YouVersion Logo
Search Icon

Hag 2

2
Darajar Sabon Haikalin
1A rana ta ashirin da ɗaya ga watan bakwai sai Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai ya ce, 2“Ka yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, ka ce, 3#Ezra 3.12 ‘Wa ya ragu a cikinku da ya ga wannan Haikali da darajarsa ta dā? Ƙaƙa kuke ganinsa yanzu? A ganinku ba a bakin kome yake ba? 4Duk da haka yanzu sai ku yi ƙarfin hali, kai Zarubabel, da kai Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukanku mutanen ƙasar, ku kama aikin, gama ina tare da ku. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa. 5#Fit 29.45,46 Na yi muku alkawari a sa'ad da kuka fito daga Masar, cewa Ruhuna zai zauna tare da ku, haka yake yanzu, kada ku ji tsoro!’
6 # Ibr 12.26 “Ni Ubangiji Mai Runduna, ina cewa ba da jimawa ba, zan girgiza sammai, da duniya, da teku, da sandararriya ƙasa. 7Zan kuma girgiza al'umman duniya duka don dukiyar al'umman duniya ta samu. Zan kuwa cika Haikalin nan da daraja. 8Azurfa tawa ce, zinariya kuma tawa ce. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa. 9Darajar Haikalin nan ta nan gaba za ta fi ta dā. A wannan wuri zan ba da salama. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
An Tsauta wa Mutane saboda Rashin Amincinsu
10A rana ta ashirin da huɗu ga watan tara a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji kuma ya yi magana da annabi Haggai ya ce, 11“Ka tambayi firistoci a kan wannan doka. 12‘Idan mutum yana riƙe da nama tsattsarka a rigarsa, idan rigar ta taɓa gurasa, ko dafaffen abinci, ko ruwan inabi, ko mai, ko kowane irin abinci, wannan zai sa abin ya tsarkaka?’ ”
Sai firistocin suka amsa suka ce, “A'a.”
13 # L.Ƙid 19.11-22 Sai kuma Haggai ya ce, “Idan wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa, wannan zai sa abin ya ƙazantu?”
Sai firistoci suka ce, “Wannan zai sa abin ya ƙazantu!”
14Sai Haggai ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Haka yake da wannan jama'a da wannan al'umma da take gabana da kowane irin aikinsu. Abin da suke miƙawa kuma marar tsarki ne.
15“ ‘Ina roƙonku, ku tuna a ran nan tun kafin a ɗora dutse a kan dutse na gina Haikalin Ubangiji, yaya kuke? 16A lokacin, idan wani ya tafi wurin tsibin da zai auna mudu ashirin, sai ya iske mudu goma kawai. Idan kuma wani ya tafi wurin matse ruwan inabi don ya ɗebo mudu hamsin, sai ya tarar da mudu ashirin kawai. 17Na aukar muku da burtuntuna, da fumfuna, da ƙanƙara a kan amfanin gonakinku, duk da haka ba ku komo wurina ba, ni Ubangiji na faɗa. 18Yanzu ku tuna a ran nan, wato rana ta ashirin da huɗu ga watan tara, tun daga ranar da aka aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji. 19Ba sauran iri a rumbu. Kurangar inabi kuma, da itacen ɓaure, da rumman, da itacen zaitun ba su ba da amfani ba tukuna. Amma daga wannan rana zuwa gaba zan sa muku albarka.’ ”
Ubangiji Ya Yi wa Zarubabel Alkawari
20Ubangiji kuma ya yi magana da Haggai a rana ta ashirin da huɗu ga watan, ya ce, 21“Ka faɗa wa Zarubabel, mai mulkin Yahuza cewa, ‘Ina cikin shirin girgiza sammai da duniya. 22Zan kuma hamɓare gadon sarautan daula, in kuma karya ƙarfin daular al'umman. Zan kuma hallaka karusai da mahayansu. Sojojin dawakai kuma za su kashe junansu da takuba. 23A wannan rana, ni Ubangiji Mai Runduna, zan ɗauke ka, kai Zarubabel, bawana ɗan Sheyaltiyel, in maishe ka kamar zobe mai hatimi, gama na zaɓe ka, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’ ”

Currently Selected:

Hag 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy