Ish 59
59
Faɗar Muguntar Al'ummar
1Duba, ikon Ubangiji bai kasa ba, har da ba zai yi ceto ba. Shi ba kurma ba, har da ba zai ji ba. 2Amma laifofinku suka raba tsakaninku da Allahnku. Zunubanku ne kuma suka sa ya juya daga gare ku don kada ya ji ku. 3Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma sun ƙazantu da mugunta, leɓunanku kuma suna faɗar ƙarairayi, harsunanku kuwa suna raɗar mugunta.
4Ba wanda yake kai ƙara ta gaskiya, ba wanda yake yanke shari'a da adalci. Kuna dogara ga shaidar ƙarya, kuna faɗar ƙarya, kuna ɗaukar ciki na ɓarna, ku haifi mugunta. 5Kuna ƙyanƙyashe ƙwan kāsa, kuna saƙa da saƙar gizogizo. Duk wanda ya ci ƙwayayenku zai mutu, ƙwan da ya fashe zai ƙyanƙyashe kububuwa. 6Saƙarku ba za ta yi amfani kamar tufa ba, ba za ku yi sutura da abin da kuka yi ba. Ayyukanku ayyukan mugunta ne, kuna aikata ayyukan kama-karya. 7#Rom 3.15-17 Kukan sheƙa a guje don ku aikata mugunta, kuna gaggawar zub da jinin marasa laifi. Tunaninku tunanin mugunta ne, lalatarwa da hallakarwa suna a manyan karaukunku. 8Hanyar salama ba ku san ta ba. Ba adalci a hanyoyinku, kukan karkatar da hanyoyinku, ba wanda zai yi tafiya lafiya a cikinku.
9Mutane suna cewa, “Don haka ne, yin gaskiya ya yi nisa da mu, adalci kuwa bai iske mu ba. Muna ta neman haske, sai ga duhu, muna neman haske, sai muka yi tafiya cikin duhu. 10Muna ta lalubar bango kamar makafi, muna ta lalubawa kamar marasa idanu. Da tsakar rana muke ta tuntuɓe, sai ka ce da almuru. A tsakanin waɗanda suke da cikakken ƙarfi, kamar matattu muke. 11Dukanmu muna gurnani kamar beyar, muna ta ƙugi kamar kurciyoyi. Muna ta neman adalci, amma ina. Muna ta neman ceto, amma ya yi nisa da mu.
12“Gama laifofinmu sun yi yawa a gabanka, zunubanmu kuwa suna ba da shaida gāba da mu. Laifofinmu suna tare da mu, muna kuwa sane da laifofinmu, 13wato musun Ubangiji, da ƙin bin Allah, da maganar zalunci, da ta tayarwa, da shirya ƙarairayi a zuciya, da kuma hurta su. 14Aikata gaskiya ya kawu, adalci ya tsaya daga can nesa, gama gaskiya ta fāɗi a dandali, sahihanci ba zai shiga ba. 15Gaskiya ba ta, wanda ba ya aikata mugunta ya zama ganima.”
Ubangiji ya gani, bai kuwa ji daɗi ba, da yake gaskiya ba ta. 16#Ish 63.5 Ya ga ba wani mutum, ba kuwa wanda zai taimaki waɗanda ake zalunta. Sa'an nan da ikon kansa ya yi nasara, adalcinsa ya goyi bayansa. 17#Afi 6.14,17; 1Tas 5.8 Ya rufe ƙirjinsa da sulken adalci, da kwalkwalin ceto a kansa. Ya sa rigar ɗaukar fansa, ya yafa alkyabbar ikonsa. 18Bisa ga ayyukansu, haka zai sāka musu hasala, a kan maƙiyansa kuwa ramawa, a kan abokan gābansa, zai rama, da kuma a kan ƙasashen da suke a bakin gāɓa. 19Saboda haka waɗanda suke yamma za su ji tsoron sunan Ubangiji, waɗanda suke wajen gabas kuma za su ji tsoron ɗaukakarsa, gama zai zo kamar rafi mai tsananin gudu, wanda iskar Ubangiji take korawa.
20 #
Rom 11.26
Zai zo Sihiyona ya zama mai fansa ga waɗanda suke na Yakubu, su da suka juya suka bar mugunta. 21Ubangiji ya ce, “Amma ni, wannan shi ne alkawarina da su, Ruhuna da yake tare da ku, da kalmomina da na sa a bakunanku, ba za su rabu da bakunanku ba, ko daga bakunan 'ya'yanku, ko na jikokinku, tun daga wannan lokaci har abada.”
Currently Selected:
Ish 59: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979