Ibr 7
7
Firist Kwatancin Malkisadik
1 #
Far 14.17-20
Shi wannan Malkisadik, Sarkin Urushalima, firist na Allah Maɗaukaki, ya gamu da Ibrahim a lokacin da Ibrahim yake dawowa daga kisan sarakuna, ya sa masa albarka. 2Shi ne kuwa Ibrahim ya ba shi ushirin kome. Da farko dai, kamar yadda ma'anar sunansa take, shi sarkin adalci ne, sa'an nan kuma Sarkin Urushalima ne, wato, sarkin salama. 3Shi ba shi da uwa ko uba, ba a kuma san asalinsa ba. Ba shi da ranar haihuwa balle ranar mutuwa, yana dai kama da Ɗan Allah, firist ne har abada.
4Kai, ku dubi irin girmansa! Har kakanmu Ibrahim ma ya ba shi ushirin ganima! 5#L.Ƙid 18.21 Ga shi kuma, waɗansu na zuriyar Lawi, in sun sami matsayin firist, akan umarce su bisa ga Shari'a su karɓi ushiri a gun jama'a, wato a gun 'yan'uwansu, ko da yake su ma zuriyar Ibrahim ne. 6Amma wannan, wanda ma ba a asalin Lawi yake ba, ya karɓi ushiri a gun Ibrahim, har ya sa masa albarka, shi ma da aka yi wa alkawarai. 7Ai, ba abin musu ba ne, cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka. 8Ga shi, a nan masu karɓar ushiri, mutane ne masu mutuwa, a can kuwa mai karɓar wanda aka shaida shi, rayayye ne. 9A ma iya cewa ko Lawi ma da kansa, mai karɓar ushiri, ya ba da ushiri ta wurin Ibrahim, 10don shi Lawi yana daga tsatson kakansa Ibrahim, sa'ad da Ibrahim ɗin ya gamu da Malkisadik.
11Gama da a ce kammala tana samuwa ta wurin firistoci na zuriyar Lawi (don ta gare su ne jama'a suka karɓi shari'a), wace bukata kuma ake da ita ta wani firist dabam ya bayyana kwatancin ɗabi'ar Malkisadik, wanda za a ambata ba kwatancin ɗabi'ar Haruna ba? 12Domin in an sauya matsayin firistoci, sai tilas a sauya Shari'a kuma. 13Domin kuwa shi wannan da aka faɗi waɗannan abubuwa a game da shi, ai, na wata kabila ne dabam, wadda ba waninta da ya taɓa hidimar bagadin hadaya. 14Tabbatacce ne, cewa Ubangijinmu ya fito daga zuriyar Yahuza ne, Musa kuwa bai ce kome ba a game da kabilar nan a kan zancen firistoci.
15Wannan kuma ya ƙara fitowa fili sosai, sa'ad da wani firist dabam ya bayyana kamar Malkisadik, 16wanda kuwa ya zama firist, ba bisa ga wata ka'ida ta al'adar 'yan adam ba, sai dai ta wurin ikon rai marar gushewa. 17#Zab 110.4 Domin an shaide shi da cewa,
“Kai firist ne na har abada,
Kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.”
18Ta wani hali an soke wani umarni ta dā saboda rauninsa da kuma rashin amfaninsa, 19don Shari'a ba ta kammala kome ba, ta wani hali kuma an shigo da wani bege wanda yake mafi kyau, ta wurinsa kuwa muke kusatar Allah.
20Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. 21#Zab 110.4 Waɗancan sun zama firistoci, ba tare da an yi musu rantsuwa ba, amma wannan kam, sai da aka yi masa rantsuwa, da Allah ya ce masa,
“Ubangiji ya rantse,
Ba kuwa zai ta da maganarsa ba cewa,
‘Kai firist ne har abada.’ ”
22A sanadin wannan ne Yesu ya zama lamunin alkawarin da ya fi wancan nesa.
23Waɗancan firistoci, an yi su da yawa, domin mutuwa ta hana su tabbata a aikin. 24Amma shi da yake madawwami ne, yana da matsayinsa na firist wanda ba ya komawa hannun wani. 25Saboda haka, yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da yake kullum a raye yake saboda yi musu addu'a.
26Irin babban firist wanda muke bukata ke nan, mai tsarki, marar aibu, marar cikas, keɓaɓɓe daga masu zunubi, ɗaukakke kuma birbishin sammai. 27#L.Fir 9.7 Ba zai miƙa hadaya kowace rana kumar waɗancan manyan firistocin ba, wato, da farko saboda zunubansa, sa'an nan kuma saboda na jama'a. Wannan ya yi ta ne sau ɗaya tak, lokacin da ya miƙa kansa hadaya. 28Wato shari'a tana sa mutane su zama manyan firistoci duk da rauninsu, amma maganar nan ta rantsuwa da ta sauko bayan Shari'a, ta sa Ɗa wanda yake kammalalle har abada.
Currently Selected:
Ibr 7: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979