Yush 7
7
Zunubin Isra'ila da Tayarwarta
1“Sa'ad da zan warkar da mutanen Isra'ila,
Sai zunubin Ifraimu da muguntar Samariya su bayyana,
Gama suna cin amana.
Ɓarawo yakan fasa, ya shiga,
'Yan fashi suna fashi a fili,
2Amma ba su tunani,
Cewa zan tuna da dukan muguntarsu.
Yanzu ayyukansu sun kewaye su,
Ina ganinsu.
3“Suna faranta zuciyar sarki da muguntarsu,
Na shugabanni kuma da ƙarairayinsu.
4Dukansu mazinata ne,
Suna kama da tanda da aka zafafa,
Wadda matoyi ya daina iza mata wuta,
Tun daga lokacin cuɗe kullu
Har zuwa lokacin da yisti ya tasar da shi.
5A ranar bikin sarki,
Sukan sa sarki da shugabanni su bugu da ruwan inabi.
Yakan yi cuɗanya da shakiyai.
6Zukatansu suna ƙuna da ƙullaƙulle kamar tanderu.
Fushinsu na ci dare farai,
Da safe fushinsu yana ci bal-bal kamar harshen wuta.
7“Dukansu suna da zafi kamar tanderu.
Suna kashe masu mulkinsu.
Dukan sarakunansu sun faɗi.
Ba wanda ya kawo mini kuka.”
Ifraimu ta Haɗu da Al'ummai
8Ubangiji ya ce, “Mutanen Ifraimu sun haɗa kansu da al'ummai,
Sun zama kamar wainar da ba a juya ba.
9Baƙi sun cinye ƙarfinsu, su kuwa ba su sani ba,
Furfura ta faso musu, amma ba su sani ba.
10Girmankan mutanen Isra'ila ya kai ƙararsu,
Duk da haka ba wanda ya komo wurin Ubangiji Allahnsu,
Ba su kuwa neme shi ba.
11Ifraimu kamar kurciya take, marar wayo, marar hankali,
Takan tafi Masar da Assuriya neman taimako.
12Lokacin da suke tafiya, zan shimfiɗa musu ragata,
Zan saukar da su ƙasa kamar yadda akan yi wa tsuntsun da yake tashi sama.
Zan hukunta su saboda mugayen ayyukansu.
13“Tasu ta ƙare, gama sun ratse, sun rabu da ni.
Halaka za ta auka musu domin sun tayar mini.
Ko da yake zan cece su, duk da haka suna faɗar karya a kaina.
14Ba su yi kuka gare ni da zuciya ɗaya ba,
Sa'ad da suke kuka a gadajensu,
Sun tsattsaga jikinsu domin abinci da ruwan inabi.
Sun yi mini tawaye.
15Ko da yake na horar da su, na ƙarfafa damatsansu,
Duk da haka suna shirya mini maƙarƙashiya.
16Sun juya mini baya, suna bin gunkin nan Ba'al.
Suna kama da tankwararren baka.
Za a kashe shugabanninsu da takobi
Saboda maganganunsu na fariya.
Za su zama abin ba'a a ƙasar Masar.”
Currently Selected:
Yush 7: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979