YouVersion Logo
Search Icon

Josh 21

21
Biranen da Aka Ba Lawiyawa
(1Tar 6.54-81)
1Shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa suka zo wurin Ele'azara, firist, da wurin Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan jama'ar Isra'ila. 2#L.Ƙid 35.1-8 Suka yi magana da su a Shilo a ƙasar Kan'ana, suka ce musu, “Ubangiji ya umarta ta bakin Musa a ba mu biranen zama da wuraren kiwo domin dabbobinmu.” 3Bisa ga umarnin Ubangiji, sai jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa waɗannan birane da wuraren kiwo daga cikin gādonsu.
4Kuri'a ta faɗo a kan iyalan Kohatawa. Sai Lawiyawa na zuriyar Haruna firist suka karɓi birane goma sha uku daga kabilar Yahuza, da kabilar Saminu, da kabilar Biliyaminu.
5Sauran Kohatawa suka karɓi birane goma daga iyalan kabilar Ifraimu, da kabilar Dan, da rabin kabilar Manassa.
6Gershonawa kuwa suka karɓi birane goma sha uku ta hanyar jefa kuri'a daga iyalan kabilar Issaka, da kabilar Ashiru, da kabilar Naftali, da rabin kabilar Manassa a Bashan.
7Sai Merariyawa bisa ga iyalansu suka karɓi birane goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da ta Zabaluna.
8Waɗannan birane da wuraren kiwo nasu su ne jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa ta hanyar jefa kuri'a kamar yadda Ubangiji ya umarta ta bakin Musa.
9Daga cikin kabilar Yahuza da kabilar Saminu aka ba zuriyar Haruna waɗannan birane da aka ambata. 10Zuriyar Haruna tana cikin iyalan Kohatawa waɗanda suke Lawiyawa. Kuri'arsu ce ta fito da farko. 11Sai aka ba su Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar tuddai ta Yahuza tare da wuraren kiwo nata da suke kewaye. Arba shi ne mahaifin Anak. 12Amma saurukan birnin da ƙauyukansu an ba Kalibu, ɗan Yefunne, su zama mallakarsa.
13Biranen da aka ba zuriyar Haruna firist ke nan, Hebron tare da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Libna tare da wuraren kiwo nata, 14da Yattir tare da wuraren kiwo nata, da Eshtemowa tare da wuraren kiwo nata, 15da Holon tare da wuraren kiwo nata, da Debir tare da wuraren kiwo nata, 16da Ayin tare da wuraren kiwo nata, da Yutta tare da wuraren kiwo nata, da Bet-shemesh tare da wuraren kiwo nata. Birane tara ke nan daga cikin kabilun nan biyu. 17Daga cikin kabilar Biliyaminu aka ba su birane huɗu, wato Gibeyon tare da wuraren kiwo nata, da Geba tare da wuraren kiwo nata, 18da Anatot tare da wuraren kiwo nata, da Almon tare da wuraren kiwo nata. 19Dukan biranen da aka ba firistoci, wato zuriyar Haruna, guda goma sha uku ne tare da wuraren kiwo nasu.
20-22Aka ba sauran Kohatiyawa na iyalan Lawiyawa birane huɗu daga kabilar Ifraimu. Aka ba su Shekem tare da wuraren kiwo nata, a ƙasar tuddai ta Ifraimu, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Gezer tare da wuraren kiwo nata, da Yokmeyam tare da wuraren kiwo nata, da Bet-horon tare da wuraren kiwo nata. 23-24Aka kuma ba su birane huɗu daga kabilar Dan, wato Elteki tare da wuraren kiwo nata, da Gibbeton tare da wuraren kiwo nata, da Ayalon tare da wuraren kiwo nata, da Gat-rimmon tare da wuraren kiwo nata. 25Daga cikin rabin kabilar Manassa, aka ba su birane biyu, su ne Ta'anak tare da wuraren kiwo nata, da Bileyam tare da wuraren kiwo nata. 26Dukan birane da wuraren kiwo nasu da aka ba sauran Kohatawa na iyalan Lawiyawa guda goma ne.
27Aka ba iyalan Gershonawa na cikin Lawiyawa birane biyu daga cikin rabo na rabin kabilar Manassa. Biranen su ne, Golan tare da wuraren kiwo nata, cikin Bashan, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Ashtarot da wuraren kiwo nata. 28-29Aka kuma ba su birane huɗu daga cikin kabilar Issaka, biranen su ne, Kishiyon da wuraren kiwo nata, da Daberat da wuraren kiwo nata, da Yarmut da wuraren kiwo nata, da Enganim da wuraren kiwo nata. 30-31Daga cikin rabon kabilar Ashiru aka ba su birane huɗu, su ne Mishal da wuraren kiwo nata, da Abdon da wuraren kiwo nata, da Helkat da wuraren kiwo nata, da Rehob da wuraren kiwo nata. 32Daga cikin rabon kabilar Naftali aka ba su birane uku, su ne, Kedesh ta Galili da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Hammon da wuraren kiwo nata, da Kartan da wuraren kiwo nata. 33Dukan birane da wuraren kiwo nasu da aka ba iyalan Gershonawa guda goma sha uku ne.
34-35Aka ba iyalan Merari na cikin Lawiyawa birane huɗu daga cikin rabon kabilar Zabaluna. Biranen ke nan, Yakneyam da wuraren kiwo nata, da Karta da wuraren kiwo nata, da Rimmon da wuraren kiwo nata, da Nahalal da wuraren kiwo nata. 36-37Aka kuma ba su birane huɗu daga cikin rabon kabilar Ra'ubainu. Biranen ke nan, Bezer da wuraren kiwo nata, da Yahaza da wuraren kiwo nata da Kedemot da wuraren kiwo nata, da Mefayat da wuraren kiwo nata., 38-39Daga cikin kabilar Gad aka ba su birane huɗu, su ne Ramot ta Gileyad da wuraren kiwo nata, wannan birnin mafaka ne domin wanda ya yi kisankai, da Mahanayim da wuraren kiwo nata, da Heshbon da wuraren kiwo nata, da Yazar da wuraren kiwo nata. 40Dukan biranen da aka ba iyalan Merari na Lawiyawa guda goma sha biyu ne.
41Jimillar biranen da wuraren kiwo nasu da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama'ar Isra'ila guda arba'in da takwas ne. 42Kowane birni yana da wuraren kiwo nasa kewaye da shi.
Isra'ilawa Sun Mallaki Ƙasar
43Haka kuwa Ubangiji ya ba Isra'ilawa dukan ƙasar da ya rantse zai ba kakanninsu. Suka ci ƙasar, suka zauna a ciki. 44Ubangiji kuma ya ba da hutawa ko'ina kamar yadda ya rantse wa kakanninsu. Babu wani daga cikin abokan gābansu da ya iya ta da kai da su, gama Ubangiji ya ba da abokan gābansu duka a hannunsu. 45Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alheri da ya yi wa gidan Isra'ila.

Currently Selected:

Josh 21: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in