YouVersion Logo
Search Icon

Ish 19

19
Annabci a kan Masar
1 # Irm 46.2-26; Eze 29.1—32.32 Wannan shi ne jawabi a kan Masar.
Ubangiji yana zuwa Masar a kan girjije a sukwane. Gumakan Masarawa za su yi rawar jiki a gabansa, zuciyar Masarawa za ta karai. 2Ubangiji ya ce, “Zan ta da hargitsi a yi yaƙin basasa a Masar, ɗan'uwa ya yi gāba da ɗan'uwa, maƙwabci kuma gaba da maƙwabci. Biranen da suke hamayya za su yi faɗa da juna, sarakunan da suke hamayya kuma za su yi faɗa saboda neman iko. 3Zan warware shirye-shiryen Masarawa in sa ku karai. Za su roƙi taimako ga gumakansu, za su je kuma su yi shawara da mabiyansu, su kuma nemi shawarar kurwar matattu. 4Zan ba da Masarawa a hannun azzalumi a hannun mugun sarki kuma da zai mallake su. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗi wannan.”
5Ruwan Kogin Nilu zai ƙafe, a hankali kogin zai bushe. 6Mazaunan kogin za su ji wari sa'ad da yake ƙafewa a hankali. Iwa da jema za su bushe. 7Dukan amfanin gonakin da aka shuka a gaɓar Kogin Nilu za su bushe, iska ta fyauce su. 8Duk wanda sana'arsa ta kama kifi ce a Kogin Nilu zai yi ƙugi ya yi kuka, gama ƙugiyoyinsa da tarunansa za su zama marasa amfani. 9Waɗanda suke yin tufafin lilin za su fid da zuciya, 10shugabanni da ma'aikata za su karai su kuma damu.
11Shugabannin birnin Zowan wawaye ne! Mutanen Masar mafi hikima za su ba da gurguwar shawara! Ta ƙaƙa za su iya dosar sarki su faɗa masa, cewa su ne suka gāji masana da sarakuna na dā can? 12Sarkin Masar, ina mashawartan nan naka masu hikima? Watakila za su iya faɗa maka shirye-shiryen da Ubangiji Mai Runduna ya yi domin Masar. 13Shugabannin Zowan da na Memfis wawaye ne. Su ake zaton za su bi da al'ummar, amma sai suka bi da su a karkace. 14Ubangiji ne ya sa su ba da gurguwar shawara. Sakamakon haka sai Masar ta yi ta aikata dukan abu a hugunce, tana tangaɗi kamar bugagge wanda santsi na kwasarsa cikin aman da ya yi. 15A Masar duka, attajiri da matalauci, ƙarami ko babba, ba wanda zai iya yin wani taimako.
16Lokaci zai yi in da zuciyar mutanen Masar za ta narke kamar mata. Za su yi rawar jiki da razana lokacin da suka ga Ubangiji Mai Runduna ya miƙa hannunsa don ya hukunta su. 17Mutanen Masar za su firgita saboda Yahuza, kowane lokaci za su tuna da ƙaddarar da Ubangiji Mai Runduna ya shirya dominsu.
18A wannan rana, za a yi amfani da harshen Ibrananci a birane biyar na Masar. Mutanen da suke can za su riƙa yin rantsuwarsu da sunan Ubangiji Mai Runduna. Za a sa wa ɗaya daga cikin biranen nan suna, “Birnin Hallaka.”
19A wannan rana, za a gina wa Ubangiji bagade a ƙasar Masar, za a keɓe masa ginshiƙi na dutse a kan iyakar Masar. 20Za su zama alamu na kasancewar Ubangiji Mai Runduna a Masar. Sa'ad da aka zalunci mutanen da suke can, za su yi kira ga Ubangiji su nemi taimako, zai aika musu wanda zai kuɓutar da su. 21Ubangiji zai bayyana kansa ga mutanen Masar, sa'ad da ya yi haka kuwa, za su karɓe shi, su yi masa sujada, su kuma kawo masa hadayu da sadakoki. Za su yi masa alkawarai ƙwarara, su kuwa cika abin da suka alkawarta. 22Ubangiji zai hukunta Masarawa, amma zai warkar da su. Za su juyo gare shi, shi kuma zai ji addu'o'insu ya warkar da su.
23A wannan rana, za a yi wata babbar hanya tsakanin Masar da Assuriya. Mutanen ƙasashen nan biyu za su yi ta kai da kawowa tsakaninsu, al'ummai biyu za su yi sujada tare. 24A wannan rana, za a lasafta Isra'ila tare da Masar da Assuriya, waɗannan al'ummai uku za su zama albarka ga dukan duniya. 25Ubangiji Mai Runduna zai sa musu albarka, ya ce, “Zan sa muku albarka, ke Masar, jama'ata, da suke Assuriya wadda na halitta, da ke kuma Isra'ila zaɓaɓɓiyar jama'ata.”

Currently Selected:

Ish 19: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in