Irm 45
45
Jawabin Irmiya ga Baruk
1 #
2Sar 24.1; 2Tar 36.5-7; Dan 1.1,2 A shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Baruk ɗan Neriya ya rubuta abin da Irmiya ya faɗa masa. 2“Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce maka, kai Baruk, 3kai ka ce, ‘Kaitona, gama Ubangiji ya ƙara baƙin ciki a kan wahalaina, na gaji da nishina, ba ni da hutu!’
4“Sai ka faɗa wa Baruk cewa, ‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, abin da na gina zan rushe shi, abin da kuma na dasa zan tumɓuke shi, wato ƙasar ɗungum. 5Kana nemar wa kanka manyan abubuwa? Kada ka neme su, gama zan kawo masifa a kan dukan 'yan adam, amma zan kuɓutar da ranka kamar ganima, a dukan wuraren da za ka tafi.’ ”
Currently Selected:
Irm 45: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979