YouVersion Logo
Search Icon

Irm 2

2
Ubangiji Ya Ji da Isra'ila da Masu Ridda
1Ubangiji ya ce mini, 2in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce,
“Na tuna da amincinki a lokacin
ƙuruciyarki,
Da ƙaunarki kamar ta amarya da
ango.
Yadda kika bi ni a cikin jeji, da a
ƙasar da ba a shuka ba.
3Isra'ila tsattsarka ce ta Ubangiji,
Nunar fari ta girbina.
Dukan waɗanda suka ci daga cikinki
sun yi laifi,
Masifa za ta auko miki.
Ni Ubangiji, na faɗa.”
4Ku ji jawabin Ubangiji, ku zuriyar Yakubu, ku dukan kabilan Isra'ila.
5Ubangiji ya ce,
“Wane laifi ne na yi wa kakanninku,
Da suka bar bina?
Suka bauta wa gumaka marasa
amfani,
Su kuma suka zama marasa amfani.
6Ba su kula da ni ba,
Ko da yake na cece su daga ƙasar
Masar.
Na bi da su a cikin hamada,
A ƙasa mai tuddai da kwazazzabai,
Busasshiya mai yawan hatsari,
Ba a bi ta cikinta,
Ba wanda yake zama cikinta kuma.
7Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi,
Don su more ta su ci amfaninta,
Amma da suka shiga, sun ƙazantar
mini da ita,
Suka sa ƙasar da na gādar musu ta
zama abar ƙyama.
8Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina Ubangiji Yake’ ba?
Masanan shari'a ba su san ni ba.
Masu mulki sun yi mini laifi,
Annabawa sun yi annabci da sunan
Ba'al,
Sun bi waɗansu abubuwa marasa
amfani.”
Shari'ar da Ubangiji yake Yi wa Mutanensa
9“Domin haka, ni Ubangiji zan
gabatar da ku gaban shari'a.
Ku da 'ya'yanku, da 'ya'yan
'ya'yanku, wato jikokinku.
10Ku haye zuwa tsibirin Kittim wajen
yamma, ku gani,
Ku aika zuwa Kedar wajen gabas, ku
duba da kyau,
A dā an taɓa yin wani abu haka?
11Akwai wata al'umma da ta taɓa
sāke gumakanta
Ko da yake su ba kome ba ne?
Amma mutanena sun sauya darajarsu
da abin da ba shi da rai.
12Sammai, ku girgiza saboda wannan,
ku razana,
Ku yi shiru, ni Ubangiji na faɗa.
13Mutanena sun yi zunubi iri biyu,
Sun rabu da ni, ni da nake
maɓuɓɓugar ruwan rai,
Sun haƙa wa kansu tafkunan ruwa,
hudaddu,
Waɗanda ba za su iya ajiye ruwa ba.
14“Isra'ila ba bawa ba ne, ba a kuma
haife shi bawa ba,
Amma me ya sa ya zama ganima?
15Zakuna suna ruri a kansa,
Suna ruri da babbar murya.
Sun lalatar da ƙasarsa,
Garuruwansa sun lalace,
Ba wanda yake zaune cikinsu.
16Mutanen Memfis kuma da na
Tafanes sun fasa ƙoƙwan kansa.
17Ya Isra'ila, kai ne ka jawo wa kanka
wannan,
Da ka rabu da Ubangiji Allahnka,
Sa'ad da ya bishe ka a hanya.
18Wace riba ka samu, har da ka tafi
Masar,
Don ka sha ruwan Kogin Nilu?
Wace riba ka samu, har da ka tafi
Assuriya,
Don ka sha ruwan Kogin
Yufiretis?
19Muguntarka za ta hore ka,
Riddarka kuma za ta hukunta ka.
Sa'an nan za ka sani, ka kuma
gane,
Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a gare
ka
Ka rabu da Ubangiji Allahnka,
Ba ka tsorona a zuciyarka.
Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna na
faɗa.”
Isra'ila Ya Ƙi Yi wa Ubangiji Biyayya
20“Ya Isra'ila, tun da daɗewa, ka ƙi
yarda
Ubangiji ya mallake ka,
Ka ƙi yin biyayya da ni,
Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’
Amma ka yi karuwanci a kan
kowane tudu,
Da kowane ɗanyen itace.
21Na dasa ka kamar zaɓaɓɓiyar
kurangar inabi, zaɓaɓɓen iri mafi
kyau.
Ta yaya ka lalace haka ka zama
rassan kurangar inabi ta jeji,
Waɗanda ba zan yarda da su ba?
22Ko da za ka yi wanka da sabulun
salo,
Ka yi amfani da sabulu mai yawa,
Duk da haka zan ga tabban
zunubanka.
Ni Ubangiji Allah na faɗa.
23Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar da
kanka ba,
Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba'al ba?
Ka duba hanyarka ta zuwa cikin
kwari, ka san abin da ka yi.
Kana kama da taguwa, mai yawon
neman barbara.
24Kamar jakar jeji kake, wadda take
son barbara,
Wadda take busar iska,
Sa'ad da take son barbara, wa zai iya
hana ta?
Jakin da take sonta, ba ya bukatar
wahalar da kansa
Gama a watan barbararta za a same
ta.
25Kai Isra'ila, kada ka bar ƙafafunka
ba takalma,
Kada kuma ka bar maƙogwaronka
ya bushe.
Amma ka ce, ‘Wannan ba amfani,
Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwa
zan bi.’
26“Kamar yadda ɓarawo yakan sha
kunya sa'ad da aka kama shi,
Haka nan mutanen Isra'ila za su sha
kunya,
Da su, da sarakunansu, da
shugabanninsu,
Da firistocinsu, da annabawansu.
27Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai ne
mahaifinmu.’
Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, ka
haife mu.’
Gama sun ba ni baya, ba su fuskance
ni ba.
Amma sa'ad da suke shan wahala,
sukan ce,
‘Ka zo ka taimake mu.’
28Ina gumakan da kuka yi wa
kanku?
Bari su tashi in sun iya cetonku
lokacin wahalarku.
Yahuza, yawan gumakanku sun kai
Yawan garuruwanku.
29Ni Ubangiji, ina tambayarku, ‘Wace
ƙara kuke da ita game da ni?’
Kun yi mini tawaye dukanku.
30Na hori 'ya'yanku, amma a banza, ba
su horu ba,
Kun kashe annabawanku da takobi
kamar mayunwacin zaki.
31Ya ku mutanen zamanin nan, ku
saurari maganata.
Na zamar wa Isra'ila jeji? Ko ƙasar
da take da kurama?
Don me fa mutanena suke cewa,
‘Mu 'yantattu ne,
Ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?
32Budurwa ta manta da kayan
kwalliyarta?
Ko kuwa amarya ta manta da kayan
adonta?
Amma mutanena sun manta da ni
kwanaki ba iyaka.
33Kun sani sarai yadda za ku yi ku
farauci masoya,
Har mugayen mata ma, kun koya
musu hanyoyinku.
34Tufafinku sun ƙasantu da jinin
marasa laifi,
Waɗanda ba ku same su suna fasa
gidajenku ba.
Amma duk da haka kuna cewa,
35‘Ba mu da laifi, hakika kuwa,
Ubangiji bai yi fushi da mu ba.’
Amma ni Ubangiji zan hukunta ku,
Domin kun ce ba ku yi zunubi ba.
36Me ya sa ba ku da tsayayyiyar zuciya,
Sai ku yi nan ku yi can?
Masar za ta kunyata ku kamar yadda
Assuriya ta yi.
37Da hannuwanku a kā za ku komo
daga Masar don kunya.
Gama waɗanda kuke dogara gare su,
ni Ubangiji, na ƙi su,
Ba za ku yi arziki tare da su ba.”

Currently Selected:

Irm 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in