Irm 47
47
Jawabin Ubangiji a kan Filistiyawa
1 #
Ish 14.29-31; Eze 25.15-17; Yow 3.4-8; Amos 1.6-8; Zaf 2.4-7; Zak 9.5-7 Kafin Fir'auna ya ci Gaza da yaƙi Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan Filistiyawa. 2Ubangiji ya ce,
“Ga shi, ruwa yana tasowa daga
arewa,
Zai zama kogi da yake ambaliya.
Zai malala bisa ƙasa da dukan abin
da yake cikinta,
Da birni da mazauna cikinsa,
Maza za su yi kuka,
Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.
3Da jin takawar kofatan dawakai,
Da amon karusai da ƙafafun karusai,
Ubanni ba su juya, su dubi
'ya'yansu ba,
Domin hannuwansu sun yi laƙwas,
4Domin lokacin hallaka dukan
Filistiyawa ya yi.
Za a datse wa Taya da Sidon kowane
taimakon da ya ragu,
Gama Ubangiji zai hallaka
Filistiyawa
Waɗanda suke baƙin teku na Kaftor.
5Baƙin ciki zalla ya sami Gaza,
Ashkelon ta lalace.
Ya ƙattin mutane, yaushe za ku
daina tsattsage kanku?
6Ya takobin Ubangiji, yaushe za ka
huta?
Sai ka koma ƙubenka,
Ka huta, ka yi shiru!
7Ƙaƙa zai huta, tun da ni Ubangiji ne
na umarce shi?
Ni Ubangiji na umarce shi ya yi yaƙi
da Ashkelon
Da mazauna a bakin teku.”
Currently Selected:
Irm 47: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979
Irm 47
47
Jawabin Ubangiji a kan Filistiyawa
1 #
Ish 14.29-31; Eze 25.15-17; Yow 3.4-8; Amos 1.6-8; Zaf 2.4-7; Zak 9.5-7 Kafin Fir'auna ya ci Gaza da yaƙi Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan Filistiyawa. 2Ubangiji ya ce,
“Ga shi, ruwa yana tasowa daga
arewa,
Zai zama kogi da yake ambaliya.
Zai malala bisa ƙasa da dukan abin
da yake cikinta,
Da birni da mazauna cikinsa,
Maza za su yi kuka,
Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.
3Da jin takawar kofatan dawakai,
Da amon karusai da ƙafafun karusai,
Ubanni ba su juya, su dubi
'ya'yansu ba,
Domin hannuwansu sun yi laƙwas,
4Domin lokacin hallaka dukan
Filistiyawa ya yi.
Za a datse wa Taya da Sidon kowane
taimakon da ya ragu,
Gama Ubangiji zai hallaka
Filistiyawa
Waɗanda suke baƙin teku na Kaftor.
5Baƙin ciki zalla ya sami Gaza,
Ashkelon ta lalace.
Ya ƙattin mutane, yaushe za ku
daina tsattsage kanku?
6Ya takobin Ubangiji, yaushe za ka
huta?
Sai ka koma ƙubenka,
Ka huta, ka yi shiru!
7Ƙaƙa zai huta, tun da ni Ubangiji ne
na umarce shi?
Ni Ubangiji na umarce shi ya yi yaƙi
da Ashkelon
Da mazauna a bakin teku.”
Currently Selected:
:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979