YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 10

10
Ayuba Ya Yi Kukan Matsayin da Yake Ciki
1“Na gaji da rayuwa,
Ku ji ina fama da baƙin ciki.
2Kada ka hukunta ni, ya Allah.
Ka faɗa mini laifin da kake tuhumata da shi.
3Daidai ne a gare ka ka yi mugunta?
Ka wulakanta abin da kai da kanka ka yi?
Sa'an nan ka yi murmushi saboda dabarun mugaye?
4Yadda mutane suke duban abu, haka kake duba?
5Kai ma ranka gajere ne kamar namu?
6In haka ne, me ya sa kake bin diddigin dukan laifofina,
Kana farautar dukan abin da na yi?
7Ka sani, ba ni da laifi,
Ka kuma sani, ba wanda zai cece ni daga gare ka.
8“Da ikonka ne ka yi ni, ka siffata ni,
Yanzu kuma da ikon nan naka ne za ka hallaka ni.
9Ka tuna, ya Allah, kai ka halicce ni, da yumɓu kuwa ka yi ni.
Za ka murtsuke ni ne, in kuma koma ƙura?
10Kai ne ka ba mahaifina ƙarfin da zai haife ni,
Kai ne ka sa na yi girma a cikin cikin mahaifiyata.
11Kai ne ka siffata jikina da ƙasusuwa da jijiyoyi,
Ka rufe ƙasusuwan da nama, naman kuma ka rufe da fata.
12Kai ne ka ba ni rai da madawwamiyar ƙauna,
Kulawarka ce ta sa ni rayuwa.
13Amma yanzu na sani,
Dukan lokacin nan kana da wani nufi a ɓoye game da ni.
14Jira kake ka ga ko zan yi zunubi,
Don ka ƙi gafarta mini.
15Da cewa na yi zunubi, na shiga uku ke nan a wurinka.
Amma sa'ad da na yi abin kirki ba na samun yabo.
Ina baƙin ciki ƙwarai, kunya ta rufe ni.
16Da zan ci nasara a kan kowane abu,
Da sai ka yi ta farautata kamar zaki,
Kana aikata al'ajabai don ka cuce ni.
17A koyaushe kakan karɓi shaida gāba da ni,
Fushinka sai gaba gaba yake yi a kaina,
Kakan yi mini farmaki a koyaushe.
18“Ya Allah, me ya sa ka bari aka haife ni?
Da ma na mutu tun kafin wani ya gan ni!
19Da a ce daga cikin cikin mahaifiyata an wuce da ni zuwa kabari
Da ya fi mini kyau bisa ga kasancewata.
20Raina bai kusa ƙarewa ba? A bar ni kawai!
Bari in ci moriyar lokacin da ya rage mini.
21An jima kaɗan zan tafi, ba kuwa zan komo ba faufau,
Zan tafi ƙasa mai duhu, inda ba haske,
22Ƙasa mai duhu, da inuwoyi da ɗimuwa
Inda ko haske ma kansa duhu ne.”

Currently Selected:

Ayu 10: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in