YouVersion Logo
Search Icon

Far 36

36
Zuriyar Isuwa
(1Tar 1.34-36)
1Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, wato Edom. 2#Far 26.34 Isuwa ya auri matansa daga cikin Kan'aniyawa, wato Ada 'yar Elon Bahitte, da Oholibama 'yar Ana ɗan Zibeyon Bahiwiye, 3#Far 28.9da Basemat, 'yar Isma'ilu, 'yar'uwar Nebayot. 4Ada ta haifa wa Isuwa, Elifaz, Basemat kuma ta haifi Reyuwel. 5Oholibama ta haifi Yewush, da Yalam, da Kora. Waɗannan su ne 'ya'yan Isuwa waɗanda aka haifa masa a ƙasar Kan'ana.
6Isuwa ya kwashi matansa, da 'ya'yansa mata da maza, da dukan jama'ar gidansa, da shanunsa, da dabbobinsa duka, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan'ana, ya kuwa tafi wata ƙasa nesa da ɗan'uwansa Yakubu. 7Gama abin mallakarsu ya yi yawa har ba zai yiwu su zama tare ba, ƙasar baƙuntarsu kuwa ba ta wadace su ba saboda yawan dabbobinsu. 8Saboda haka Isuwa ya zauna a ƙasar Seyir ta tuddai. Isuwa shi ne Edom.
9Waɗannan su ne zuriyar Isuwa, kakan Edomawa, a ƙasar Seyir ta tuddai. 10Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isuwa, maza, wato Elifaz ɗan Ada matar Isuwa, Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa. 11'Ya'yan Elifaz su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz. 12Timna kuwa ƙwarƙwarar Elifaz ɗan Isuwa ce, ta haifa wa Elifaz Amalek. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Ada, matar Isuwa.
13Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa.
14Waɗannan su ne 'ya'yan Oholibama matar Isuwa 'yar Ana ɗan Zibeyon. Ta haifi wa Isuwa Yewush, da Yalam, da Kora.
15Waɗannan su ne shugabanni na zuriyar Isuwa. Ga 'ya'yan Elifaz, maza, ɗan farin Isuwa, shugaba Teman, da Omar, da Zeho, da Kenaz, 16da Kora, da Gatam, da Amalek, su ne shugabannin Elifaz cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'yan Ada.
17Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, ɗan Isuwa. Shugaba Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza, waɗannan su ne shugabannin Reyuwel na cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa.
18Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Oholibama matar Isuwa, shugaba Yewush, da Yalam, da Kora, waɗannan su ne shugabanni waɗanda Oholibama matar Isuwa, 'yar Ana ta haifa. 19Waɗannan su ne 'ya'yan Isuwa, maza, wato Edom, da shugabanninsu.
Zuriyar Seyir
(1Tar 1.38-42)
20Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Seyir Bahore, mazaunan ƙasar Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana, 21da Dishon, da Ezer, da Dishan. Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, 'ya'yan Seyir, maza, a ƙasar Edom. 22'Ya'yan Lotan, maza, su ne Hori da Hemam, 'yar'uwarsa Timna ce. 23Waɗannan su ne 'ya'yan Shobal, maza, Alwan, da Manahat, da Ebal, da Sheho, da Onam. 24Waɗannan su ne 'ya'yan Zibeyon, maza, Aiya da Ana. Shi ne Ana wanda ya sami maɓuɓɓugan ruwan zafi a cikin jeji, a sa'ad da yake kiwon jakunan mahaifinsa Zibeyon. 25Waɗannan su ne 'ya'yan Ana, Dishon da Oholibama 'yar Ana. 26Waɗannan su ne 'ya'yan Dishon, maza, Hemdan da Eshban, da Yitran, da Keran. 27Waɗannan su ne 'ya'yan Ezer, maza, Bilhan, da Zayawan, da Akan. 28Waɗannan su ne 'ya'yan Dishan, maza, Uz da Aran. 29Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, shugaba Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana, 30da Dishon, da Ezer, da Dishan, waɗannan su ne shugabannin Horiyawa bisa ga shugabancinsu a ƙasar Seyir.
Sarakunan Edom
(1Tar 1.43-54)
31Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a ƙasar Edom, kafin wani sarki ya taɓa yin mulkin Isra'ilawa. 32Bela ɗan Beyor ya yi sarautar Edom, sunan birninsa kuwa Dinhaba. 33Bela ya rasu, sai Yobab ɗan Zera daga Bozara ya ci sarauta a bayansa. 34Ɗan Yobab ya rasu, sai Husham na ƙasar Temanawa ya ci sarauta a bayansa. 35Da Husham ya rasu, sai Hadad ɗan Bedad wanda ya ci Madayana a ƙasar Mowab, ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa kuwa Awit ne. 36Da Hadad ya rasu, sai Samla na Masreka ya ci sarauta a bayansa. 37Da Samla ya rasu, sai Shawul na Rehobot ta Yufiretis ya ci sarauta a bayansa. 38Da Shawul ya rasu, sai Ba'al-hanan ɗan Akbor ya ci sarauta a bayansa. 39Da Ba'al-hanan ɗan Akbor ya rasu, sai Hadad ya ci sarauta a bayansa, sunan birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel 'yar Matred, 'yar Mezahab.
40Waɗannan su ne sunayen sarakunan Isuwa bisa ga dangoginsu da bisa ga wurin zamansu. Ga sunayensu, sarki Timna, da Alwa, da Yetet, 41da Oholibama, da Ila, da Finon, 42da Kenaz, da Teman, da Mibzar, 43da Magdiyel, da Iram. Waɗannan su ne sarakunan Edom, (wato Isuwa ne kakan Edomawa) bisa ga wuraren zamansu a ƙasar mallakarsu.

Currently Selected:

Far 36: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy