Ish 23
23
Annabci a kan Taya da Sidon
1 #
Eze 26.1—28.19; Yow 3.4-8; Amos 1.9,10; Zak 9.1-4; Mat 11.21,22; Luk 10.13,14 Wannan shi ne jawabi a kan Taya.
Ku yi hargowa ta baƙin ciki, ku matuƙan jiragen ruwan teku! An lalatar da tashar jiragen ruwan garinku na Taya. Gidajenta da gaɓarta sun rurrushe. Sa'ad da jiragen ruwanku suka komo daga Kubrus za ku ji labarin. 2Ku yi kuka ku fataken Sidon! Kun aika da mutane 3a hayin teku don su yi muku saye da sayarwa na hatsin da ake nomawa a Masar, su yi hulɗa da dukan sauran al'umma.
4Birnin Sidon, ke abar kunya ce! Teku da manyan zurfafan ruwaye sun yanke hulɗa da ke, sun ce, “Ban taɓa haihuwar 'ya'ya ba, ban taɓa goyon 'ya'ya mata ko maza ba.”
5Har Masarawa ma za su firgita su razana, sa'ad da suka ji, cewa an hallakar da Taya.
6Ku yi ruri da baƙin ciki, ku jama'ar bakin teku, ku yi ƙoƙari ku tsere zuwa Tarshish! 7Ya yiwu kuwa a ce wannan Taya ce birnin farin ciki, wadda aka kafa ta tuntuni? Wannan kuwa ita ce birnin da yake aikawa da mutane hayin teku su kafa nahiyoyi? 8Wane ne wannan wanda ya shirya ya aukar wa Taya da wannan duka, wannan muhimmiyar alkarya, wadda fatakenta hakimai ne, waɗanda ake ɗaukaka su fiye da sauran mutane a duniya? 9Ubangiji Mai Runduna ne ya shirya wannan! Ya shirya haka ne don ya kawo ƙarshen girmankanta saboda abin da suka aikata, don ya ƙasƙantar da manyan mutanenta.
10Ku je ku nomi ƙasarku jama'ar nahiyoyin Tarshish! Ba wanda zai ƙara kiyaye ku. 11Ubangiji ya miƙa dantsensa a kan tekun, ya hamɓarar da mulkoki. Ya umarta a lalatar da manyan biranen ciniki na Taya. 12Birnin Sidon, farin cikinki ya ƙare. Ana zaluntar jama'arki, ko da za su tsere zuwa Kubrus duk da haka ba za su zauna lafiya ba.
13(Mutanen Babila ne, ba na Assuriya ba, waɗanda suka bar namomin jeji su murƙushe Taya. Mutanen Babila ne suka gina hasumiya, suka ragargaza kagarar Taya suka bar birnin kango.)
14Ku yi hargowar baƙin ciki ku matuƙan jiragen teku! An hallaka birnin da kuke dogara gare shi.
15Lokaci yana zuwa da za a manta da Taya har shekara saba'in, gwargwadon kwanakin sarki. Bayan waɗannan shekaru kuma, Taya za ta yi waƙa irin ta karuwa, cewa
16“Ɗauki garayarki, kewaya cikin gari,
Ayya, an manta da karuwa!
Yi kiɗa, sāke raira waƙoƙinki,
Don ki komo da masoyanki.”
17Bayan shekara saba'in ɗin, Ubangiji zai bar Taya ta koma a kan cinikinta na dā, za ta ba da kanta ijara ga dukan mulkokin duniya. 18Kuɗin da ta samu ta kasuwanci za a keɓe wa Ubangiji. Ba za ta tara wa kanta ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada su za su yi amfani da kuɗinta don su saya wa kansu abinci da sutura da suke bukata.
Currently Selected:
Ish 23: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979