YouVersion Logo
Search Icon

Irm 17

17
Zunubin Yahuza Ya Yi Kanta
1Ubangiji ya ce, “An rubuta zunubin mutanen Yahuza da alƙalamin ƙarfe, mai bakin yakutu. An zana shi a allon zuciyarsu da a zankayen bagadansu. 2Idan sun tuna da 'ya'yansu haka sun tuna da bagadansu da Ashtarot ɗinsu a gindin itatuwa masu duhuwa da kan tuddai masu tsayi. 3Ku mazauna a tsaunuka da cikin saura, zan ba da dukiyarku da wadatarku ganima saboda dukan zunuban da kuka yi a dukan ƙasar. 4Za ku rasa abin da yake hannunku daga cikin gādon da na ba ku. Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama da fushina wuta ta kama wadda za ta yi ta ci har abada.”
5Ubangiji ya ce,
“La'ananne ne mutumin da yake
dogara ga mutum,
Wanda jiki ne makaminsa,
Wanda ya juya wa Ubangiji baya,
6Gama yana kama da sagagi a
hamada,
Ba zai ga wani abu mai kyau yana
zuwa ba.
Zai zauna a busassun wuraren
hamada,
A ƙasar gishiri, inda ba kowa.
7“Mai albarka ne mutumin da yake
dogara ga Ubangiji,
Wanda Ubangiji ne madogararsa.
8 # Zab 1.3 Shi kamar itace ne wanda ake dasa a
bakin rafi
Wanda yake miƙa saiwoyinsa zuwa
cikin rafin,
Ba zai ji tsoron rani ba,
Kullum ganyensa kore ne,
Ba zai damu a lokacin fari ba,
Ba zai ko fasa yin 'ya'ya ba.
9“Zuciya ta fi kome rikici,
Cuta gare ta matuƙa,
Wa zai san kanta?
10 # W.Yah 2.23; Zab 62.12 Ni Ubangiji nakan bincike tunani,
In gwada zuciya,
Domin in sāka wa kowane mutum
gwargwadon al'amuransa,
Da kuma gwargwadon ayyukansa.
11“Kamar makwarwar da ta kwanta
kan ƙwan da ba ita ta nasa ba,
Haka yake ga wanda ya sami dukiyar
haram,
Yana gaɓar ƙarfinsa, za ta rabu da
shi,
A ƙarshe zai zama wawa.”
12Kursiyi mai daraja,
Da aka sa a bisa tun daga farko,
Wurin ke nan inda Haikalinmu
yake.
13Ya Ubangiji, begen Isra'ila,
Duk waɗanda suka rabu da kai, za su
sha kunya.
Waɗanda suka ba ka baya a duniya
za a rubuta su
Domin sun rabu da Ubangiji,
maɓuɓɓugar ruwan rai.
Irmiya Ya Roƙi Ubangiji ya Kiyaye Shi
14Ubangiji, ka warkar da ni, zan kuwa
warke,
Ka cece ni, zan kuwa cetu,
Gama kai ne abin yabona.
15Ga shi, suna ce mini,
“Ina maganar Ubangiji take?
Ta zo mana!”
16Amma ni ban yi gudun zaman
makiyayi a gabanka ba,
Ban kuma so zuwan ranar bala'i ba,
Ka kuwa sani.
Abin da ya fito daga bakina kuwa,
A bayyane yake gare ka.
17Kada ka zamar mini abin razana,
Kai ne mafakata cikin ranar masifa,
18Bari waɗanda suka tsananta mini su
sha kunya,
Amma kada ka bar ni in kunyata.
Bari su tsorata,
Amma kada ka bar ni in tsorata.
Ka aukar musu da ranar masifa,
Ka hallaka su riɓi biyu!
A kan Kiyaye Ranar Asabar
19Haka Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi ka tsaya a ƙofar Biliyaminu, wadda sarakunan Yahuza suke shiga da fita ta cikinta, ka kuma tafi dukan ƙofofin Urushalima. 20Ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuza, da dukan Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi. 21#Neh 13.15-22 Haka Ubangiji ya ce, ku yi hankali saboda rayukanku, kada ku ɗauki kaya a ranar Asabar, ko ku shigar da kowane abu ta ƙofofin Urushalima. 22#Fit 20.8-10; M.Sh 5.12-14 Kada ku ɗauki kaya, ku fita da shi daga gidajenku a ranar, ko ku yi kowane irin aiki, amma ku kiyaye ranar Asabar da tsarki, kamar yadda na umarci kakanninku.’ 23Amma duk da haka ba su kasa kunne, ko su mai da hankali ba. Amma suka taurare don kada su ji, su karɓi koyarwa.
24“ ‘Amma idan kun kasa kunne gare ni,’ in ji Ubangiji, ‘ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofin wannan birni a ranar Asabar ba, amma kuka kiyaye ranar Asabar da tsarki, ba ku yi aiki a cikinta ba, 25sa'an nan ne sarakuna waɗanda za su zauna a kan gadon sarautar Dawuda, za su shiga ta ƙofofin wannan birni, suna hawan karusai, da dawakai, su da sarakunansu, da jama'ar Yahuza da mazaunan Urushalima. Za a zauna a wannan birni har abada. 26Mutane za su zo daga biranen Yahuza da wuraren da yake kewaye da Urushalima, daga ƙasar Biliyaminu, da ta Shefela, da ta ƙasar tuddai, da kuma ta Negeb, suna kawo hadayu na ƙonawa da sadakoki, da hadayu na sha, da na turare, za su kuma kawo hadayu na godiya a Haikalin Ubangiji. 27Amma idan ba ku kasa kunne gare ni ba, ba ku kuwa kiyaye ranar Asabar da tsarki ba, kun kuma ɗauki kaya kun shiga ta ƙofofin Urushalima a ranar Asabar, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wuta. Za ta kuwa cinye fādodin Urushalima, ba kuwa za ta kasu ba.’ ”

Currently Selected:

Irm 17: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in