Ayu 18
18
Bildad Ya Bayyana Abin da Za a Yi wa Mugun Mutum
1Bildad ya amsa.
2“Ayuba, mutane kamarka sun taɓa yin shiru?
Da ka yi ƙoƙari ka kasa kunne da mun yi magana da kai.
3Me ya sa kake tsammani mu dakikai ne kamar shanu?
4Cutar kanka kake yi saboda fushin da kake ji.
Duniya za ta ƙare ne sabili da kai?
Za a kawar da duwatsu sabili da kai?
5 #
Ayu 21.17
“Za a kashe hasken mugun mutum,
Harshen wutarsa ba zai ƙara ci ba.
6Fitilar da take cikin alfarwarsa ba za ta ba da haske ba.
7A dā gagau yake tafiya, amma yanzu ɗingishi yake yi,
Shawararsa ta kāshe shi.
8Yana tafiya, sai ya fāɗa cikin tarko.
Tarkon ya kama ƙafafunsa.
9Tarko ya kama diddigensa ya riƙe shi,
10An binne masa tarko a ƙasa,
An kafa masa tarko a hanyarsa.
11“Kewaye da shi duka razana tana jiransa,
Duk inda ya nufa tana biye da shi,
12Dā attajiri ne, amma yanzu ya talauce,
Kusa da shi bala'i na tsaye yana jiransa.
13Mummunan ciwo ya bazu ko'ina a jikinsa,
Yana sa hannuwansa da ƙafafunsa su ruɓe,
14Dā yana zaune lafiya,
Sai razana ta tatike shi,
Ta jawo shi zuwa ga Sarkin Mutuwa.
15Yanzu kowa zai iya zama a alfarwarsa,
Bayan da an karkashe ƙwayoyin cuta da farar wuta.
16Saiwoyinsa da rassansa suka yi yaushi suka bushe.
17Sunansa ya ƙare a gida da a jeji,
Ba wanda yake ƙara tunawa da shi.
18Za a kore shi daga ƙasar masu rai,
Za a kore shi daga haske zuwa duhu.
19Ba shi da zuriya, da sauran waɗanda suka ragu da rai.
20Daga gabas zuwa yamma, duk wanda ya ji labarin ƙaddarar da ta same shi,
Zai yi makyarkyata, ya yi rawar jiki don tsoro.
21Wannan ita ce ƙaddarar mugaye,
Wannan ita ce ƙaddarar mutane waɗanda ba su damu da kome na Allah ba.”
Currently Selected:
Ayu 18: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979