YouVersion Logo
Search Icon

Ish 38

38
Ciwon Sarki Hezekiya da Warkewarsa
(2Sar 20.1-11; 2Tar 32.24-26)
1A lokacin nan sai sarki Hezekiya ya kamu da rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya je wurinsa domin ya gaishe shi, ya ce masa, “Ubangiji ya ce ka kintsa kome daidai, gama ba za ka warke ba. Ka yi shirin mutuwa.”
2Hezekiya kuwa ya juya wajen bango ya yi addu'a, ya ce, 3“Ya Ubangiji, ka tuna, na bauta maka da aminci da biyayya, na kuma yi ƙoƙarin aikata abin da kake so in yi.” Sai ya fara kuka mai zafi.
4Sa'an nan Ubangiji ya umarci Ishaya, 5cewa ya koma wurin Hezekiya ya faɗa masa, “Ni, Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, na ji addu'arka, na kuma ga hawayenka, zan bar ka ka ƙara shekara goma sha biyar nan gaba. 6Zan cece ka, da wannan birni na Urushalima, daga Sarkin Assuriya, zan ci gaba da kiyaye birnin.”
7Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ubangiji zai nuna maka alama da za ta tabbatar maka zai cika alkawarinsa. 8Ubangiji zai komar da inuwa baya da taki goma, bisa ga ma'aunin rana na sarki Ahaz.” Inuwa kuwa ta koma da baya daga fuskar rana har mataki goma.
9Bayan da Hezekiya ya warke daga rashin lafiyarsa, sai ya rubuta wannan waƙar yabo.
10Na zaci a gaɓar ƙarfina
Zan tafi lahira,
Ba zan ƙara rayuwa ba.
11Na zaci ba zan ƙara ganin Ubangiji ba
A wannan duniya ta masu rai,
Ko kuwa in ga wani mutum mai rai.
12An datse raina, ya ƙare,
Kamar alfarwar da aka kwance,
Kamar saƙar da aka yanke,
Na zaci Allah zai kashe ni.
13Dare farai na yi ta kuka saboda azaba,
Sai ka ce zaki yake kakkarya ƙasusuwana.
Na zaci Allah zai kashe ni.
14Muryata ƙarama ce, ba kuma ƙarfi,
Na kuwa yi kuka kamar kurciya,
Idanuna sun gaji saboda duban sama.
Ya Ubangiji, ka cece ni daga dukan wannan wahala.
15Me zan iya faɗa? Ubangiji ne ya yi wannan.
Ina da ɓacin zuciya, ba na iya barci.
16Ya Ubangiji, zan bi ka, kai kaɗai.
Ka warkar da ni, ka bar ni da rai.
17Ɓacin zuciyata zai juya ya zama salama.
Ka ceci raina daga dukan hatsari,
Ka gafarta dukan zunubaina.
18Ba wanda yake yabonka a lahira,
Matattu ba za su iya dogara ga amincinka ba.
19Masu rai ne suke yabonka,
Kamar yadda nake yabonka yanzu.
Iyaye za su faɗa wa 'ya'yansu irin amincinka.
20Ya Ubangiji, ka riga ka warkar da ni!
Za mu kaɗa garayu mu kuma raira waƙar yabo,
Za mu raira yabo cikin Haikalinka muddin ranmu.
21Haka ya faru bayan da Ishaya ya faɗa wa sarki ya sa curin da aka yi da 'ya'yan ɓaure a kan marurun, ya kuwa warke. 22Sarki Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan iya zuwa Haikali?”

Currently Selected:

Ish 38: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in