YouVersion Logo
Search Icon

Josh 7

7
Zunubin Akan
1Amma Isra'ilawa suka ci amana, gama Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza ya ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.
2Joshuwa kuma ya aiki mutane daga Yariko zuwa Ai wadda take kusa da Betawen gabashin Betel, ya ce musu, “Ku tafi ku leƙi asirin ƙasar.” Sai mutanen suka tafi, suka leƙo asirin Ai.
3Da suka komo wurin Joshuwa, sai suka ce masa, “Kada dukan mutane su tafi, amma a bar mutum wajen dubu biyu ko uku su tafi su bugi Ai, kada a sa dukan mutane su sha wahalar zuwa can, domin su kima ne.” 4Sai mutum wajen dubu uku daga cikin jama'a suka tafi, amma mutanen Ai suka kore su. 5Mutanen Ai suka kashe mutum wajen talatin da shida daga cikin Isra'ilawa, suka runtume su tun daga ƙofar garin har zuwa Shebarim, suka yi ta karkashe su har zuwa gangaren. Zukatan mutanen Isra'ila kuwa suka narke, suka zama kamar ruwa.
6Sai Joshuwa ya yayyage tufafinsa, ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin Ubangiji har yamma. Shi da dattawan Isra'ila, suka zuba ƙura a bisa kansu. 7Joshuwa ya ce, “Kaitonmu, ya Ubangiji Allah, me ya sa ka haye da jama'an nan zuwa wannan hayin Urdun, don ka bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallakar da mu? Da ma mun haƙura, mun yi zamanmu a wancan hayin Urdun. 8Ya Ubangiji, me zan ce bayan da Isra'ilawa sun ba da baya ga abokan gābansu? 9Gama Kan'aniyawa da dukan mazaunan ƙasar za su ji labari, su kewaye mu, su shafe sunanmu daga duniya, to, me za ka yi don sunanka mai girma?”
10Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Tashi, don me ka fāɗi rubda ciki? 11Isra'ilawa sun yi zunubi. Sun ta da alkawarina, wanda na umarce su, gama sun ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, sun sa a kayansu, sun yi ƙarya. 12Saboda haka Isra'ilawa ba su iya tsayawa a gaban abokan gābansu ba, sun ba da baya ga abokan gābansu, gama sun zama haramtattu don hallakarwa. Daɗai, ba zan kasance tare da ku ba, sai dai kun kawar da haramtattun abubuwa da suke cikinku. 13Tashi, ka tsarkake jama'a, ka ce, ‘Ku tsarkake kanku domin gobe, gama Ubangiji, Allah na Isra'ila ya ce akwai haramtattun abubuwa a tsakiyarku. Ya Isra'ila, ba ku iya tsayawa a gaban abokan gābanku ba, sai kun kawar da haramtattun abubuwa daga tsakiyarku. 14Da safe kuwa za a gabatar da ku kabila kabila, zai zama kuwa kabilar da Ubangiji ya ware, za a gabatar da ita iyali iyali, iyalin da Ubangiji ya ware kuma, za a gabatar da su gida gida, gidan kuma da Ubangiji ya ware, za a gabatar da su mutum mutum. 15Zai zama kuwa wanda aka same shi da haramtattun abubuwa, za a ƙone shi da wuta, shi da dukan abin da yake da shi, domin ya tā da alkawarin Ubangiji, ya kuma yi abin kunya cikin Isra'ila.’ ”
16Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, ya gabatar da Isra'ilawa kabila kabila, aka ware kabilar Yahuza. 17Ya gabatar da iyalan Yahuza, aka ware iyalin Zera. Ya gabatar da iyalin Zera gida gida, aka ware gidan Zebdi. 18Ya gabatar da iyalin gidansa mutum mutum, aka ware Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza. 19Sai ya ce wa Akan, “Ɗana, ka ba da girma ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka yabe shi ka gaya mini abin da ka yi, kada ka ɓoye mini.”
20Akan kuwa ya amsa wa Joshuwa, ya ce, “A gaskiya kam, na yi wa Ubangiji, Allah na Isra'ila zunubi. Ga abin da na yi. 21A cikin kayan ganimar na ga wata kyakkyawar alkyabba irin ta Shinar, da shekel dari biyu na azurfa, da sandan zinariya mai nauyin shekel hamsin, sai na yi ƙyashi, na kwashe su, ga su a binne a ƙasa a alfarwata da azurfa a ƙarƙashi.”
22Joshuwa ya aika da manzanni, suka sheƙa a guje zuwa alfarwar, suka tarar da abubuwan a binne cikin alfarwarsa da azurfa a ƙarƙashi. 23Sai suka kwaso suka kawo wa Joshuwa da dukan Isra'ilawa, suka ajiye su a gaban Ubangiji. 24Joshuwa kuwa tare da dukan Isra'ilawa suka ɗauki Akan, ɗan Zera, da azurfar, da alkyabbar, da sandan zinariya, da 'ya'yansa mata da maza, da shanunsa, da jakunansa, da tumakinsa, da alfarwarsa, da dukan abin da yake da shi, suka kawo su a Kwarin Akor. 25Sai Joshuwa ya ce, “Don me ka wahalshe mu? Kai ma, Ubangiji zai wahalshe ka yau!” Dukan Isra'ilawa suka jajjefe su da duwatsu, suka ƙone su da wuta. 26Suka tara tsibin duwatsu a kansu. Tsibin duwatsun kuwa yana nan har wa yau. Sa'an nan Ubangiji ya huce daga zafin fushinsa. Domin haka ana kiran wurin Kwarin Akor, wato azaba, har wa yau.

Currently Selected:

Josh 7: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in