Ish 44
44
Ubangiji Shi Kaɗai ne Allah
1Ubangiji ya ce,
“Ka saurara yanzu, ya Isra'ila, bawana,
Zaɓaɓɓun mutanena, zuriyar Yakubu,
2Ni ne Ubangiji wanda ya halicce ku,
Tun farko, na taimake ku.
Kada ku ji tsoro, ku bayina ne,
Zaɓaɓɓun mutanena waɗanda nake ƙaunarsu.
3“Zan ba da ruwa ga ƙasa mai ƙishi,
In kuma sa rafuffuka su yi gudu a hamada.
Zan kwararo da albarka a kan 'ya'yanku,
In sa albarkata kuma a kan zuriyarku.
4Za su yi kumari kamar ciyawar da ta sami ruwa sosai,
Kamar itatuwan wardi a gefen rafuffukan ruwa mai gudu.
5“Da ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya mutane za su ce, ‘Ni na Ubangiji ne!’
Za su zo su haɗa kai da jama'ar Isra'ila.
Ko wanne zai ɗaura sunan Ubangiji a dantsensa,
Ya ce da kansa ɗaya daga cikin mutanen Allah.”
6 #
Ish 48.12; W.Yah 1.17; 2.8; 22.13 Ubangiji, wanda yake mulkin Isra'ila, ya kuma fanshe su,
Ubangiji Mai Runduna, yake faɗar wannan,
“Ni ne farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici,
Ba wani Allah sai ni.
7Ko akwai wanda zai iya yin abin da na yi,
Ya kuma fito fili ya faɗi abin da zai faru
Tun daga farko, har zuwa ƙarshe?
8Ya jama'ata, kada ku ji tsoro!
Kun sani tun daga zamanin dā can, har zuwa yanzu,
Na faɗa tun da wuri abin da zai faru.
Ku ne kuwa shaiduna!
Ko akwai wani Allah?
Ko akwai wani Allah mai iko da ban taɓa jin labarinsa ba?”
Wautar Bautar Gumaka
9Dukan waɗanda suke ƙera gumaka mutanen banza ne, gumakan da suke sa wa kuɗi da tsada kuma aikin banza ne. Waɗanda suke yi wa gumaka sujada kuwa makafi ne su, jahilai, za su sha kunya. 10Wannan aikin banza ne, mutum ya yi siffa da ƙarfe don ya yi mata sujada! 11Dukan wanda ya yi mata sujada za a ƙasƙantar da shi. Mutanen da suka ƙera gumakan, 'yan adam ne, ba wani abu ba. Bari su zo su tsaya gaban shari'a, za su razana, su kuma sha kunya.
12Maƙeri yakan ɗauki guntun ƙarfe ya sa shi a wuta ya yi aiki. Da hannunsa mai ƙarfi yana ɗaukar guduma yana bugun ƙarfen, yana mai da shi siffa. Yakan ji yunwa, da ƙishi, yakan kuma ji gajiya.
13Masassaƙi yakan auna itace. Ya zana siffa da alli, sa'an nan ya sassaƙe shi da kayan aikinsa. Ya yi shi da siffar mutum kyakkyawa, domin a ajiye shi a masujadarsu. 14Zai yiwu ya sare itacen al'ul ya yi da shi, ko kuwa ya zaɓi itacen oak, ko na kasharina daga jeji. Ko kuwa ya dasa wani itace, ya jira ruwan sama don ya sa itacen ya yi girma. 15Mutum yakan yi abin wuta da wani sashi na itacen, wani sashi kuma ya yi gunki da shi. Yakan hura wuta da wani sashi don ya ji ɗumi, yakan kuma toya gurasa. Yakan yi gunki da wani sashi, ya riƙa yi masa sujada! 16Yakan hura wuta da wani sashi domin ya gasa nama, ya ci, ya ƙoshi. Ya ji ɗumi ya ce, “Kai, ɗumi da daɗi, wutar tana da kyau!” 17Sauran itacen ya mai da shi gunki. Yana rusunawa ya yi masa sujada. Yana addu'a gare shi yana cewa, “Kai ne Allahna, ka cece ni!”
18Irin waɗannan mutane dakikai ne, har ba su san abin da suke yi ba. Sun rufe idanunsu da tunaninsu ga gaskiya. 19Masu ƙera gumaka ba su da ko tunanin da za su ce, “Na ƙone wani sashi na itacen nan. Na toya gurasa a garwashin, na kuma gasa nama, na ci shi, na kuwa ce sauran itacen zan sassaƙa gunki da shi. Ga ni yanzu, ina ta rusunawa gaban guntun itace!”
20Ya zama daidai kamar mutum ya ci toka. Manufarsa ta wauta ta ɓatar da shi, har ba yadda za a iya taimakonsa. Ba zai iya ganewa ba, gunkin da ya riƙe a hannunsa ba allah ba ne ko kaɗan.
Ubangiji Mai Fansar Isra'ila
21Ubangiji ya ce,
“Ka tuna da waɗannan abu, ya Isra'ila,
Ka tuna kai bawana ne.
Na halicce ka domin ka zama bawana,
Ba zan taɓa mantawa da kai ba.
22Na shafe zunubanka kamar baƙin girgije,
Da girgije kuma zan rufe laifofinka
Ka komo wurina, ni ne na fanshe ka.”
23Ku yi sowa ta farin ciki ya ku sammai!
Ku yi sowa ku zurfafan wurare na duniya!
Ku yi sowa ta murna, ku duwatsu, da kowane itace na jeji!
Ubangiji ya fanshi mutanensa, Isra'ila,
Saboda haka ya nuna girmansa.
24“Ni ne Ubangiji, Mahaliccinku, Mai Fansarku.
Ni ne Ubangiji, Mahaliccin dukkan abu.
Ni kaɗai na shimfiɗa sammai,
Ba wanda ya taimake ni sa'ad da na yi duniya.
25 #
1Kor 1.20
Na sa masu duba su zama wawaye,
Na sassāke annabce-annabcen masanan taurari.
Na bayyana kuskuren maganar masu hikima,
Na kuma nuna masu hikimarsu wauta ce.
26Amma sa'ad da bawana ya yi annabci,
Sa'ad da na aika da manzona domin ya bayyana shirye-shiryena,
Na sa waɗannan shirye-shirye da annabce-annabce su cika.
Ina faɗa wa Urushalima, cewa mutane za su sāke zauna a can,
Za a kuma sāke gina biranen Yahuza.
Waɗannan birane za su daina zama kufai.
27Na yi umarni na sa teku ta ƙafe.
28 #
2Tar 36.23; Ezra 1.2 Na ce wa Sairus, ‘Kai ne wanda za ka yi mulki domina,
Za ka yi abin da nake so ka yi,
Za ka ba da umarni, cewa a sāke gina Urushalima,
A kuma kafa harsashin ginin Haikali.’ ”
Currently Selected:
Ish 44: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979