Yush 12
12
1Ifraimu tana kiwon iska,
Tana ta bin iskar gabas dukan yini.
Tana riɓaɓɓanya ƙarya da kamakarya.
Tana ƙulla yarjejeniya da Assuriya,
Tana kai mai a Masar.”
2Ubangiji yana da magana game da mutanen Yahuza,
Zai hukunta Isra'ila saboda hanyoyinta,
Zai sāka mata gwargwadon ayyukanta.
3 #
Far 25.26
#
Far 32.24-26
A cikin mahaifa kakansu Yakubu ya kama diddigen ɗan'uwansa,
Sa'ad da ya zama baligi ya yi kokawa da Allah.
4 #
Far 28.10-22
Ya yi kokawa da mala'ika ya yi rinjaye.
Ya yi kuka, ya roƙi albarka.
Ya sadu da Allah a Betel,
A can Allah ya yi magana da shi.
5Ubangiji Allah Mai Runduna,
Sunansa Ubangiji,
6Sai ku koma wurin Allahnku,
Ku yi alheri, ku yi adalci,
Ku saurari Allahnku kullayaumin.
7Ubangiji ya ce, “Ɗan kasuwa wanda yake da ma'aunin algus a hannunsa.
Yana jin daɗin yin zalunci.
8Mutanen Ifraimu sun ce, ‘Hakika, mun zama attajirai,
Mun samar wa kanmu dukiya.
A cikin harkokinmu ba za a sami wata mugunta ba.’
9 #
L.Fir 23.42,43 Ni ne Ubangiji Allahnku tun daga ƙasar Masar,
Zan kuma sa ku zauna cikin alfarwai,
Kamar lokatan ƙayyadaddun idodi.
10“Na yi magana da annabawa,
Ni ne na ba da wahayi da yawa,
Da misalai kuma ta wurin annabawa.
11Idan akwai laifi a Gileyad,
Hakika za su zama wofi.
A Gilgal ana sadaka da bijimai,
Bagadansu za su zama kamar tsibin duwatsu
A gyaffan kunyoyin gona.”
12 #
Far 29.1-20
Kakanmu Yakubu ya gudu zuwa ƙasar Aram,
A can Isra'ila ya yi barantaka saboda mace,
Saboda mace ya yi kiwon tumaki.
13 #
Fit 12.50,51 Ta wurin annabi Ubangiji ya fito da mutanen Isra'ila daga Masar,
Ta wurin annabi kuma ya kiyaye su.
14Mutanen Ifraimu sun yi muguwar tsokana mai ta da fushi,
Domin haka Ubangiji zai ɗora musu hakkin jini a kansu,
Zai saka musu cin mutuncin da suka yi.
Currently Selected:
Yush 12: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979