YouVersion Logo
Search Icon

Irm 10

10
Gumaka da Allah na Gaskiya
1Ya jama'ar Isra'ila, ku ji jawabin da Ubangiji yake yi muku.
2Ubangiji ya ce,
“Kada ku koyi abubuwan da
al'ummai suke yi,
Kada ku ji tsoron alamun da suke a
sama,
Ko da yake al'ummai suna jin
tsoronsu.
3Gama al'adun mutane na ƙarya ne,
Daga cikin jeji aka sare wani itace,
Gwanin sassaƙa ya sassaƙa shi da
gizago.
4Mutane sukan yi masa ado na azurfa
da zinariya,
Sukan ɗauki guduma su kafa shi da
ƙusoshi,
Don kada ya motsa.
5Gumakansu dodon gona suke, a
cikin gonar kabewa,
Ba su iya yin magana,
Ɗaukarsu ake yi domin ba su iya
tafiya!
Kada ku ji tsoronsu.
Gama ba su da ikon aikata mugunta
ko alheri.”
6Ya Ubangiji, ba wani kamarka,
Kai mai girma ne,
Sunanka kuma yana da girma da
iko.
7 # W.Yah 15.4 Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya
Sarkin dukan al'ummai?
Ka isa a ji tsoronka,
Gama babu kamarka a cikin dukan
masu hikima na al'ummai,
Da kuma cikin dukan mulkokinsu,
Ba wani kamarka.
8Dukansu dakikai ne wawaye,
Koyarwar gumaka ba wani abu ba
ne, itace ne kawai!
9An kawo fallayen azurfa daga
Tarshish,
Da zinariya kuma daga Ufaz,
Aikin gwanaye da maƙeran
zinariya.
Tufafinsu na mulufi ne da shunayya,
duka aikin gwanaye.
10Amma Ubangiji shi ne Allah na
gaskiya,
Shi Allah mai rai ne,
Shi Sarki ne madawwami.
Saboda hasalarsa duniya ta girgiza,
Al'ummai ba za su iya jurewa da
fushinsa ba.
11Haka za ku faɗa musu, “Gumakan da ba su yi sammai da duniya ba, za su lalace a duniya da a ƙarƙashin sammai.”
12Shi ne, ta wurin ikonsa ya yi duniya,
Ta wurin hikimarsa ya kafa ta,
Ta wurin basirarsa kumaya ya shimfiɗa
sammai.
13Sa'ad da ya yi murya akan ji ƙugin
ruwa a cikin sammai
Yakan kawo ƙasashi daga ƙurewar
duniya,
Yakan yi walƙiyoyi saboda ruwan
sama,
Daga cikin taskokinsa yakan kawo
iska.
14Kowane mutum dakiki ne, marar
ilimi,
Kowane maƙerin zinariya zai sha
kunya saboda gumakansa,
Gama siffofinsa ƙarya ne,
Ba numfashi a cikinsu.
15Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne,
A lokacin da za a hukunta su za su
lalace.
16Gama shi ba kamar waɗannan yake
ba,
Shi na Yakubu ne.
Shi ne ya yi dukan kome,
Kabilan Isra'ilawa gādonsa,
Sunansa Ubangiji Mai Runduna.
Risɓewar Yahuza
17Ku tattara kayayyakinku,
Ku mazaunan wurin da aka kewaye
da yaƙi.
18Gama haka Ubangiji ya ce,
“Ga shi, ina jefar da mazaunan
ƙasar daga ƙasarsu a wannan
lokaci,
Zan kawo musu wahala, za su kuwa
ji jiki.”
19Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka
yi mini.
Raunina mai tsanani ne,
Amma na ce, lalle wannan azaba ce,
Tilas in daure da ita.
20An lalatar da alfarwata,
Dukan igiyoyi sun tsintsinke,
'Ya'yana maza sun bar ni, ba su
nan.
Ba wanda zai kafa mini alfarwata
Ya kuma rataya labulena.
21Makiyayan dakikai ne,
Ba su roƙi Ubangiji ba,
Don haka ba su sami wadata ba,
An watsa dukan garkensu.
22Ku ji fa, an ji ƙishin-ƙishin! Ga shi
kuma, yana tafe.
Akwai babban hargitsin da ya fito
daga arewa,
Don a mai da biranen Yahuza kufai,
wurin zaman diloli.
23“Ya Ubangiji, na sani al'amuran
mutum ba a hannunsa suke ba,
Ba mutum ne yake kiyaye takawarsa
ba
24Ka tsauta mini, ya Ubangiji, amma
da adalcinka,
Ba da fushinka ba, don kada ka
wofinta ni.
25Ka kwarara hasalarka a kan sauran
al'umma da ba su san ka ba,
Da a kan jama'ar da ba su kiran
sunanka,
Gama sun cinye Yakubu,
Sun cinye shi, sun haɗiye shi,
Sun kuma mai da wurin zamansa
kufai.”

Currently Selected:

Irm 10: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in