YouVersion Logo
Search Icon

Far 46

46
Yakubu da Iyalinsa suka Tafi Masar
1Isra'ila ya kama tafiyarsa da dukan abin da yake da shi. Ya zo Biyer-sheba, ya kuwa ba da hadayu ga Allah na mahaifinsa Ishaku. 2Sai Allah ya yi magana cikin wahayin dare, ya ce, “Yakubu.”
Ya amsa ya ce, “Na'am.”
3Sai ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama a can zan maishe ka babbar al'umma. 4Ni kuwa zan gangara tare da kai zuwa Masar, ni kuma zan sāke haurowa tare da kai. Lokacin mutuwarka za ka mutu a hannun Yusufu.”
5Sai Yakubu ya tashi daga Biyer-sheba, 'ya'yan Isra'ila maza kuwa suka ɗauki mahaifinsu Yakubu, da 'yan ƙananansu da matansu a cikin kekunan shanun da Fir'auna ya aika a ɗauko su. 6#A.M 7.15 Suka kuma kora shanunsu, suka ɗauki kayayyakinsu waɗanda suka samu a ƙasar Kan'ana, suka iso Masar, Yakubu da zuriyarsa duka, 7'ya'yansa maza da jikokinsa maza tare da shi, 'ya'yansa mata, da jikokinsa mata, ya kawo zuriyarsa dukka zuwa ƙasar Masar.
8Waɗannan su ne sunayen 'ya'ya maza na Isra'ila, wato Yakubu, waɗanda suka iso Masar. Ra'ubainu, ɗan farin Yakubu. 9'Ya'yan Ra'ubainu, maza kuwa, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. 10'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan wata Bakan'aniya. 11'Ya'yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari. 12'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul. 13'Ya'yan Issaka, maza, su ne Tola, da Fuwa, da Yashub, da Shimron. 14'Ya'yan Zabaluna, maza, su ne Sered, da Elon, da Yaleyel, 15(waɗannan su ne 'ya'yan Lai'atu, maza, waɗanda ta haifa wa Yakubu cikin Fadan-aram, da 'ya tasa kuma Dinatu, 'ya'yansa mata da maza duka, mutum talatin da uku ne).
16'Ya'yan Gad, maza, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni, da Ezbon, da Eri, da Arodi, da Areli. 17'Ya'yan Ashiru, maza, su ne Yimna, da Yishuwa, da Yishwi, da Beriya, da Sera, 'yar'uwarsu. 'Ya'yan Beriya, maza kuma, su ne Eber da Malkiyel. 18Waɗannan su goma sha shida, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Zilfa, wadda Laban ya bai wa Lai'atu, 'yarsa.
19'Ya'ya maza, na Rahila, matar Yakubu, su ne Yusufu da Biliyaminu. 20#Far 41.50-52 Asenat 'yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusufu Manassa da Ifraimu a ƙasar Masar. 21'Ya'yan Biliyaminu, maza, su ne Bela, da Beker, da Ashbel, da Gera, da Na'aman, da Ahiram, da Rosh, da Muffim, da Huffim, da Adar. 22Waɗannan su goma sha huɗu su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Rahila.
23Hushim shi ne ɗan Dan. 24'Ya'yan Naftali, maza, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum. 25Waɗannan su bakwai, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Bilha, wadda Laban ya bai wa 'yarsa Rahila.
26Mutanen Yakubu dukka da suka shiga Masar, waɗanda suke zuriyarsa ne, banda matan 'ya'yansa, su mutum sittin da shida ne. 27#A.M 7.14 'Ya'yan Yusufu, maza, waɗanda aka haifa masa a Masar su biyu ne. Dukkan mutane na gidan Yakubu da suka zo Masar su saba'in.
Yakubu da Iyalinsa a Masar
28Isra'ila kuwa ya aiki Yahuza ya yi gaba zuwa wurin Yusufu ya faɗa masa ya sadu da shi a nuna masa Goshen. Da suka zo ƙasar Goshen, 29sai Yusufu ya kintsa karusarsa ya haura zuwa Goshen don ya taryi Isra'ila, mahaifinsa. Nan da nan da isowarsa wurinsa, ya rungume shi, ya jima yana ta kuka a kafaɗarsa. 30Isra'ila ya ce wa Yusufu, “To, bari in mutu yanzu, tun da na ga fuskarka na sani kuma kana da rai har yanzu.”
31Yusufu ya ce wa 'yan'uwansa da iyalin gidan mahaifinsa, “Zan tafi in faɗa wa Fir'auna, in ce masa, ‘'yan'uwana da iyalin gidan mahaifina, waɗanda dā yake a ƙasar Kan'ana, sun zo wurina, 32mutanen kuwa makiyaya ne, sun kuwa zo da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunansu na shanu, da dukkan abin da suke da shi.’ 33To, sa'ad da Fir'auna zai kira ku, ya tambaye ku, ‘Mece ce sana'arku?’ 34Sai ku ce, ‘Ranka ya daɗe, mu makiyayan shanu ne tun muna 'yan yara har zuwa yau, da mu da kakanninmu,’ don ku sami wurin zama a ƙasar Goshen, gama kowane makiyayi abin ƙyama ne ga Masarawa.”

Currently Selected:

Far 46: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy