Josh 15
15
Yankin Ƙasar da Aka Ba Yahuza
1Rabon da aka ba jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu ya yi kudu, a iyakar Edom zuwa jejin Zin, can kudu nesa. 2Iyakarsu wajen kudu ta miƙa tun daga ƙarshen Tekun Gishiri, daga wajen gaɓar da ta fuskanci kudu. 3Ta milla kudanci hawan Akrabbim, ta zarce zuwa Zin, ta haura kudu da Kadesh-barneya, ta wajen Hesruna har zuwa Addar. Sai ta karkata zuwa Karka. 4Ta zarce zuwa Azemon, ta bi ta rafin Masar zuwa inda ya gangara a teku. Wannan ita ce iyakar mutanen Yahuza wajen kudu. 5Iyakarsu wajen gabas ta kama daga Tekun Gishiri zuwa bakin Urdun. Wajen arewa kuwa ta miƙa daga bakin teku a inda Kogin Urdun ya gangara a tekun. 6Iyakar ta bi zuwa Bet-hogla, ta zarce zuwa arewa da Bet-araba, ta haura zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ra'ubainu. 7Daga kwarin Akor ta wuce zuwa Debir ta yi wajen arewa, sa'an nan ta juya zuwa Gilgal wadda take daura da hawan Adummim wanda yake kudancin gefen kwarin. Sai ta zarce zuwa ruwan En-shemesh, ta ƙare a En-rogel. 8Daga nan iyakar ta bi ta kwarin ɗan Hinnom a wajen kudancin kafaɗar Yebus, wato Urushalima. Ta kuwa bi ta dutsen da yake shimfiɗe daura da kwarin Hinnom wajen yamma, a arewacin ƙarshen kwarin Refayawa. 9Ta kuma milla daga kan dutsen zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa, daga can zuwa biranen Dutsen Efron. Daga can kuma ta karkata zuwa Ba'ala, wato Kiriyat-yeyarim. 10Ta kuma kewaye kudancin Ba'ala zuwa Dutsen Seyir. Ta zarce zuwa arewacin kafaɗar Dutsen Yeyarim, wato Kesalon. Daga nan ta gangara zuwa Bet-shemesh, ta kuma wuce zuwa Timna. 11Iyakar kuma ta biya wajen kafaɗar tudun, arewa da Ekron, sa'an nan ta karkata zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba'ala, ta tafi zuwa Yabneyel, sa'an nan ta gangara a teku. 12Bakin Bahar Rum, ita ce iyaka a wajen yamma. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu.
Kalibu Ya Ci Hebron da Debir da Yaƙi
(L.Mah 1.11-15)
13 #
L.Mah 1.20
Kamar yadda Ubangiji ya umarci Joshuwa, ya ba Kalibu, ɗan Yefunne, rabonsa a tsakiyar jama'ar Yahuza. Rabon da aka ba shi, shi ne Kiriyat-arba, wato Hebron. Arba shi ne uban Anak. 14Daga can sai Kalibu ya kori 'ya'yan Anak, maza, su uku, da Sheshai, da Ahiman, da Talmai, zuriyar Anak. 15Daga can kuma ya tafi ya fāɗa wa mazaunan Debir, dā sunan Debir Kiriyat-sefer ne. 16Kalibu ya ce, “Duk wanda ya bugi Kiriyat-sefer, har ya ci ta, zan ba shi 'yata Aksa aure.” 17Otniyel kuwa, ɗan Kenaz, ɗan'uwan Kalibu, ya ci Kiriyat-sefer. Kalibu kuwa ya ba shi Aksa 'yarsa aure. 18Da ta zo wurinsa, ya zuga ta ta roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”
19Ta kuwa ce masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ina roƙonka ka ba ni maɓuɓɓugar ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugar tuddai da na kwari.
Biranen Kabilar Yahuza
20Wannan shi ne gādon jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu. 21Biranen jama'ar Yahuza da suke can kudu sosai wajen iyakar Edom, su ne Kabzeyel, da Eder, da Yagur, 22da Kina, da Dimona, da Adada, 23da Kedesh, da Hazor, da Yitnan, 24da Zif, da Telem, da Beyalot, 25da Hazor-hadatta, da Kiriyot-hesruna, wato Hazor, 26da Amam, da Shema, da Molada, 27da Hazar-gadda, da Heshmon, da Bet-felet, 28da Hazar-shuwal, da Biyer-sheba, da Biziyotaya, 29da Ba'ala, da Abarim, da Ezem, 30da Eltola, da Kesil, da Horma, 31da Ziklag, da Madmanna, da Sansanna, 32da Labayot, da Shilhim, da Ayin, da Rimmon. Birane ashirin da tara ke nan da ƙauyukansu.
33Na filayen kwarin kuwa, su ne Eshtawol, da Zora, da Ashna, 34da Zanowa, da En-ganim, da Taffuwa, da Enayim, 35da Yarmut, da Adullam, da Soko, da Azeka, 36da Shayarim, da Aditayim, da Gedera, da Gederotayim. Birane goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu.
37Da kuma Zenan, da Hadasha, da Migdal-gad, 38da Dileyan, da Mizfa, da Yokteyel, 39da Lakish, da Bozkat, da Eglon, 40da Kabbon, da Lahmam, da Kitlish, 41da Gederot, da Bet-dagon, da Na'ama, da Makkeda, birane goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.
42Da kuma Libna, da Eter, da Ashan, 43da Yifta, da Ashna, da Nezib, 44da Kaila, da Akzib, da Maresha, birane tara ke nan da ƙauyukansu.
45Da kuma Ekron da garuruwanta da ƙauyukanta. 46Daga Ekron zuwa tekun, da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod.
47Ashdod da garuruwanta da ƙauyukanta, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta zuwa rafin Masar da Bahar Rum da bakinta.
48Birane na cikin ƙasar tuddai kuwa, su ne Shamir, da Yattir, da Soko, 49da Danna, da Kiriyat-sanna, wato Debir, 50da Anab, da Eshtemowa, da Anim, 51da Goshen, da Holon, da Gilo. Birane goma sha ɗaya ke nan da ƙauyukansu.
52Da kuma Arab, da Duma, da Eshan, 53da Yanim, da Bet-taffuwa, da Afeka, 54da Hunta, da Kiriyat-arba, wato Hebron, da Ziyor, birane tara ke nan da ƙauyukansu.
55Da kuma Mawon, da Karmel, da Zif, da Yutta, 56da Yezreyel, da Yokdeyam, da Zanowa, 57da Kayin, da Gebeya, da Timna, birane goma ke nan da ƙauyukansu.
58Halhul, da Bet-zur, da Gedor, 59da Ma'arat, da Bet-anot da Eltekon, birane shida ke nan da ƙauyukansu.
60Da kuma Kiriyat-ba'al, wato Kiriyat-yeyarim, da Rabba, birane biyu ke nan da ƙauyukansu.
61Biranen da suke a jeji kuwa su ne Bet-araba, da Middin, da Sekaka, 62da Nibshan, da Birnin Gishiri, da En-gedi, birane shida ke nan da ƙauyukansu.
63 #
L.Mah 1.21; 2Sam 5.6; 1Tar 11.4 Amma jama'ar Yahuza ba su iya korar Yebusiyawa waɗanda suke zaune a Urushalima ba, don haka Yebusiyawa suka yi zamansu da jama'ar Yahuza cikin Urushalima har wa yau.
Currently Selected:
Josh 15: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979