YouVersion Logo
Search Icon

Ibr 9

9
Wurare Tsarkaka na Duniya da na Sama
1Alkawarin farko yana da ka'idodinsa na yin sujada, da kuma wurin yinta tsattsarka wanda mutane suka shirya. 2#Fit 26.1-30; Fit 25.31-40; Fit 25.23-30 Wato, an kafa alfarwa wadda sashinta na farko yake da fitila, da tebur, da kuma keɓaɓɓiyar gurasa. Ana kiran wannan sashi Wuri Mai Tsarki. 3#Fit 26.31-33 Bayan labule na biyu kuma, akwai sashin alfarwa da ake kira Wuri Mafi Tsarki. 4#Fit 30.1-6; Fit 25.10-16; Fit 16.33; L.Ƙid 17.8-10; Fit 25.16; M.Sh 10.3-5 A cikinsa kuwa da faranti na zinariya domin ƙona turare, da kuma akwatin alkawari da aka yi masa laffa da zinariya ta kowane gefe. A cikinsa kuwa akwai tasar zinariya da manna a ciki, da sandar Haruna wadda ta yi toho, da kuma allunan dutse na alkawarin nan. 5#Fit 25.18-22 A bisa akwatin alkawari kuma akwai kerubobin nan na ɗaukakar Allah, waɗanda suka yi wa murfin akwatin nan laima. Ba za mu iya yin maganar waɗannan abubuwa filla filla ba a yanzu.
6 # L.Ƙid 18.2-6 In an gama waɗannan shirye-shirye haka, sai firistoci kullum su riƙa shiga sashin farko an alfarwar, suna hidimarsu ta ibada. 7#L.Fir 16.2-34 Amma na biyun, sai babban firist kaɗai yake shiga, shi ma kuwa sai sau ɗaya a shekara, sai kuma da jini wanda yakan miƙa saboda kansa, da kuma kurakuran jama'a. 8Ta haka Ruhu Mai Tsarki yake yin ishara, cewa ba a buɗe hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin alfarwa tana nan a tsaye, 9wadda take ishara ce ga wannan zamani. Bisa ga wannan ishara akan yi miƙa sadaka da hadaya, amma ba sa iya kammala lamirin mai ibadar, 10tun da yake ci da sha da wankewanke iri iri kaɗai suke shafa, ka'idodi ne a game da jiki kurum, waɗanda aka sa kafin a daidaita al'amari.
11Amma Almasihu ya riga ya zo, yana babban firist na kyawawan abubuwan da suke akwai. Masujadar da yake hidima a ciki mafi ɗaukaka ce, mafi kammala kuwa (wadda ba yin mutum ba ce, wato, ba ta wannan halittacciyar duniya ba ce). 12Almasihu ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak, ba ƙari, ba kuwa ta wurin jinin awaki ko na 'yan maruƙa ya shiga ba, sai dai ta wurin nasa jini, ya samo mana madawwamiyar fansa. 13#L.Fir 16.15,16; L.Ƙid 19.9,17-19 To, jinin awaki ne fa da na bijimai, da kuma tokar karsana da ake yayyafa wa waɗanda suka ƙazantu, suke tsarkake su da tsabtacewar jiki, 14balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.
15Saboda haka, shi ne matsakancin sabon alkawari, domin waɗanda aka kira su karɓi dawwamammen gādon da aka yi musu alkawari, tun da yake an yi wata mutuwa mai fansar waɗanda suke keta umarni a game da alkawarin farko. 16A game da al'amarin wasiyya, lalle ne a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta tukuna. 17Domin ba a zartar da wasiyya sai bayan an mutu, tun da yake ba a yin aiki da ita muddin wanda ya yi ta yana a raye. 18Ashe kuwa, mun ga alkawarin nan na farko, ba a tabbatar da shi ba, sai a game da jini. 19#Fit 24.6-8 Don bayan Musa ya sanar da kowane umarnin Shari'a ga dukan jama'a, sai ya ɗebi jinin 'yan maruƙa da na awaki, tare da ruwa, da jan ulu, da kuma ganyen izob, ya yayyafa wa Littafin kansa, da kuma duk jama'a, 20yana cewa, “Wannan shi ne jini na tabbatar alkawarin nan, da Allah ya yi umarni a game da ku.” 21#L.Fir 8.15Haka kuma, ya yayyafa jinin ga alfarwar nan, da dukan kayanta na yin hidima. 22#L.Fir 17.11 Hakika, bisa ga Shari'a, kusan kowane abu da jini ake tsarkake shi, in ba a game da zubar da jini ba kuwa, to, ba gafara.
Almasihu ya Miƙa Kansa domin Kawar da Zunubi
23Da waɗannan abubuwa ne, ya wajaba a tsarkake makamantan abubuwan da suke a Sama, sai dai ainihin abubuwan Sama za a tsarkake su ne da hadayar da ta fi waɗannan kyau. 24Domin Almasihu bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake sura ne kawai na gaskataccen, a'a Sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu. 25Ba kuwa domin ya riƙa miƙa kansa hadaya a kai a kai ba ne, kamar yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki a kowace shekara da jinin da ba nasa ba ne. 26In da haka ne, ashe, da sai lalle ya yi ta shan wuya a kai a kai ke nan, tun daga farkon duniya. Amma a yanzu ya bayyana sau ɗaya tak, a ƙarshen zamanai, domin ya kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya. 27Tun da yake an ƙaddara wa ɗan adam ya mutu sau ɗaya ne, bayan haka kuma sai shari'a, 28#Ish 53.12 shi Almasihu ma, da aka miƙa shi hadaya sau ɗaya tak, domin ya ɗauke zunuban mutane da yawa, zai sāke bayyana, bayyana ta biyu, ba a kan maganar kawar da zunubi ba, sai dai domin yă ceci waɗanda suke ɗokin zuwansa.

Currently Selected:

Ibr 9: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in