YouVersion Logo
Search Icon

Far 40

40
Yusufu Ya Fassara Mafarkan 'Yan Kurkuku
1Bayan waɗannan al'amura, sai mai shayarwa da mai tuya na Sarkin Masar suka yi wa maigidansu Sarkin Masar laifi. 2Fir'auna ya yi fushi da ma'aikatan nan nasa biyu, wato shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya. 3Ya ba da su a sa su kurkuku, cikin gidan shugaban masu tsaron fāda, wato kurkuku inda Yusufu yake a tsare. 4Shugaban 'yan tsaron ya danƙa su ga Yusufu don ya hidimta musu, sun kuwa jima a kurkukun har an daɗe.
5Suka yi mafarki, su biyu ɗin, a dare ɗaya, da shi mai shayarwar da mai tuyar na gidan Sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, kowanne kuwa da nasa mafarkin da kuma tasa irin fassarar mafarkin. 6Da Yusufu ya zo wurinsu da safe, ya ga sun damu. 7Sai ya tambaye su ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a yamutse yau?”
8Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.”
Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”
9Saboda haka, shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusufu mafarkinsa, ya ce masa, “A mafarkina ga kurangar inabi a gabana. 10A kurangar akwai rassa uku. Sai ta yi toho, ta huda nan da nan, ta kuma yi nonna, har suka nuna suka zama inabi. 11Finjalin Fir'auna na hannuna, sai na ɗauki 'ya'yan inabi na matse su cikin finjalin Fir'auna, na sa finjalin a hannun Fir'auna.”
12Yusufu ya ce masa, “Wannan ita ce fassararsa, rassan nan uku, kwana uku ne, 13bayan kwana uku Fir'auna zai ɗaukaka ka, ya komar da kai matsayinka, za ka kuma sa finjalin Fir'auna a hannunsa kamar dā lokacin da kake mai hidimar shayarwarsa. 14Amma ka tuna da ni sa'ad da abin ya tabbata gare ka, sai ka yi mini alheri, ka ambace ni a wurin Fir'auna, har da za a fisshe ni daga wannan gida. 15Gama ni, hakika sato ni aka yi daga ƙasar Ibraniyawa. A nan kuma ban yi wani abin da zai isa a sa ni a kurkuku ba.”
16Sa'ad da shugaban masu tuya ya ga fassarar tana da kyau, sai ya ce wa Yusufu, “Ni ma cikin nawa mafarki, na ga kwanduna uku na waina a bisa kaina. 17A kwandon da yake bisa ɗin akwai toye-toye iri iri domin Fir'auna, amma ga tsuntsaye suna ta ci daga cikin kwandon da yake bisa duka, wato wanda yake bisa kaina ɗin.”
18Yusufu ya amsa, “Wannan ita ce fassararsa, kwandunan uku, kwana uku ne, 19bayan kwana uku Fir'auna zai falle kanka ya rataye ka a bisa itace, tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.”
20A rana ta uku, wadda take ranar haihuwar Fir'auna, Fir'auna ya yi wa dukan bayinsa biki, sai ya kawo shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya a gaban fādawansa. 21Ya komar da shugaban masu shayarwa a matsayinsa na shayarwa, ya kuwa miƙa finjali a hannun Fir'auna, 22amma ya rataye shugaban masu tuya kamar yadda Yusufu ya fassara musu. 23Duk da haka shugaban masu shayarwar bai tuna da Yusufu ba, amma ya manta da shi.

Currently Selected:

Far 40: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy