YouVersion Logo
Search Icon

Ish 61:1-3

Ish 61:1-3 HAU

Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku. Ya aike ni in yi shela, Cewa lokaci ya yi Da Ubangiji zai ceci mutanensa, Ya kuma ci nasara a kan abokan gābansu. Ya aike ni domin in ta'azantar da masu makoki, Domin in kawo wa masu makoki a Sihiyona Farin ciki da murna maimakon baƙin ciki, Waƙar yabo maimakon ɓacin rai. Ubangiji kansa zai lura da su, Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa. Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai, Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi.

Free Reading Plans and Devotionals related to Ish 61:1-3