Irm 28
28
Annabcin Ƙarya na Hananiya
1 #
2Sar 24.18-20; 2Tar 36.11-13 Ya zama fa a wannan shekara, a watan biyar, a shekara ta huɗu ta sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza, sai annabi Hananiya ɗan Azzur mutumin Gibeyon, ya yi magana da ni a Haikalin Ubangiji, a gaban firistoci da dukan jama'a, ya ce, 2“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa, ‘Na karya karkiyar Sarkin Babila. 3Bayan shekara biyu zan komo da kayayyakin Haikalin Ubangiji zuwa wurin nan. Kayayyakin da Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya kwashe daga wannan wuri, ya kai Babila. 4Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan waɗanda aka kai su zaman talala daga Yahuza, gama zan karya karkiyar Sarkin Babila.’ ”
5Sa'an nan annabi Irmiya ya yi magana da annabi Hananiya a gaban firistoci da dukan jama'ar da suke tsaye a Haikalin Ubangiji, ya ce, 6“Amin, amin, Ubangiji ya sa ya zama haka, Ubangiji ya sa annabcin da ka yi ya zama gaskiya, Ubangiji ya komo da kayayyakin Haikalinsa da dukan waɗanda aka kai su zaman talala a Babila. 7Amma yanzu sai ka ji maganan nan da zan faɗa maka, kai da dukan jama'an nan. 8Annabawan da suka riga mu, ni da kai a zamanin dā, sun yi wa ƙasashe masu yawa da manyan mulkoki annabcin yaƙi da yunwa, da annoba. 9Idan maganar wannan annabi kuwa da ya yi annabcin salama ta cika, sa'an nan ne za a sani gaskiya Ubangiji ne ya aiko shi.”
10Sai annabi Hananiya ya cire karkiyar daga wuyan annabi Irmiya ya karya ta. 11Sa'an nan Hananiya ya yi magana a gaban dukan jama'a, ya ce, “In ji Ubangiji, haka zan karya karkiyar Nebukadnezzar, Sarkin Babila, daga wuyan dukan al'ummai kafin shekara biyu.” Sai annabi Irmiya ya yi tafiyarsa.
12Da ɗan daɗewa bayan da annabi Hananiya ya karya karkiyar da take a wuyan annabi Irmiya, sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce 13ya tafi ya faɗa wa Hananiya, ya ce, “Haka Ubangiji ya ce, ‘Ka karya karkiya ta itace, amma zan yi karkiya ta ƙarfe a maimakonta. 14Gama haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na faɗa. Na sa wa wuyan dukan waɗannan al'ummai karkiya ta ƙarfe, don su bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila, za su kuwa bauta masa, gama na ba shi su, har da namomin jeji.’ ”
15Sai annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka ji, ya Hananiya, Ubangiji bai aike ka ba, kana sa mutanen nan su dogara ga ƙarya. 16Saboda haka, in ji Ubangiji, ‘Zan kawar da kai daga duniya. Za ka mutu a wannan shekara domin ka kuta tayarwa ga Ubangiji.’ ”
17A wannan shekara kuwa, a watan bakwai, sai annabi Hananiya ya mutu.
Currently Selected:
Irm 28: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979