YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 23

23
Ayuba Yana Marmarin Kai Ƙara Gaban Allah
1Ayuba ya amsa.
2“Duk da haka zan yi tawaye in yi wa Allah gunaguni,
In dinga yin nishi.
3Da ma na san inda zan same shi,
In kuma san yadda zan kai wurinsa,
4Da zan kai ƙarata a gare shi, in faɗa masa duk muhawarata, in kāre kaina ne.
5Ina so in san irin amsar da zai mayar mini,
Ina kuma so in san yadda zai amsa mini.
6Allah kuwa da dukan ƙarfinsa zai yi gāba da ni?
A'a, zai saurara in na yi magana.
7Ina da aminci, zan faɗa wa Allah ra'ayina,
Zai tabbatar da amincina duka.
8“Na nemi Allah a gaba, amma ban same shi a can ba,
Ban kuwa same shi a baya ba sa'ad da na neme shi.
9Allah ya tafi wurin aiki a dama,
Ya kuma tafi hagu, amma har yanzu ban gan shi ba.
10Duk da haka Allah ya san kowane irin hali da nake ciki.
Idan ya jarraba ni zai tarar ni tsattsarka ne.
11Da aminci ina bin hanyar da ya zaɓa,
Ban kuwa taɓa kaucewa daga wannan gefe zuwa wancan ba.
12A kullum ina aikata abin da Allah ya umarta,
Ina bin nufinsa, ba nufin kaina ba.
13“Bai taɓa sākewa ba. Ba wanda zai iya gāba da shi,
Ko kuma ya hana shi yin abin da yake so ya aikata.
14Zai tabbatar da abin da ya shirya domina,
Wannan ma ɗaya daga cikin shirye-shiryen da ya yi ne.
15Don haka in rawar jiki a gabansa saboda tsoro.
16Allah Mai Iko Dukka ya lalatar da ƙarfin halina.
Allah ne ya tsorata ni,
17Amma ban damu da damu ba,
Ko da yake duhu ya dunɗe idanuna.”

Currently Selected:

Ayu 23: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in