YouVersion Logo
Search Icon

Josh 9

9
Munafuncin Gibeyonawa
1Sa'ad da dukan sarakunan da suke hayin Urdun, na cikin ƙasar tuddai, da na ƙasar kwari a gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon, wato sarakunan Hittiyawa, da na Amoriyawa, da na Kan'aniyawa, da na Ferizziyawa, da na Hiwiyawa, da na Yebusiyawa, suka ji wannan labari, 2sai suka tattaru, suka haɗa kansu domin su yaƙi Joshuwa da Isra'ilawa.
3Amma da mazaunan Gibeyon suka ji abin da Joshuwa ya yi wa Yariko da Ai, 4sai suka yi musu hila, suka shirya guzuri, suka ɗauki tsofaffin buhuna a kan jakunansu da tsofaffin salkuna na ruwan inabi, yagaggu, sun kuwa sha ɗinki. 5Suka kuma sa tsofaffin takalma waɗanda suka sha gyara, da tsofaffin tufafi. Dukan guzurinsu ya bushe, ya yi fumfuna. 6Suka tafi wurin Joshuwa da Isra'ilawa a zango a can Gilgal, suka ce musu, “Daga ƙasa mai nisa muka fito, yanzu fa, sai ku yi alkawari da mu.”
7 # Fit 23.32; 34.12; M.Sh 7.2 Amma Isra'ilawa suka ce wa Hiwiyawa, “Watakila kuna zaune a tsakiyarmu ne, to, ƙaƙa za mu yi muku alkawari?”
8Su kuwa suka ce wa Joshuwa, “Mu bayinka ne.”
Joshuwa kuwa ya ce musu, “Su wane ne ku? Daga ina kuka zo kuma?”
9Suka amsa masa suka ce, “Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka, gama mun ji labarinsa da dukan abin da ya yi a Masar, 10#L.Ƙid 21.21-35 da dukan abin da ya yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon, Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake a Ashtarot. 11Dattawanmu da dukan mazaunan ƙasarmu suka ce mana mu ɗauki guzuri a hannunmu don tafiya, mu tafi taryarku, mu ce muku, ‘Mu bayinku ne, yanzu dai sai ku yi mana alkawari.’ 12Wannan abinci, da ɗuminsa muka ɗauko shi daga gidajenmu a ranar da muka fito zuwa gare ku, amma ga shi, yanzu ya bushe ya yi fumfuna. 13Waɗannan salkunan ruwan inabi kuma da muka cika sababbi ne, amma ga shi, sun kyakkece, waɗannan tufafinmu kuma da takalmanmu sun tsufa saboda tsawon hanya!” 14Sai Isra'ilawa suka ɗiba daga cikin guzurin Hiwiyawa, amma ba su nemi shawara wurin Ubangiji ba. 15Joshuwa kuwa ya yi amana da su, ya yi musu alkawari zai bar su da rai. Shugabannin jama'a kuma suka rantse musu.
16Amma a rana ta uku bayan da suka yi alkawari da su, suka ji cewa, su maƙwabtansu ne, suna zaune a cikinsu. 17Sai Isra'ilawa suka kama hanyarsu a rana ta uku suka isa biranen mutanen, wato Gibeyon, da Kefira, da Biyerot, da Kiriyat-yeyarim. 18Amma Isra'ilawa ba su kashe su ba, domin shugabannin jama'a sun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila. Dukan jama'a kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin. 19Amma shugabanni suka ce wa dukan jama'a, “Mun riga mun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila, don haka yanzu ba shi yiwuwa mu taɓa su. 20Abin da za mu yi musu ke nan, a bar su da rai saboda rantsuwar da muka rantse musu don kada mu jawo wa kanmu fushin Ubangiji!” 21Suka ƙara da cewa, “A bar su da rai domin su zama masu sarar mana itace, da masu ɗebo mana ruwa.”
22Joshuwa kuwa ya kirawo su, ya ce musu, “Me ya sa kuka ruɗe mu da cewa, ‘Muna nesa da ku ƙwarai,’ ga shi kuwa, a tsakiyarmu kuke zaune? 23Yanzu fa ku la'anannu ne, a cikinku ba za a rasa bayin da za su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin masujadar Allahnmu ba.”
24Sai suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Domin bayinka sun ji labari Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa ya ba ku ƙasar duka, ku hallaka dukan mazaunan ƙasar a gabanku, don haka muka ji tsoronku ƙwarai saboda rayukanmu, shi ya sa muka yi haka. 25Yanzu dai muna a hannunka, ka yi yadda ka ga ya yi maka kyau.” 26Haka kuwa ya yi musu, ya cece su daga hannun Isra'ilawa, har ba su kashe su ba. 27Amma Joshuwa ya sa su su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin jama'a da bagaden Ubangiji. Zai zama aikinsu na yau da kullum a wurin da Ubangiji zai zaɓa.

Currently Selected:

Josh 9: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in