Irm 51
51
Hukuncin Ubangiji a kan Babila
1Ubangiji ya ce,
“Ga shi, zan kawo iskar ɓarna a
kan Babila
Da mazaunan Kaldiya.
2Zan aika da masu casawa zuwa
Babila, za su casa ta,
Su bar ƙasarta kango.
Za su kewaye ta a kowane sashi
A wannan ranar masifa.
3Kada ku bar maharbi ya yi harbi da
bakansa,
Kada kuma ya sa kayan yaƙinsa,
Kada ku rage samarinta,
Ku hallaka dukan sojojinta.
4Za su fāɗi matattu a ƙasar
Kaldiyawa,
Za a sassoke su a titunansu.”
5Allah na Isra'ila da Yahuza,
Ubangiji Mai Runduna, bai yashe
su ba,
Ko da yake sun yi wa Mai Tsarki na
Isra'ila zunubi.
6Ku gudu daga cikin Babila,
Bari kowa ya ceci ransa,
Kada a hallaka ku tare da ita,
Gama a wannan lokaci Ubangiji zai
sāka mata,
Zai sāka mata bisa ga alhakinta.
7 #
W.Yah 17.2-4; 18.3 Babila ta zama ƙoƙon zinariya a
hannun Ubangiji,
Ta sa dukan duniya ta yi maye.
Ƙasashen duniya sun sha ruwan
inabinta, suka haukace.
8Farat ɗaya, Babila ta fāɗi, ta
kakkarye,
Ku yi kuka dominta!
Ku samo mata magani domin azabar
da take sha, watakila ta warke.
9 #
W.Yah 18.5
Mun ba Babila magani, amma ba ta
warke ba.
Bari mu ƙyale ta, kowannenmu ya
koma garinsu,
Gama hukuncinta ya kai sammai, ya
yi tsawo har samaniya.
10Ubangiji ya baratar da mu a fili,
Bari mu tafi mu yi shelar aikin
Ubangiji Allahnmu a cikin
Sihiyona.
11Ku wasa kibau, ku cika
kwaruruwanku!
Ubangiji ya ta da ruhun sarakunan
Mediyawa,
Domin yana niyyar hallaka Babila.
Gama Ubangiji zai yi ramuwa
saboda Haikalinsa.
12Ku ta da tuta don a faɗa wa garun
Babila,
Ku ƙarfafa matsara,
Ku sa su su yi tsaro,
Ku kuma sa 'yan kwanto!
Ga shi, Ubangiji ya yi niyya, ya kuwa
aikata
Abin da ya faɗa a kan mazaunan
Babila.
13 #
W.Yah 17.1
Ƙarshenki ya zo,
Ke mai zama kusa da ruwa mai yawa,
Mai yawan dukiya.
Ajalinki ya auka.
14Ubangiji Mai Runduna ya rantse da
zatinsa, ya ce,
“Hakika zan cika Babila da mutane
kamar fāra,
Za su kuwa raira waƙar nasara a
kanta.”
15Ubangiji ne ya halicci ƙasa da
ikonsa,
Ya kafa duniya da hikimarsa,
Ya kuma shimfiɗa sammai da
fahiminsa.
16Bisa ga umarninsa ruwan da yake
samaniya yakan yi ruri,
Yakan sa gajimare su tashi daga
ƙarshen duniya,
Yakan sa walƙiya ta walƙata cikin
ruwan sama,
Yakan sa iska ta haura daga cikin
taskokinsa.
17Kowane ɗan adam wawa ne, marar
ilimi,
Kowane maƙerin zinariya kuma zai
sha kunya daga wurin gumakansa,
Gama siffofinsa na ƙarya ne, ba
numfashi a cikinsu.
18Su marasa amfani ne, aikin ruɗarwa
ne kawai,
Za su lalace a lokacin da za a
hukunta su.
19Amma wanda yake wajen Yakubu ba
haka yake ba,
Domin shi ne ya halicci dukan abu,
Isra'ila kuwa abin mallakarsa ne,
Ubangiji Mai Runduna ne sunansa.
20Ubangiji ya ce,
“Kai ne guduma da kayan yaƙina,
Da kai ne na farfasa ƙasashen duniya,
Da kai ne na hallaka mulkoki.
21Da kai ne na karya doki da mahayinsa,
22Da kai ne na farfasa karusa da mahayinsa.
Da kai ne na kakkarya mace da namiji,
Da kai ne na kakkarya tsoho da saurayi,
Da kai ne na kakkarya saurayi da budurwa,
23Da kai ne na kakkarya makiyayi da garkensa,
Da kai ne na kakkarya manoma
da dawakan nomansa,
Da kai ne na kakkarya masu mulki
da shugabanni.”
24Ubangiji ya ce, “Zan sāka wa Babila da dukan mazaunan Kaldiya a ganin idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona.
25“Ga shi, ina gaba da kai, ya dutse mai
hallakarwa,
Wanda ya hallaka duniya duka.
Zan miƙa hannuna gāba da kai,
Zan mirgino da ƙasa daga
ƙwanƙolin dutse,
Zan maishe ka ƙonannen dutse.
26Ba za a sami dutsen yin kusurwa, ko
na kafa harsashen gini a cikinka ba,
Amma za ka zama marar amfani har abada.”
27Ku ta da tuta a duniya,
Ku busa wa ƙasashen duniya ƙaho,
Ku shirya ƙasashe don su yi yaƙi da ita,
Ku kirawo mulkokin Ararat, da na
Minni, da na Ashkenaz, su yi yaƙi da ita.
Ku naɗa sarkin yaƙi wanda zai
shugabanci yaƙin da za a yi da ita,
Ku kawo dawakai kamar fāra.
28Ku shirya ƙasashe su yi yaƙi da ita,
Sarakunan Mediyawa, da masu
mulkinsu, da shugabanninsu,
Da kowace ƙasar da take ƙarƙashin mulkinsu.
29Duniya ta girgiza, tana makyarkyata
saboda azaba,
Gama nufin Ubangiji na gāba da
Babila ya tabbata,
Nufinsa na mai da ƙasar Babila
kufai, inda ba kowa.
30Sojojin Babila sun daina yaƙi, suna
zaune a cikin kagaransu.
Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata,
An sa wa wuraren zamanta wuta,
An karya ƙyamaren ƙofofin garinta.
31Maguji yana biye da maguji a guje,
Jakada yana biye da jakada,
Don su faɗa wa Sarkin Babila, cewa
an ci birninsa a kowane gefe.
32An ƙwace mashigai
An ƙone fadamu da wuta,
Sojoji sun gigice.
33Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na
Isra'ila na ce,
“Mutanen Babila sun zama kamar
daɓen masussuka
A lokacin da ake sussuka,
Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”
34Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya
cinye Urushalima,
Ya ragargaza ta,
Ya maishe ta kufai,
Ya haɗiye ta kamar yadda dodon
ruwa yakan yi,
Ya cika cikinsa da kayan marmarinta,
Ya tatse ta sarai.
35Bari mutanen Sihiyona su ce,
“Allah ya sa muguntar da mutanen
Babila suka yi mana ta koma kansu!”
Bari kuma mutanen Urushalima su ce,
“Allah ya sa hakkin jininmu ya koma
kan Kaldiyawa!”
36Ubangiji ya ce,
“Zan tsaya muku,
Zan ɗaukar muku fansa,
Zan sa tekunsu da maɓuɓɓugarsu su ƙafe.
37Babila za ta zama tarin juji, wurin
zaman diloli,
Abar ƙyama da abar ba'a, inda ba kowa.
38Mutanen Babila za su yi ruri kamar
zakuna,
Su yi gurnani kamar 'ya'yan zaki.
39Sa'ad da suke cike da haɗama zan yi
musu biki,
In sa su sha, su yi maye, su yi murna.
Za su shiga barcin da ba za su farka ba.
40Zan kai su mayanka kamar 'yan
raguna, da raguna, da bunsurai.
41“An ci Babila,
Ita wadda duniya duka take yabo an
cinye ta da yaƙi,
Ta zama abar ƙyama ga sauran al'umma!
42Teku ta malalo a kan Babila,
Raƙuman ruwa masu hauka sun rufe ta.
43Garuruwanta sun zama abin ƙyama,
Ta zama hamada, inda ba ruwa,
Ƙasar da ba mazauna,
Ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta.
44Zan hukunta Bel, gunkin Babila,
Zan sa ya yi aman abin da ya haɗiye,
Ƙasashen duniya ba za su ƙara
bumbuntowa wurinsa ba.
Garun Babila ya rushe!”
45“Ku fito daga cikinta, ya jama'ata,
Kowa ya tsere da ransa daga zafin
fushin Ubangiji.
46Kada zuciyarku ta yi suwu,
Kada kuma ku ji tsoro saboda
labarin da ake ji a ƙasar,
Labari na wannan shekara dabam,
na wancan kuma dabam,
A kan hargitsin da yake a ƙasar,
Mai mulki ya tasar wa mai mulki.
47Saboda haka kwanaki suna zuwa,
Sa'ad da zan hukunta gumakan Babila,
Za a kunyatar da dukan ƙasar Babila,
Dukan matattunta za su faɗi a tsakiyarta.
48 #
W.Yah 18.20
Sa'an nan sama da duniya, da dukan
abin da take cikinsu,
Za su raira waƙar farin ciki,
Domin masu hallakarwa daga arewa
da za su auko mata,
Ni Ubangiji na faɗa.”
49 #
W.Yah 18.24
Babila za ta fāɗi,
Saboda mutanen Isra'ila da dukan
mutanen duniya waɗanda ta kashe.
50Ku waɗanda kuka tsere wa takobi!
Ku gudu! Kada ku tsaya!
Ku tuna da Ubangiji a can nesa inda kuke,
Ku kuma yi ta tunawa da
Urushalima.
51Mun sha kunya saboda zargin da ake
yi mana,
Kunya ta rufe mu,
Gama baƙi sun shiga tsarkakan
wurare na Haikalin Ubangiji.
52“Domin haka kwanaki suna zuwa,”
in ji Ubangiji,
“Sa'ad da zan hukunta gumakan
Babila, da dukan ƙasarta,
Waɗanda aka yi wa rauni, za su yi nishi.
53Ko da Babila za ta hau samaniya,
Ta gina kagara mai ƙarfi a can,
Duk da haka zan aiki masu
hallakarwa a kanta,
Ni Ubangiji na faɗa.”
54Ku ji muryar kuka daga Babila,
Da hargowar babbar hallakarwa
daga ƙasar Kaldiyawa!
55Gama Ubangiji yana lalatar da Babila,
Yana kuma sa ta kame bakinta na alfarma,
Sojoji suna kutsawa kamar raƙuman ruwa,
Suna ta da muryoyinsu.
56Gama mai hallakarwa ya auka wa Babila,
An kama sojojinta,
An kuma kakkarya bakunansu,
Gama Ubangiji shi Allah ne, mai sakayya,
Zai yi sakayya sosai.
57“Zan sa mahukuntanta, da masu hikimarta,
Da masu mulkinta, da shugabanninta,
Da sojojinta su sha su yi maye.
Za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,”
In ji Sarkin, mai suna Ubangiji Mai Runduna.
58“Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce,
Za a baje garun nan na Babila mai fāɗi
Za a kuma ƙone dogayen
ƙyamarenta da wuta.
Mutane sun wahalar da kansu a banza.
Sauran al'umma sun yi wahala kawai
domin wutar lalata.”
59Jawabin da annabi Irmiya ya ba Seraiya, ɗan Neriya, wato jikan Ma'aseya, lokacin da ya tafi tare da Zadakiya, Sarkin Yahuza, zuwa Babila a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Seraiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi. 60Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babila, wato dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babila. 61Irmiya kuwa ya ce wa Seraiya, “Lokacin da ka kai Babila, sai ka karanta dukan maganan nan. 62Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’ 63#W.Yah 18.21Sa'ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa'an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yufiretis. 64Sa'an nan ka ce, ‘Haka Babila za ta nutse, ba za ta ƙara tashi ba saboda masifar da Ubangiji zai kawo mata.’ ”
Wannan shi ne ƙarshen maganar Irmiya.
Currently Selected:
Irm 51: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979