Irm 46
46
Annabci a kan Masar
1Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan sauran al'umma. 2#Ish 19.1-25; Eze 29.1—32.32 Ya yi magana game da sojojin Fir'auna, Sarkin Masar, waɗanda suke a bakin Kogin Yufiretis a Karkemish, waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya ci su da yaƙi a shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza.
3Masarawa suka yi ihu, suka ce,
“Ku shirya kutufani da garkuwa,
Ku matso zuwa wurin yaƙi!
4Ku ɗaura wa dawakanku sirdi, ku
hau!
Ku tsaya a wurarenku da kwalkwali
a ka!
Ku wasa māsunku!
Ku sa kayan yaƙi!”
5Ubangiji ya yi tambaya ya ce,
“Me nake gani?
Sun tsorata, suna ja da baya,
An ci sojojinsu, suna gudu,
Ba su waiwayen baya, akwai tsoro a
kowane sashi.”
6Masu saurin gudu ba za su tsere ba,
Haka nan kuma jarumi,
A arewa a gefen Kogin Yufiretis,
Sun yi tuntuɓe, sun fādi.
7Wane ne wannan mai tashi kamar
Kogin Nilu,
Kamar kogunan da ruwansu yake
ambaliya?
8Masar tana tashi kamar Nilu,
Kamar kogunan da ruwansu yake
ambaliya.
Masar ta ce, “Zan tashi, in rufe
duniya,
Zan hallaka birane da mazauna
cikinsu.”
9Ku haura, ku dawakai,
Ku yi sukuwar hauka, ku karusai!
Bari sojoji su fito,
Mutanen Habasha da Fut masu
riƙon garkuwoyi,
Da mutanen Lud, waɗanda suka iya
riƙon baka.
10Wannan rana ta Ubangiji, Allah Mai
Runduna ce,
Ranar ɗaukar fansa ce don ya rama
wa maƙiyansa.
Takobi zai ci, ya ƙoshi,
Ya kuma sha jininsu, ya ƙoshi,
Gama Ubangiji Allah Mai Runduna
zai hallaka maƙiyansa,
A arewa, a bakin Kogin Yufiretis.
11Ku mutanen Masar, ku haura zuwa
Gileyad
Don ku samo ganye!
A banza kuke morar magunguna,
Ba za ku warke ba.
12Kunyarku ta kai cikin sauran
al'umma,
Kukanku kuma ya cika duniya.
Soja na faɗuwa bisa kan soja.
Dukansu biyu sun faɗi tare.
13 #
Irm 43.10-13
Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan zuwan Nebukadnezzar, Sarkin Babila, don ya yi yaƙi da ƙasar Masar.
14“Ku yi shelarsa cikin garuruwan
Masar,
Cikin Migdol, da Memfis, da
Tafanes,
Ku ce, ‘Ku tsaya, ku yi shiri,
Gama takobi yana cin waɗanda suke
kewaye da ku!’
15Me ya sa gunkinka, Afis, ya fāɗi,
Wato bijimi, gunkinka bai tsaya ba?
Domin Ubangiji ya tunkuɗe shi
ƙasa!
16Sun yi ta fāɗuwa,
Suna faɗuwa a kan juna,
Sai suka ce, ‘Mu tashi mu koma
wurin mutanenmu,
Zuwa ƙasar haihuwarmu, mu gudu
daga takobin azzalumi!’
17“Ku ba Fir'auna Sarkin Masar
sabon suna,
‘Mai yawan surutu, wanda bai rifci
zarafi ba!’
18Ni wanda sunana Ubangiji Mai
Runduna Sarki ne,
Na rantse da raina, wani zai ɓullo,
Kamar Tabor a cikin tsaunuka,
Ko kuwa kamar Karmel a bakin
teku.
19Ya ku mazaunan Masar,
Ku shirya kayanku don zuwa bauta,
Gama Memfis za ta lalace, ta zama
kufai,
Ba mai zama a ciki.
20“Masar kyakkyawar karsana ce,
Amma bobuwa daga arewa ta aukar
mata!
21Sojojin ijararta kamar 'yan maruƙa
ne, masu yawan kitse,
Sun ba da baya, sun gudu, ba su
tsaya ba,
Domin ranar masifarsu ta zo,
Lokacin halakarsu ya yi.
22Masar tana gudu, tana huci kamar
maciji,
Gama abokan gābanta suna zuwa da
ƙarfi,
Za su faɗo mata da gatura kamar
masu saran itatuwa.
23Ni Ubangiji na ce, za su sari
kurminta,
Ko da yake ba su ƙirguwa,
Gama suna da yawa kamar fara,
Ba su lasaftuwa.
24Za a kunyatar da mutanen Masar,
An bashe su a hannun mutanen
arewa.”
25Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ga shi, zan hukunta Amon na No, da Fir'auna, da Masar, tare da allolinta, da sarakunanta, wato Fir'auna, tare da waɗanda suke dogara gare shi. 26Zan bashe su a hannun waɗanda suke neman ransu, wato a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da shugabanninsa. Daga baya kuma mutane za su zauna a Masar kamar dā. Ni Ubangiji na faɗa.
27 #
Irm 30.10,11 “Ya bawana Yakubu, kada ka ji
tsoro,
Kada ka firgita, ya Isra'ila.
Gama zan cece ka daga ƙasa mai
nisa,
Zan ceci zuriyarka daga ƙasar
bautarsu.
Yakubu zai komo, ya yi zamansa da
rai kwance,
Ba wanda zai razanar da shi.
28Ni Ubangiji na ce,
Kada ka ji tsoro, ya bawana
Yakubu,
Gama ina tare da kai.
Zan hallaka dukan sauran al'umma
sarai inda na kora ka.
Amma ba zan hallaka ka sarai ba.
Zan hukunta ka yadda ya kamata,
Ba zan bar ka ba hukunci ba.”
Currently Selected:
Irm 46: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979
Irm 46
46
Annabci a kan Masar
1Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan sauran al'umma. 2#Ish 19.1-25; Eze 29.1—32.32 Ya yi magana game da sojojin Fir'auna, Sarkin Masar, waɗanda suke a bakin Kogin Yufiretis a Karkemish, waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya ci su da yaƙi a shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza.
3Masarawa suka yi ihu, suka ce,
“Ku shirya kutufani da garkuwa,
Ku matso zuwa wurin yaƙi!
4Ku ɗaura wa dawakanku sirdi, ku
hau!
Ku tsaya a wurarenku da kwalkwali
a ka!
Ku wasa māsunku!
Ku sa kayan yaƙi!”
5Ubangiji ya yi tambaya ya ce,
“Me nake gani?
Sun tsorata, suna ja da baya,
An ci sojojinsu, suna gudu,
Ba su waiwayen baya, akwai tsoro a
kowane sashi.”
6Masu saurin gudu ba za su tsere ba,
Haka nan kuma jarumi,
A arewa a gefen Kogin Yufiretis,
Sun yi tuntuɓe, sun fādi.
7Wane ne wannan mai tashi kamar
Kogin Nilu,
Kamar kogunan da ruwansu yake
ambaliya?
8Masar tana tashi kamar Nilu,
Kamar kogunan da ruwansu yake
ambaliya.
Masar ta ce, “Zan tashi, in rufe
duniya,
Zan hallaka birane da mazauna
cikinsu.”
9Ku haura, ku dawakai,
Ku yi sukuwar hauka, ku karusai!
Bari sojoji su fito,
Mutanen Habasha da Fut masu
riƙon garkuwoyi,
Da mutanen Lud, waɗanda suka iya
riƙon baka.
10Wannan rana ta Ubangiji, Allah Mai
Runduna ce,
Ranar ɗaukar fansa ce don ya rama
wa maƙiyansa.
Takobi zai ci, ya ƙoshi,
Ya kuma sha jininsu, ya ƙoshi,
Gama Ubangiji Allah Mai Runduna
zai hallaka maƙiyansa,
A arewa, a bakin Kogin Yufiretis.
11Ku mutanen Masar, ku haura zuwa
Gileyad
Don ku samo ganye!
A banza kuke morar magunguna,
Ba za ku warke ba.
12Kunyarku ta kai cikin sauran
al'umma,
Kukanku kuma ya cika duniya.
Soja na faɗuwa bisa kan soja.
Dukansu biyu sun faɗi tare.
13 #
Irm 43.10-13
Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan zuwan Nebukadnezzar, Sarkin Babila, don ya yi yaƙi da ƙasar Masar.
14“Ku yi shelarsa cikin garuruwan
Masar,
Cikin Migdol, da Memfis, da
Tafanes,
Ku ce, ‘Ku tsaya, ku yi shiri,
Gama takobi yana cin waɗanda suke
kewaye da ku!’
15Me ya sa gunkinka, Afis, ya fāɗi,
Wato bijimi, gunkinka bai tsaya ba?
Domin Ubangiji ya tunkuɗe shi
ƙasa!
16Sun yi ta fāɗuwa,
Suna faɗuwa a kan juna,
Sai suka ce, ‘Mu tashi mu koma
wurin mutanenmu,
Zuwa ƙasar haihuwarmu, mu gudu
daga takobin azzalumi!’
17“Ku ba Fir'auna Sarkin Masar
sabon suna,
‘Mai yawan surutu, wanda bai rifci
zarafi ba!’
18Ni wanda sunana Ubangiji Mai
Runduna Sarki ne,
Na rantse da raina, wani zai ɓullo,
Kamar Tabor a cikin tsaunuka,
Ko kuwa kamar Karmel a bakin
teku.
19Ya ku mazaunan Masar,
Ku shirya kayanku don zuwa bauta,
Gama Memfis za ta lalace, ta zama
kufai,
Ba mai zama a ciki.
20“Masar kyakkyawar karsana ce,
Amma bobuwa daga arewa ta aukar
mata!
21Sojojin ijararta kamar 'yan maruƙa
ne, masu yawan kitse,
Sun ba da baya, sun gudu, ba su
tsaya ba,
Domin ranar masifarsu ta zo,
Lokacin halakarsu ya yi.
22Masar tana gudu, tana huci kamar
maciji,
Gama abokan gābanta suna zuwa da
ƙarfi,
Za su faɗo mata da gatura kamar
masu saran itatuwa.
23Ni Ubangiji na ce, za su sari
kurminta,
Ko da yake ba su ƙirguwa,
Gama suna da yawa kamar fara,
Ba su lasaftuwa.
24Za a kunyatar da mutanen Masar,
An bashe su a hannun mutanen
arewa.”
25Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ga shi, zan hukunta Amon na No, da Fir'auna, da Masar, tare da allolinta, da sarakunanta, wato Fir'auna, tare da waɗanda suke dogara gare shi. 26Zan bashe su a hannun waɗanda suke neman ransu, wato a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da shugabanninsa. Daga baya kuma mutane za su zauna a Masar kamar dā. Ni Ubangiji na faɗa.
27 #
Irm 30.10,11 “Ya bawana Yakubu, kada ka ji
tsoro,
Kada ka firgita, ya Isra'ila.
Gama zan cece ka daga ƙasa mai
nisa,
Zan ceci zuriyarka daga ƙasar
bautarsu.
Yakubu zai komo, ya yi zamansa da
rai kwance,
Ba wanda zai razanar da shi.
28Ni Ubangiji na ce,
Kada ka ji tsoro, ya bawana
Yakubu,
Gama ina tare da kai.
Zan hallaka dukan sauran al'umma
sarai inda na kora ka.
Amma ba zan hallaka ka sarai ba.
Zan hukunta ka yadda ya kamata,
Ba zan bar ka ba hukunci ba.”
Currently Selected:
:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979