YouVersion Logo
Search Icon

L.Mah 15

15
1Bayan 'yan kwanaki, sai Samson ya tafi ya ziyarci matarsa, ya kai mata ɗan akuya, a lokacin girbin alkama. Ya ce wa mahaifinta, “Zan shiga wurin matata a ɗakin kwana.”
Amma mahaifinta bai yardar masa ba. 2Ta ce wa Samson, “Na yi tsammani ba ka sonta ne sam, don haka sai na ba da ita ga wanda ya yi maka abokin ango. Amma ƙanwarta ta fi ta kyau. Ina roƙonka ka ɗauki ƙanwar maimakon matarka.”
3Sai Samson ya ce musu, “A wannan lokaci, zan zama marar laifi saboda abin da zan yi wa Filistiyawa.” 4Ya tafi ya kama yanyawa ɗari uku, ya haɗa wutsiyoyinsu, wato wutsiya da wutsiya, sa'an nan ya ɗaura jiniya tsakanin kowaɗanne wutsiya biyu. 5Da ya sa wa jiniyar wuta, ya sake su zuwa cikin hatsin Filistiyawa. Suka ƙone dammunan hatsi, da hatsin da take a tsaye, da gonakin zaitun.
6Filistiyawa kuwa suka ce, “Wane ne ya yi mana wannan abu?”
Sai aka ce, “Samson ne, surukin mutumin Timna, domin ya ɗauki matar Samson ya ba wanda ya yi masa abokin ango.” Filistiyawa kuwa suka je suka ƙone matar, ta mutu, suka kuma ƙone gidan mahaifinta.
7Samson ya ce musu, “Wato haka kuka yi! To, na rantse, ba zan bari ba sai na rama!” 8Ya kuwa fāɗa musu, ya kashe su da yawa. Sa'an nan ya tafi ya zauna a kogon dutsen Itam.
Samson Ya Ci Nasara a kan Filistiyawa
9Filistiyawa suka haura, suka kafa sansani a Yahudiya, suka bazu a cikin Lihai. 10Mutanen Yahuza suka ce, “Me ya sa kuka kawo mana yaƙi?”
Filistiyawa suka ce, “Mun zo ne domin mu kama Samson, mu yi masa kamar yadda ya yi mana.”
11Sa'an nan mutum dubu uku na Yahuza suka gangara zuwa kogon dutsen Itam. Suka ce wa Samson, “Ba ka sani ba Filistiyawa ne suke mulkinmu? Me ya sa ka yi mana haka?”
Shi kuwa ya amsa musu, ya ce, “Kamar yadda suka yi mini, haka ni kuma na yi musu.”
12Suka ce masa, “Mun gangara zuwa wurinka don mu ɗaure ka, mu miƙa ka gare su.”
Samson ya ce musu, “Ku rantse mini idan ba ku ne da kanku kuke so ku kashe ni ba.”
13Suka ce masa, “A'a, ba za mu kashe ka ba, mu dai za mu kama ka, mu miƙa ga Filistiyawa.” Sa'an nan suka ɗaure shi da sababbin igiyoyi biyu, suka sauko da shi daga dutsen.
14Sa'ad da ya zo Lihai, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje suna ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji ya sauko kansa da iko, sai igiyoyin da suke a ɗaure da shi suka tsintsinke kamar zaren da ya kama wuta. 15Ya kuwa sami sabon muƙamuƙin jaki, ya ɗauka ya kashe mutum dubu da muƙamuƙin. 16Sa'an nan Samson ya raira waƙa ya ce.
“Da muƙamuƙin jaki na kashe mutum dubu,
Da muƙamuƙin jaki na tsiba su tsibi-tsibi.”
17Da ya gama, ya jefar da muƙamuƙin. Sai aka ba wurin suna, Ramat-Lihai, wato tudun muƙamuƙi.
18Ƙishirwa kuwa ta kama shi ƙwarai, sai ya roƙi Ubangiji ya ce, “Kai ne ka yi wannan babbar nasara ta hannun bawanka, yanzu kuwa ko zan mutu da ƙishirwa, har Filistiyawa marasa kaciya su kama ni?” 19Allah kuwa ya buɗe wani rami daga ƙasa, sai ruwa ya ɓuɓɓugo daga ciki. Da ya sha, hankalinsa ya komo, ya wartsake. Don haka aka ba wurin suna En-hakkore, wato mai kira. Ramin yana nan a Lihai har wa yau.
20Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin a zamanin da Filistiyawa suke mulkinsu.

Currently Selected:

L.Mah 15: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in