YouVersion Logo
Search Icon

Far 33

33
Yakubu ya Sadu da Isuwa
1Yakubu ya ɗaga ido ya duba ke nan, sai ga Isuwa na zuwa da mutum arbaminya tare da shi. Sai ya raba wa Lai'atu da Rahila 'ya'yan, tare da kuyangin nan biyu. 2Ya sa kuyangin da 'ya'yansu a gaba, sa'an nan Lai'atu sa'an nan Rahila da Yusufu a ƙarshen duka. 3Shi kansa ya wuce gabansu, ya yi ta sunkuyar da kansa ƙasa sau bakwai, har sa'ad da ya kai kusa da ɗan'uwansa. 4Amma Isuwa ya sheƙa ya tarye shi, ya rungume shi, ya faɗa a wuyansa, ya sumbace shi, suka kuwa yi kuka. 5Sa'ad da Isuwa ya ta da idonsa ya ga mata da 'ya'ya, ya ce, “Su wane ne waɗannan tare da kai?”
Yakubu ya ce, “Su ne 'ya'ya waɗanda Allah cikin alherinsa ya ba baranka.” 6Sai kuyangin suka matso kusa, su da 'ya'yansu, suka sunkuya ƙasa. 7Haka nan kuma Lai'atu da 'ya'yanta suka matso, suka sunkuya ƙasa, a ƙarewa Yusufu da Rahila suka matso kusa, su kuma suka sunkuya ƙasa.
8Isuwa kuwa ya ce, “Ina manufarka da duk waɗannan ƙungiyoyi da na gamu da su?”
Yakubu ya amsa, ya ce, “Ina neman tagomashi ne a idon shugabana.”
9Amma Isuwa ya ce, “Ina da abin da ya ishe ni, ɗan'uwana, riƙe abin da kake da shi don kanka.”
10Yakubu ya ce, “A'a, ina roƙonka, in dai na sami tagomashi a idonka, to, sai ka karɓi kyautar da yake hannuna, gama hakika ganin fuskarka, kamar ganin fuskar Allah ne, bisa ga yadda ka karɓe ni. 11Ina roƙonka, ka karɓi kyautar da na kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri matuƙa, gama ina da abin da ya ishe ni.” Da haka Yakubu ya i masa, Isuwa kuwa ya karɓa.
12Sa'an nan Isuwa ya ce, “Bari mu ci gaba da tafiyarmu, ni kuwa in wuce gabanka.”
13Amma Yakubu ya ce masa, “Shugabana, ai, ka sani 'ya'yan ba su da ƙarfi, ga kuma bisashe da shanun tatsa, ina jin tausayinsu ƙwarai da gaske. Idan kuwa aka tsananta korarsu kwana ɗaya, garkunan za su mutu duka. 14Bari shugabana ya wuce gaban baransa, ni zan biyo a hankali bisa ga saurin shanun da yake gabana, da kuma bisa ga saurin yaran, har in isa wurin shugaba a Seyir.”
15Sai Isuwa ya ce, “Bari in bar waɗansu daga cikin mutanen da suke tare da ni, a wurinka.”
Amma Yakubu ya ce, “Ka kyauta ƙwarai, amma ba na bukatar haka, ya shugaba.” 16A ran nan Isuwa ya koma a kan hanyarsa zuwa Seyir. 17Yakubu ya kama hanya zuwa Sukkot, ya kuwa gina wa kansa gida, ya yi wa shanunsa garke. Saboda haka aka sa wa wurin suna Sukkot.
18Yakubu kuwa ya kai birnin Shalem wanda yake ƙasar Kan'ana lafiya, a kan hanyarsa daga Fadan-aram, ya kuwa yi zango a ƙofar birnin. 19#Josh 24.32; Yah 4.5 Ya kuma sayi yankin saura inda ya kafa alfarwarsa daga 'ya'yan Hamor, mahaifin Shekem, a bakin azurfa ɗari. 20A wurin ya gina bagade ya sa masa suna El-Elohe-Isra-el.

Currently Selected:

Far 33: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy