lahani, don hadaya ta ƙonawa, 4da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.”
5Sai suka kawo abin da Musa ya umarce su a gaban alfarwa ta sujada. Dukan taron jama'a suka matso kusa, suka tsaya a gaban Ubangiji. 6Musa kuma ya ce, “Ubangiji ya umarce ku ku yi dukan wannan, domin ɗaukakar Ubangiji za ta bayyana gare ku.” 7#Ibr 7.27 Sa'an nan Musa ya ce wa Haruna, “Matsa kusa da bagaden, ka miƙa hadayarka don zunubi, da hadayarka ta ƙonawa, ka yi kafara don kanka da kuma don jama'a. Ka kuma kawo hadayar jama'a, ka yi kafara dominsu kamar yadda Ubangiji ya umarta.”
8Sai Haruna ya matsa kusa da bagaden, ya yanka ɗan maraƙi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. 9'Ya'yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya tsoma yatsansa a cikin jinin, ya shafa a zankayen bagaden, ya kuma zuba jinin a gindin bagaden. 10Amma kitsen, da ƙodojin, da kitsen da yake rufe da hanta na hadaya don zunubi, ya ƙone su a bisa bagaden kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. 11Naman da fatar kuwa ya ƙone su a bayan zangon.
12Haruna ya yanka hadaya ta ƙonawa, 'ya'yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa a bagaden da kewayensa. 13Suka kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa gunduwa gunduwa tare da kan, sai ya ƙone su bisa bagaden. 14Ya kuma wanke kayan ciki, da ƙafafu, sa'an nan ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden.
15Haruna kuma ya miƙa hadayar jama'a. Ya ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi jama'ar, ya yanka, ya miƙa shi hadaya don zunubi kamar yadda aka yi da na farin. 16Ya kuma miƙa hadaya ta ƙonawa, ya yi kamar yadda aka faɗa. 17Ya kuma kawo hadaya ta gari, ya ɗibi garin cike da tafin hannunsa, ya ƙone shi a bisa bagaden tare da hadaya ta ƙonawa ta safiya. 18#L.Fir 3.1-11 Sai kuma ya yanka bijima da rago don yin hadayun salama domin jama'ar. 'Ya'yansa maza suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa. 19Suka cire kitsen bijimin, da na ragon, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, da ƙodoji, da matsarmama. 20Sai Haruna ya aza kitsen a bisa ƙirjin dabbobin ya ƙone kitsen a bisa bagaden. 21Amma ya yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin da cinyoyi na dama ga Ubangiji, kamar yadda Musa ya umarta.
22 # L.Ƙid 6.22-26 Sai Haruna ya ta da hannuwansa wajen jama'a, ya sa musu albarka sa'an nan ya sauka daga wurin yin hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa, da hadayun salama. 23Musa da Haruna suka shiga alfarwa ta sujada. Da suka fita, sai suka sa wa jama'a albarka. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana ga jama'a duka. 24Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta ƙone hadaya ta ƙonawa da kitsen a bisa bagaden. Da jama'a duka suka gani, suka yi ihu, suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada.

Currently Selected:

L.Fir 9: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in