Josh 12
12
Sarakunan da Musa Ya Ci da Yaƙi
1 #
L.Ƙid 21.21-35; M.Sh 2.26—3.11 Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Isra'ilawa suka cinye da yaƙi, suka mallaki ƙasarsu a hayin Kogin Urdun daga yamma, tun daga kwarin Arnon har zuwa Dutsen Harmon da dukan Araba a wajen gabas, 2Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda yake zaune a Heshbon, wanda yake mulki tun daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa Kogin Yabbok a iyakar Ammonawa, 3daga kuma Araba zuwa gabashin Tekun Kinneret da zuwa Tekun Araga, wato Tekun Gishiri, a wajen gabas ta hanyar Ber-yeshimot, da wajen kudu zuwa gangaren gindin Dutsen Fisga, 4da kuma Og, Sarkin Bashan, ɗaya daga cikin sauran Refayawa, wato gwarzayen nan waɗanda suka zauna a Ashtarot da Edirai. 5Ya mallaki Dutsen Harmon, da Salka, da dukan Bashan, har zuwa iyakar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon. 6#L.Ƙid 32.33; M.Sh 3.12 Sai Musa, bawan Ubangiji, da Isra'ilawa suka ci sarakunan nan da yaƙi, sa'an nan ya ba da ƙasarsu ga Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa.
Sarakunan da Joshuwa Ya Ci da Yaƙi
7Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Joshuwa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi a yammacin Kogin Urdun tun daga Ba'al-gad a kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa Seyir. Joshuwa ya ba Isra'ilawa ƙasar gādo bisa ga yadda aka karkasa musu, 8da ƙasar tuddai, da filayen kwaruruka, da kwarin Araba, da gangaren tuddai, da jejin, da Negeb, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. 9Sunayen sarakunan su ne, Sarkin Yariko, da Sarkin Ai, da yake kusa da Betel, 10da Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, 11da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, 12da Sarkin Eglon, da Sarkin Gezer, 13da Sarkin Debir, da Sarkin Geder, 14da Sarkin Horma, da Sarkin Arad, 15da Sarkin Libna, da Sarkin Adullam, 16da Sarkin Makkeda, da Sarkin Betel, 17da Sarkin Taffuwa, da Sarkin Hefer, 18da Sarkin Afek, da Sarkin Lasharon, 19da Sarkin Madon, da Sarkin Hazor, 20da Sarkin Shimron-meron, da Sarkin Akshaf, 21da Sarkin Ta'anak, da Sarkin Magiddo, 22da Sarkin Kedesh, da Sarkin Yakneyam a Karmel, 23da Sarkin Dor a bakin teku, da Sarkin Goyim na Gilgal, 24da Sarkin Tirza. Sarakuna talatin da ɗaya ke nan.
Currently Selected:
Josh 12: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979