YouVersion Logo
Search Icon

L.Mah 19

19
Balawe da Ƙwarƙwararsa
1A lokacin nan ba sarki a Isra'ila. Sai wani Balawen da yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Ifraimu ya ɗauko wata mace daga Baitalami ta Yahudiya ta zama ƙwarƙwararsa. 2Ƙwarƙwarar kuwa ta ji haushinsa, ta koma gidan mahaifinta a Baitalami ta Yahudiya. Ta zauna a can har wata huɗu. 3Sa'an nan mutumin ya tafi ya yi bikonta. Ya tafi da baransa da jaki biyu. Da ya zo gidan mahaifinta, sai ta shigo da shi gidan, mahaifin ya karɓe shi da farin ciki. 4Mahaifin macen ya i masa ya dakata, sai ya tsaya har kwana uku. Suka ci suka sha tare. 5A safiyar rana ta huɗun, suka tashi tun da wuri, domin su yi shirin tafiya, amma mahaifin matar ya ce masa, “Ka dakata ka ƙara cin abinci tukuna sa'an nan ka tafi.”
6Su biyu kuwa suka zauna suka ci suka sha tare. Har yanzu mahaifin mace ya sāke ce masa, “Ina roƙonka ka ƙara kwana, ka saki jikinka ka more.”
7Sa'ad da mutumin ya tashi zai tafi sai mahaifin macen ya roƙe shi, ya kuma kwana. 8A rana ta biyar, sai mutumin ya tashi da wuri don ya tafi amma mahaifin macen ya ce masa, “Ka zauna ka ci abinci tukuna har rana ta yi sanyi.” Dukansu biyu suka zauna suka ci tare.
9Sa'ad da mutumin, da ƙwarƙwararsa, da baransa sun tashi za su tafi, sai mahaifin macen kuma ya ce masa, “Ga shi, rana ta kusan faɗuwa, yamma kuwa ta yi, ina roƙonka, ka sāke kwana ka ji wa ranka dādi, sa'an nan ka yi sammako gobe ka kama hanyarka zuwa gida.”
10Amma mutumin bai yarda ya sāke kwana ba, sai ya tashi shi da ƙwarƙwararsa suka kama hanya. Ya kai daura da Yebus, wato Urushalima ke nan. Yana tare da jakinsa biyu da ya yi musu shimfiɗa, da ƙwarƙwararsa. 11Baran kuwa ya ce wa maigidansa, “In ka yarda mu ratse mu kwana a birnin Yebusiyawan nan.”
12Amma maigidansa ya ce masa, “Ba za mu tsaya a birnin da mutane ba Isra'ilawa ba ne. Za mu wuce zuwa Gibeya, 13mu ƙara ɗan nisa, mu tafi mu kwana a Gibeya ko a Rama.” 14Sai suka wuce, suka yi tafiyarsu. Rana ta faɗi sa'ad da suka kai Gibeya, ta yankin ƙasar Biliyaminu. 15Suka ratse don su kwana a Gibeya. Balawen ya tafi ya zauna a dandalin garin, gama ba wanda ya kai su gidansa su kwana.
16To, ga wani tsoho yana komowa daga gona da yamma. Tsohon kuwa mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu ne, yana zama a Gibeya, amma mutanen Gibeya kabilar Biliyaminu ne. 17Da dattijon ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, ya ce masa, “Ina za ka? Daga ina kuma ka fito?”
18Balawen ya ce masa, “Muna tahowa ne daga Baitalami ta Yahudiya zuwa wani lungun da take ƙasar tudu ta Ifraimu, inda nake. Na je Baitalami ta Yahudiya ne, yanzu kuwa ina komawa gida. Ba wanda ya sauke ni a gidansa. 19Ina da baro domin jakuna, ina kuma da abinci da ruwa inabi don kaina, da ƙwarƙwarata da barana, ba mu rasa kome ba.”
20Tsohon nan ya ce, “Ku zo mu je gidana, duk abin da kuke bukata zan ba ku, amma kada ku kwana a dandalin.” 21Sai ya kai su gidansa, ya ba jakan harawa, aka wanke ƙafafun baƙin, sa'an nan suka ci suka sha.
22 # Far 19.5-8 Sa'ad da suke cikin jin daɗin ci da sha, 'yan iskan da suke birnin suka zo suka kewaye gidan, suka yi ta bubbuga ƙofar, suka ce wa tsohon, “Ka fito mana da mutumin da ya zo gidanka don mu yi luɗu!”
23Tsohon kuwa ya fito wurinsu, ya ce musu, “A'a, 'yan'uwana, kada ku yi mugun abu haka, wannan ya sauka a gidana, kada ku yi wannan rashin kunya. 24Ga 'yata budurwa da ƙwarƙwararsa, bari in fito muku da su, ku yi abin da kuka ga dama da su, amma kada ku yi wa mutumin nan wannan abin kunya!” 25Amma 'yan iskan ba su yarda ba, sai Balawen ya fitar da ƙwarƙwararsa gare su. Suka yi mata faɗe, suka wulakanta ta dukan dare har kusan wayewar gari, sa'an nan suka ƙyale ta.
26Da gari ya waye, ƙwarƙwarar ta zo ta fāɗi a ƙofar gidan tsohon, inda maigidanta ya sauka, tana nan har hantsi ya cira. 27Sa'ad da Balawen ya tashi da safe, ya buɗe ƙofa, ya fita domin ya kama hanyarsa, sai ga ƙwarƙwararsa kwance a ƙofar gida, da hannuwanta a dokin ƙofar. 28Ya ce mata, “Tashi mu tafi.” Amma ba amsa. Sai ya aza gawarta a kan jaki, sa'an nan ya kama hanya zuwa gida. 29#1Sam 11.7 Da ya isa gida, ya ɗauki wuƙa ya yanyanka gawar ƙwarƙwararsa gunduwa gunduwa har goma sha biyu, ya aika a ko'ina cikin dukan ƙasar Isra'ila.
30Dukan wanda ya ga haka sai ya ce, “Ba mu taɓa ganin irin wannan abu ba, ba a kuwa taɓa yin haka ba tun daga ranar da Isra'ilawa suka fito daga ƙasar Masar sai yau. Ku yi tunani, me za mu yi a kan wannan al'amari?”

Currently Selected:

L.Mah 19: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

Video for L.Mah 19