YouVersion Logo
Search Icon

Far 31

31
Yakubu ya Gudu daga wurin Laban
1Yakubu ya ji 'ya'yan Laban suna cewa, “Yakubu ya kwashe dukan abin da yake na mahaifinmu, daga cikin dukan abin da yake na mahaifinmu kuma ya sami dukiyarsa.” 2Yakubu kuma ya ga ba shi da farin jini a wurin Laban kamar dā. 3Ubangiji ya ce wa Yakubu, “Ka koma ƙasar kakanninka da danginka, ni kuwa ina tare da kai.”
4Saboda haka Yakubu ya aika a kirawo Rahila da Lai'atu zuwa cikin saura inda garkensa yake, 5ya ce musu, “Na ga ba ni da sauran farin jini wurin mahaifinku kamar dā. Amma Allah na mahaifina yana tare da ni. 6Kun sani na yi wa mahaifinku barantaka da dukan ƙarfina, 7duk da haka mahaifinku ya cuce ni, ya yi ta sassauya ladana har sau goma, amma Allah bai ba shi ikon zambatata ba. 8In ya ce, ‘Dabbare-dabbare, su ne ladanka,’ duk garken sai ya haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce ‘masu sofane ne ladanka,’ sai garken duka ya haifi masu sofane. 9Ta haka Allah ya kwashe dukiyar mahaifinku ya ba ni.
10“A lokacin ɗaukar cikin garke, cikin mafarki na ta da idanuna, na kuwa gani cikin mafarkin, bunsuran da suke hawan garken, masu sofane, da dabbare-dabbare da roɗi-roɗi ne. 11Sai mala'ikan Allah ya ce mini a cikin mafarki, ‘Yakubu,’ sai na ce, ‘Ga ni.’ 12Ya kuwa ce, ‘Ta da idanunka ka gani, dukan bunsuran da suke hawan awaki masu sofane ne, dabbare-dabbare da roɗi-roɗi, gama na ga dukan abin da Laban yake yi maka. 13#Far 28.18-22 Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa dutsen mai, ka kafa shi al'amudi, ka kuma rantse mini. Yanzu fa tashi ka fita daga cikin ƙasan nan, ka koma ƙasar haihuwarka.’ ”
14Rahila da Lai'atu suka amsa masa, “Akwai wani rabo, ko gādon da ya rage mana a cikin gidan mahaifinmu? 15Ba ga shi ma, sai kamar baƙi yake ɗaukarmu ba? Gama ya sayar da mu, yana kuwa morar kuɗin da aka bayar dominmu. 16Dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga wurin mahaifinmu, tamu ce da 'ya'yanmu, yanzu fa, kome Allah ya faɗa maka, sai ka yi.”
17Sai Yakubu ya tashi, ya ɗauki 'ya'yansa, da matansa a bisa raƙumansa, 18ya kora shanunsa duka, da dukan bisashen da ya samu, da shanu da suke nasa, waɗanda ya samu a Fadan-aram a ƙasar Mesofotamiya, zuwa ƙasar Kan'ana wurin mahaifinsa Ishaku. 19Amma a sa'an nan Laban ya riga ya tafi ya yi wa tumakinsa sausaya, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta. 20Yakubu kuwa ya yaudari Laban Ba'aramiye da bai sanar da shi zai gudu ba. 21Ya gudu da dukan abin da yake da shi, ya tashi ya haye Yufiretis, ya miƙe zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai.
Laban ya Bi Sawun Yakubu
22Sa'ad da aka sanar da Laban, cewa Yakubu ya gudu da kwana uku, 23sai ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi sawunsa har kwana bakwai, yana biye da shi kurkusa har zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai. 24Amma Allah ya zo wurin Laban Ba'aramiye cikin mafarki da dad dare, ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.” 25Sai Laban ya ci wa Yakubu. A yanzu Yakubu ya riga ya kafa alfarwarsa a ƙasa ta tuddai, Laban da danginsa kuma suka yi zango a ƙasar Gileyad ta tuddai.
26Laban ya ce wa Yakubu, “Me ka yi ke nan, da ka cuce ni, ka gudu da 'ya'yan matana kamar kwason yaƙi? 27Me ya sa ka gudu a ɓoye? Ka cuce ni, ba ka kuwa faɗa mini ba, ai, da na sallame ka da farin ciki, da waƙe-waƙe, da kiɗa, da garaya. 28Don me ba ka bari na sumbaci 'ya'yana mata da maza na yi bankwana da su ba? Kai! Ka yi aikin wauta. 29Ina da iko in yi maka lahani, amma Allah na mahaifinka, ya yi magana da ni a daren jiya, yana cewa, ‘Ka kula fa kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.’ 30Amma yanzu, ka gudu domin kana kewar gidan mahaifinka ƙwarai, amma don me ka sace mini gumakana?”
31Yakubu ya amsa wa Laban, ya ce, “Domin na ji tsoro ne gama na yi zaton za ka ƙwace 'ya'yanka mata ƙarfi da yaji. 32Ga duk wanda ka iske gumaka a wurinsa, a kashe shi. Yanzu a nan gaban danginmu, ka nuna abin da nake da shi wanda yake naka, ka ɗauka.” Ashe, Yakubu bai sani Rahila ce ta sace su ba.
33Laban ya shiga alfarwar Yakubu, da ta Lai'atu, da na kuyangin nan biyu, amma bai same su ba. Sai ya fita daga alfarwar Lai'atu, ya shiga ta Rahila. 34Ashe, Rahila ta kwashe gumakan ta zuba su cikin sirdin raƙumi, ta zauna a kansu. Laban ya wawaka alfarwar duka, amma bai same su ba. 35Sai ta ce wa mahaifinta, “Kada ubangijina ya yi fushi da ban iya tashi ba, don ina al'adar mata ne.” Ya kuwa bincike, amma bai sami gumakan ba.
36Yakubu ya husata, ya yi wa Laban faɗa, ya ce wa Laban, “Wane laifi na yi, mene ne zunubina da ka tsananta bina? 37Ko da yake ka wawaka dukan kayayyakina, me ka samu na gumakanka a ciki? A tabbatar a nan yau a gaban dangina da danginka, su yanke shari'a tsakanina da kai. 38Waɗannan shekaru ashirin da na yi tare da kai, tumakinka da awakinka ba su yi ɓari ba, ban kuwa ci ragunan garkenka ba. 39Wanda namomin jeji suka yayyaga ban kawo maka ba, ni da kaina na ɗauki hasararsu. Ka kuma nemi abin da aka sace da rana ko da dare daga hannuna. 40Abin da na zama ke nan, da rana na sha zafin rana, da dare kuwa na sha sanyi, ga rashin barci. 41A waɗannan shekaru ashirin da nake cikin gidanka, na yi maka barantaka shekara goma sha huɗu domin 'ya'yanka mata biyu, shekara shida kuma domin garkenka, ka kuwa sauya ladana har sau goma. 42Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”
Yarjejeniya Tsakanin Yakubu da Laban
43Sa'an nan Laban ya amsa ya ce wa Yakubu, “'Ya'ya mata, 'ya'yana ne, 'ya'yansu kuma nawa ne, garkunan, garkunana ne, dukan abin da kake gani nawa ne. Amma me zan yi a wannan rana ta yau ga waɗannan 'ya'ya mata nawa, ko kuma ga 'ya'yan da suka haifa? 44Zo mana mu ƙulla alkawari, da ni da kai, bari ya zama shaida tsakanina da kai.”
45Saboda haka Yakubu ya ɗauki dutse ya kafa shi al'amudi. 46Yakubu ya ce wa iyalinsa, “Ku tattara duwatsu.” Sai suka ɗauki duwatsu, suka tsiba, suka kuwa ci abinci kusa da tsibin. 47Laban ya sa masa suna Yegar-sahaduta, amma Yakubu ya kira shi Galeyed.
48Laban ya ce, “Wannan tsibi shaida ce tsakanina da kai yau.” Saboda haka ya sa wa wurin suna Galeyed. 49Laban kuma ya kira wurin Mizfa, gama ya ce, “Ubangiji ya kiyaye tsakanina da kai sa'ad da muka rabu da juna. 50Idan ka wulakanta 'ya'yana mata, ko kuma ka auri wata mata banda 'ya'yana mata, ko da yake babu kowa tare da mu, ka tuna, Allah shi ne mashaidi tsakanina da kai.” 51Sai Laban ya ce wa Yakubu, “Dubi wannan tsibi da al'amudi, wanda na kafa tsakanina da kai. 52Wannan tsibi, shaida ce, al'amudin kuma shaida ce ba zan zarce wannan tsibi zuwa wurinka ba, kai kuma ba za ka zarce wannan tsibi da wannan al'amudi zuwa wurina don cutarwa ba. 53Allah na Ibrahim da Nahor, Allah na mahaifinsu, ya shara'anta tsakaninmu.” Saboda haka Yakubu ya rantse da martabar mahaifinsa Ishaku. 54Yakubu kuwa ya miƙa hadaya a bisa dutsen, ya kirawo iyalinsa su ci abinci, suka kuwa ci abinci suka zauna dukan dare a bisa dutsen. 55Da sassafe, Laban ya tashi ya sumbaci jikokinsa, da 'ya'yansa mata, ya sa musu albarka. Sa'an nan ya tashi ya koma gida.

Currently Selected:

Far 31: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy