L.Mah 3
3
Al'umman da suka Ragu don a Jarraba Isra'ilawa
1Ubangiji ya bar waɗansu al'ummai a ƙasar domin ya jarraba Isra'ilawan da ba su san yaƙin Kan'ana ba. 2Ya yi haka ne domin ya koya wa tsararrakin Isra'ila yaƙi, wato waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba. 3Al'umman da suka ragu a ƙasar su ne, birane biyar na Filistiyawa, da dukan Kan'aniyawa, da Sidoniyawa, da Hiwiyawa da suke zaune a Dutsen Lebanon, tun daga Dutsen Ba'alharmon har zuwa mashigin Hamat, 4don a jarraba Isra'ilawa da su, a gani ko za su yi biyayya da umarnan Ubangiji da ya ba kakanninsu ta hannun Musa. 5Saboda haka jama'ar Isra'ila suka zauna tare da Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. 6Suka yi aurayya da su, suka kuma yi sujada ga gumakansu.
Otniyel ya Ceci Isra'ilawa
7Jama'ar Isra'ila kuwa suka manta da Ubangiji Allahnsu, suka yi masa zunubi, suka yi wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot sujada. 8Domin haka Ubangiji ya husata ƙwarai da Isra'ilawa, sai ya bashe su ga Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Jama'ar Isra'ila kuwa suka bauta masa shekara takwas. 9Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, sai Ubangiji ya ta da Otniyel, ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu don ya ceci Isra'ilawa. 10Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa domin ya hukunta Isra'ilawa. Ya fita ya yi yaƙi da Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Ubangiji kuwa ya ba da sarkin a hannun Otniyel, ya rinjaye shi. 11Ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba'in sa'an nan Otniyel, ɗan Kenaz ya rasu.
Ehud ya Ceci Isra'ilawa daga Mowabawa
12Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa Eglon Sarkin Mowab ya yi ƙarfi, domin ya yi gaba da su. 13Sai ya tattaro Amoriyawa da Amalekawa, ya je ya ci Isra'ilawa, ya mallaki birnin dabino, wato Yariko. 14Isra'ilawa suka bauta wa Eglon Sarkin Mowab, shekara goma sha takwas.
15Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, ya ba su wanda zai cece su, wato Ehud, ɗan Gera daga kabilar Biliyaminu, shi kuwa bahago ne. Isra'ilawa suka aika wa Eglon Sarkin Mowab da kyautai ta hannun Ehud. 16Sai Ehud ya ƙera wa kansa takobi mai kaifi biyu, tsawonsa kamu guda. Ya yi ɗamara da shi wajen cinyarsa ta dama a ƙarƙashin tufafinsa. 17Sa'an nan ya ɗauki kyautan, ya kai wa Eglon Sarkin Mowab. Eglon kuwa mai ƙiba ne. 18Da Ehud ya gama ba shi kyautan, sai ya sallami mutanen da suka ɗauko kyautan. 19Amma Ehud ya juya ya koma daga wajen sassaƙaƙƙun duwatsu kusa da Gilgal, ya ce wa Eglon, “Ranka ya daɗe, na kawo maka saƙo na asiri.”
Sai sarki ya ce wa fādawansa, “Ku ba mu wuri!” Dukansu kuwa suka fita, suka ba da wuri. 20Ehud kuwa ya je wurinsa, yana zaune shi kaɗai a jinkakken shirayi mai sanyi.
Sai Ehud ya ce, “Ina da saƙo daga wurin Allah zuwa gare ka!” Sarki kuwa ya tashi daga inda yake zaune, 21Ehud ya sa hannun hagunsa, ya zaro takobin da suke wajen cinyarsa ta dama, ya kirɓa masa a ciki. 22Takobin ya shiga duk da ƙotar, kitse ya rufe ruwan takobin gama bai zare takobin daga cikin sarkin ba. Ƙazanta kuwa ta fita. 23Ehud kuwa ya fita ta shirayin, ya kukkulle ƙofofin ɗakin. 24Bayan da ya tafi, fādawan suka zo, suka ga ƙofofin ɗakin suna a kulle, sai suka zaci sarkin ya zaga ne ya yi bawali. 25Suka yi ta jira har suka gaji. Da suka ga dai bai buɗe ba, suka ɗauki mabuɗi, suka buɗe, sai ga ubangijinsu a ƙasa matacce.
26Sa'ad da suke ta jira, Ehud ya riga ya tsere, ya wuce sassaƙaƙƙun duwatsu zuwa Seyira. 27Da ya isa can sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Ifraimu. Jama'ar Isra'ila kuwa suka gangara tare da shi daga ƙasar tudu. Yana kan gaba. 28Sai ya ce musu, “Ku biyo ni, gama Ubangiji ya ba da Mowabawa maƙiyanku a gare ku.” Suka gangara, suna biye da shi. Suka ƙwace wa Mowabawa mashigan Urdun, suka hana kowa wucewa. 29A lokacin ne suka kashe ƙarfafan mutane na Mowabawa mutum wajen dubu goma (10,000), ba wanda ya tsira. 30A ranar nan Isra'ilawa suka rinjayi Mowabawa. Ƙasar kuwa ta sami zaman lafiya har shekara tamanin.
Shamgar ya Ceci Isra'ilawa daga Filistiyawa
31Bayan Ehud kuma, sai Shamgar ɗan Anat, wanda ya kashe Filistiyawa ɗari shida da tsinken korar shanun noma, shi ma ya ceci Isra'ilawa.
Currently Selected:
L.Mah 3: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979