L.Fir 18
18
An Haramta yin Lalata
1Ubangiji kuma ya ce wa Musa 2ya faɗa wa mutanen Isra'ila cewa, “Ni ne Ubangiji Allahnku. 3Kada ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan'ana inda nake kai ku. Kada ku kiyaye dokokinsu. 4Amma ku bi ka'idodina, ku yi tafiya a cikinsu, gama ni ne Ubangiji Allahnku. 5#Neh 9.29; Eze 18.9; 20.11-13; Luk 10.28; Rom 10.5; Gal 3.12 Domin haka sai ku kiyaye dokokina da ka'idodina waɗanda ta wurin kiyaye su mutum zai rayu. Ni ne Ubangiji.”
6Ubangiji ya ba da waɗannan ka'idodi kuma. Kada kowane mutum ya kusaci 'yar'uwarsa don ya kwana da ita. Ya ce, “Ni ne Ubangiji.” 7Kada ya ƙasƙantar da mahaifinsa, wato, kada ya kwana da mahaifiyarsa, kada ya ƙasƙantar da mahaifiyarsa. 8#L.Fir 20.11; M.Sh 22.30; 27.20 Kada ya kwana da matar mahaifinsa, gama ita matar mahaifinsa ce. 9#L.Fir 20.17; M.Sh 27.22 Kada ya kwana da 'yar'uwarsa, 'yar mahaifinsa, ko 'yar mahaifiyarsa, ko a gida ɗaya aka haife ta da shi, ko a wani gida dabam. 10Kada ya kwana da jikanyarsa gama zai zama ƙasƙanci a gare shi. 11Kada ya kwana da 'yar matar mahaifinsa, wadda mahaifinsa ya haifa, tun da yake ita 'yar'uwarsa ce. 12#L.Fir 20.19,20 Kada ya kwana da bābarsa gama 'yar'uwar mahaifinsa ce. 13Kada ya kwana da innarsa, gama ita 'yar'uwar mahaifiyarsa ce. 14Kada ya kwana da matar ɗan'uwan mahaifinsa, gama ita ma bābarsa ce. 15#L.Fir 20.12 Kada ya kwana da matar ɗansa, gama ita surukarsa ce. 16#L.Fir 20.21 Kada ya kwana da matar ɗan'uwansa, gama ita matar ɗan'uwansa ce. 17#L.Fir 20.14; M.Sh 27.23 In ya kwana da mace, kada kuma ya kwana da 'yarta, ko jikanyarta, wannan duk haramun ne, gama su danginsa ne na kusa. 18Muddin matarsa tana da rai, ba zai auro ƙanwarta ta zama kishiyarta ba.
19 #
L.Fir 20.18
Kada ya kwana da mace a lokacin hailarta, gama ba ta da tsarki. 20#L.Fir 20.10 Kada ya kwana da matar maƙwabcinsa don kada ya ƙazantar da kansa. 21#L.Fir 20.1-5 Kada ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa don a miƙa wa Molek, gama yin haka zai ƙasƙantar da sunan Allah. Shi Ubangiji ne. 22#L.Fir 20.13 Kada ya yi luɗu, gama Allah yana ƙin wannan. 23#Fit 22.19; L.Fir 20.15,16; M.Sh 27.21 Kada wani ko wata su kwana da dabba don kada su wofintar da kansu.
24Kada su ƙazantar da kansu da irin waɗannan abubuwa, gama da irin waɗannan abubuwa ne al'umman da Ubangiji yake kora a gabansu suka ƙazantar da kansu. 25Har ƙasar ma ta ƙazantu, don haka Ubangiji ya hukunta muguntarta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta. 26Amma su sai su kiyaye dokokin Ubangiji da ka'idodinsa. Kada su aikata ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa na banƙyama, ko haifaffe na gida, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu. 27Gama mazaunan ƙasar da suka riga su, sun aikata dukan abubuwa masu banƙyaman nan, don haka ƙasar ta ƙazantu. 28Kada kuma ƙasar ta amayar da su idan sun ƙazantar da ita, kamar yadda ta amayar da al'ummar da ta riga su zama a cikinta. 29Duk wanda ya aikata abu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa masu banƙyaman nan za a raba shi da jama'a.
30Ubangiji kuma ya ce, “Don haka sai ku kiyaye umarnina, kada ku kiyaye dokoki na banƙyama waɗanda aka kiyaye kafin ku zo, kada ku ƙazantu da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
Currently Selected:
L.Fir 18: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979