YouVersion Logo
Search Icon

Yow 1

1
Ɓarnar Fāra
1Maganar Ubangiji zuwa ga Yowel, ɗan Fetuwel.
2Ku dattawa, ku kasa kunne,
Bari kowa da kowa da yake cikin
Yahuza, ya kasa kunne.
Wani abu mai kamar wannan ya taɓa
faruwa a lokacinku,
Ko a lokacin kakanninku?
3Ku faɗa wa 'ya'yanku labarinsa,
'Ya'yanku kuma su faɗa wa
'ya'yansu,
'Ya'yansu kuma su faɗa wa tsara
mai zuwa.
4Abin da ɗango ya bari fara ta ci,
Abin da fara ta bari burduduwa ta
ci.
5Ku farka, ku yi ta kuka, ku
bugaggu,
Ku yi kuka, ku mashayan ruwan
inabi,
An lalatar da 'ya'yan inabin
Da ake yin sabon ruwan inabi da su.
6 # W.Yah 9.8 Rundunar ta aukar wa ƙasarmu,
Tana da ƙarfi, ba ta kuma
ƙidayuwa,
Haƙoranta suna da kaifi kamar na
zaki.
7Ta lalatar da kurangar inabinmu,
Ta cinye itatuwan ɓaurenmu.
Ta gaigaye ɓawo duka,
Saboda haka rassan sun zama fari
fat.
8Ya jama'a, ku yi kuka
Kamar yarinyar da take makokin
rasuwar saurayinta.
9Ba hatsi ko ruwan inabin
Da za a yi hadaya da su cikin
Haikalin.
Firistoci masu miƙa wa Ubangiji
hadaya suna makoki.
10Ba kome a gonaki,
Ƙasa tana makoki,
Domin an lalatar da hatsin,
'Ya'yan inabi sun bushe,
Itatuwan zaitun kuma sun yi yaushi.
11Ya ku manoma, ku yi baƙin ciki,
Ku yi kuka, ku da kuke lura da
gonakin inabi,
Gama alkama, da sha'ir,
Da dukan amfanin gonaki sun
lalace.
12Kurangar inabi ta bushe,
Itatuwan ɓaure kuma sun yi yaushi,
Rumman, da dabino, da gawasa,
Da dukan itatuwan gonaki sun
bushe.
Murna ta ƙare a wurin mutane.
13Ya ku firistoci masu miƙa hadayu a
bagaden Ubangiji,
Ku sa tufafin makoki, ku yi kuka!
Ku shiga Haikali, ku kwana,
Kuna saye da tufafin makoki,
Gama ba hatsi ko ruwan inabi da za
a yi hadaya da su,
A cikin Haikalin Allahnku.
14Ku sa a yi azumi,
Ku kira muhimmin taro.
Ku tara dattawa da dukan mutanen
ƙasar
A Haikalin Ubangiji Allahnku,
Ku yi kuka ga Ubangiji.
15 # Ish 13.6 Taku ta ƙare a wannan rana!
Gama ranar Ubangiji ta kusa,
Halaka daga wurin Maɗaukaki ta zo.
16An lalatar da amfanin gonaki a kan
idonmu,
Ba murna a Haikalin Allahnmu.
17Itatuwa sun mutu a busasshiyar
ƙasa,
Ba hatsin da za a adana a rumbu,
Rumbuna sun lalace domin ba hatsi.
18Dabbobi suna nishi!
Garkunan shanu sun ruɗe
Domin ba su da makiyaya.
Garkunan tumaki da awaki kuma
suna shan azaba.
19Ina kuka a gare ka, ya Ubangiji,
Domin ciyayi da itatuwa sun bushe,
Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.
20Har ma namomin jeji suna kuka a
gare ka,
Domin rafuffuka sun bushe,
Ciyayi kuma sun bushe,
Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.

Currently Selected:

Yow 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in