Irm 37
37
An Sa Irmiya a Kurkuku
1 #
2Sar 24.17; 2Tar 36.10 Zadakiya ɗan Yosiya, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya naɗa Sarkin Yahuza, ya yi mulki a maimakon Yekoniya ɗan Yehoyakim. 2Amma shi da barorinsa, da mutanen ƙasar, ba wanda ya kasa kunne ga maganar Ubangiji wadda ya yi musu ta bakin annabi Irmiya.
3Sai sarki Zadakiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, a wurin annabi Irmiya cewa, “Ka yi addu'a ga Ubangiji Allah dominmu.” 4A lokacin nan Irmiya yana kai da kawowa a cikin mutane, gama ba a tsare shi a kurkuku ba tukuna. 5Rundunar sojojin Fir'auna kuwa ta taho daga Masar, amma da Kaldiyawa waɗanda suka kewaye Urushalima da yaƙi suka ji labari, sai suka janye daga Urushalima.
6Sai Ubangiji ya yi magana da annabi Irmiya, ya ce, 7“Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na ce ka faɗa wa Sarkin Yahuza wanda ya aiko ka ka tambaye ni, ka faɗa masa cewa, ‘Rundunar sojojin Fir'auna, wadda ta kawo maka gudunmawa tana gab da juyawa zuwa ƙasarta a Masar. 8Kaldiyawa kuwa za su komo su yi yaƙi da wannan birni. Za su ci birnin, su ƙone shi da wuta. 9Ni Ubangiji, na ce kada ku ruɗi kanku da cewa Kaldiyawa ba za su dawo ba, gama ba shakka za su zo. 10Ko da a ce za ku ci dukan rundunar sojojin Kaldiyawa wadda take yaƙi da ku, sauran waɗanda kuka yi wa rauni da suke kwance a alfarwai za su tashi su ƙone birnin da wuta.’ ”
11Da rundunar sojojin Kaldiyawa ta janye daga Urushalima saboda zuwan rundunar sojojin Fir'auna, 12sai Irmiya ya tashi daga Urushalima zai tafi can ƙasar Biliyaminu, don ya karɓi nasa rabo tare da dangi. 13A sa'ad da ya isa Ƙofar Biliyaminu, shugaban matsara, Irija ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama annabi Irmiya ya ce, “Kai kana gudu zuwa wurin Kaldiyawa ne.”
14Sai Irmiya ya ce, “Ƙarya ce, ni ba gudu zuwa wurin Kaldiyawa nake yi ba.” Amma Irija bai yarda ba, sai ya kai shi wurin shugabanni. 15Shugabanni suka yi fushi da Irmiya, suka yi masa dūka, suka tsare shi a gidan Jonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku. 16Irmiya ya yi kwanaki da yawa can cikin kurkukun.
Zadakiya Ya Nemi Shawara ga Irmiya
17Sarki Zadakiya ya aika a kawo masa Irmiya. Sarki kuwa ya shigar da shi gidansa, ya tambaye shi a asirce, ya ce, “Ko akwai wata magana daga wurin Ubangiji?”
Sai Irmiya ya ce, “Akwai kuwa!” Ya ci gaba ya ce, “Za a ba da kai a hannun Sarkin Babila.” 18Sai kuma ya tambayi sarki Zadakiya ya ce, “Wane laifi na yi maka, ko barorinka, ko wannan jama'a da ka sa ni a kurkuku? 19Ina annabawanku waɗanda suka yi maka annabci cewa, ‘Sarkin Babila ba zai kawo wa ƙasarku yaƙi ba?’ 20Yanzu ya maigirma sarki, ina roƙonka ka ji wannan roƙo da nake yi maka, kada ka mai da ni a gidan Jonatan magatakarda, domin kada in mutu a can.”
21Sai sarki Zadakiya ya ba da umarni, suka sa Irmiya a gidan waƙafi. Aka riƙa ba shi malmalar abinci daga unguwar masu tuya kowace rana, har lokacin da abinci ya ƙare duka a birnin. Haka kuwa Irmiya ya zauna a gidan waƙafi.
Currently Selected:
Irm 37: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979