YouVersion Logo
Search Icon

Far 5

5
Zuriyar Adamu
(1Tar 1.1-4)
1 # Far 1.27,28 Wannan shi ne littafin asalin Adamu. A sa'ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin siffar Allah. 2#Mat 19.4; Mar 10.6 Namiji da ta mace ya halicce su, ya sa musu albarka, ya sa musu suna, Mutum, sa'ad da aka halicce su. 3Da Adamu ya yi shekara ɗari da talatin, ya haifi ɗa cikin kamanninsa da cikin siffarsa, ya kuwa sa masa suna Shitu. 4Bayan da Adamu ya haifi ɗansa Shitu, ya yi shekara ɗari takwas, sa'an nan ya haifi 'ya'ya mata da maza. 5Haka nan kuwa dukan kwanakin Adamu shekara ce ɗari tara da talatin, ya rasu.
6Da Shitu ya yi shekara ɗari da biyar, ya haifi Enosh. 7Bayan da Shitu ya haifi Enosh ya rayu shekara ɗari takwas da bakwai, ya haifi 'ya'ya mata da maza. 8Haka nan kuwa dukan kwanakin Shitu shekara ce ɗari tara da goma sha biyu, ya rasu.
9Da Enosh ya yi shekara tasa'in, ya haifi Kenan. 10Bayan Enosh ya haifi Kenan ya rayu shekara ɗari takwas da goma sha biyar, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 11Haka nan kuwa dukan kwanakin Enosh shekara ce ɗari tara da biyar, ya rasu.
12Sa'ad da Kenan ya yi shekara saba'in, ya haifi Mahalalel. 13Bayan da Kenan ya haifi Mahalalel ya yi shekara ɗari takwas da arba'in, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 14Haka nan kuwa dukan kwanakin Kenan shekara ce ɗari tara da goma, ya rasu.
15Sa'ad da Mahalalel ya yi shekara sittin da biyar ya haifi Yared. 16Bayan da Mahalalel ya haifi Yared, ya yi shekara ɗari takwas da talatin, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza. 17Haka nan kuwa dukan kwanakin Mahalalel shekara ce ɗari takwas da tasa'in da biyar, ya rasu.
18Sa'ad da Yared ya yi shekara ɗari da sittin da biyu, ya haifi Anuhu. 19Bayan da Yared ya haifi Anuhu ya yi shekara ɗari takwas ya haifi 'ya'ya mata da maza. 20Haka nan kuwa dukan kwanakin Yared shekara ce ɗari tara da sittin da biyu, ya rasu.
21Sa'ad da Anuhu ya yi shekara sittin da biyar, ya haifi Metusela. 22Bayan da Anuhu ya haifi Metusela, ya yi tafiya tare da Allah shekara ɗari uku ya haifi 'ya'ya mata da maza. 23Haka nan kuwa dukan kwanakin Anuhu shekara ce ɗari uku da sittin da biyar. 24#Ibr 11.5; Yahu 1.14 Anuhu ya yi tafiya tare da Allah, Allah kuwa ya ɗauke shi, ba a ƙara ganinsa ba.
25Sa'ad da Metusela ya yi shekara ɗari da tamanin da bakwai, ya haifi Lamek. 26Bayan da Metusela ya haifi Lamek ya yi shekara ɗari bakwai da tamanin da biyu, ya haifi 'ya'ya mata da maza. 27Haka nan kuwa dukan kwanakin Metusela shekara ce ɗari tara da sittin da tara, ya rasu.
28Sa'ad da Lamek ya yi shekara ɗari da tamanin da biyu, ya haifi ɗa, 29ya sa masa suna Nuhu, yana cewa, “Daga gare shi za mu sami sauƙin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la'anta.” 30Bayan da Lamek ya haifi Nuhu ya yi shekara ɗari biyar da tasa'in da biyar, ya haifi 'ya'ya mata da maza. 31Haka nan kuwa dukan kwanakin Lamek shekara ce ɗari bakwai da saba'in da bakwai, ya rasu.
32Sa'ad da Nuhu ya yi shekara ɗari biyar, ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.

Currently Selected:

Far 5: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy