YouVersion Logo
Search Icon

Far 25

25
Sauran Zuriyar Ibrahim
(1Tar 1.32-33)
1Ibrahim ya auro wata mace kuma, sunanta Ketura. 2Ta haifa masa Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa. 3Yokshan ya haifi Sheba da Dedan. 'Ya'yan Dedan su ne Asshurim, da Letushim, da Le'umomim. 4'Ya'yan Madayana su ne Efa, da Efer, da Hanok, da Abida, da Eldaya. Waɗannan duka 'ya'yan Ketura ne.
5Ibrahim ya ba Ishaku dukan abin da yake da shi. 6Amma ga 'ya'yan ƙwaraƙwarai Ibrahim ya ba da kyautai, ya sallame su tun yana da rai, su tafi nesa da Ishaku zuwa can cikin ƙasar gabas.
Rasuwar Ibrahim da Jana'izarsa
7Waɗannan su ne kwanakin shekarun Ibrahim a duniya, shekara ɗari da saba'in da biyar. 8Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama'arsa, waɗanda suka riga shi. 9Ishaku da Isma'ilu 'ya'yansa suka binne shi a kogon Makfela a saurar Efron ɗan Zohar Bahitte, gabashin Mamre, 10#Far 23.3-16 wato saurar da Ibrahim ya saya a wurin Hittiyawa. Can ne aka binne Ibrahim gab da Saratu matarsa. 11Bayan rasuwa Ibrahim, Allah ya sa wa Ishaku ɗansa albarka. Ishaku kuwa ya zauna a Biyer-lahai-royi.
Zuriyar Isma'ilu
(1Tar 1.28-31)
12Waɗannan su ne zuriyar Isma'ilu ɗan Ibrahim, wanda Hajaratu Bamasariya, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim. 13Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isma'ilu, maza, bisa ga haihuwarsu. Nebayot ɗan farin Isma'ilu, da Kedar, da Adbeyel, da Mibsam, 14da Mishma, da Duma, da Massa, 15da Hadad, da Tema, da Yetur, da Nafish, da Kedema. 16Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isma'ilu, bisa ga ƙauyukansu da zangonsu, hakimai goma sha biyu, bisa ga kabilansu. 17Waɗannan su ne shekarun Isma'ilu a duniya, shekara ɗari da talatin da bakwai, ya ja numfashinsa na ƙarshe ya rasu, aka kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi. 18Mazauninsa a tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake ɗaura da Masar wajen Assuriya. Suka ware daga danginsu suka yi zamansu.
Haihuwar Isuwa da Yakubu
19Waɗannan su ne zuriyar Ishaku ɗan Ibrahim, Ibrahim ya haifi Ishaku. 20Ishaku yana da shekara arba'in sa'ad da ya auri Rifkatu, 'yar Betuwel Ba'aramiye daga Fadan-aram 'yar'uwar Laban Ba'aramiye. 21Ishaku kuwa ya yi addu'a sai matarsa Rifkatu ta yi ciki. 22'Ya'yan kuwa suka kama kokawa da juna a cikinta, har ta ce, “In haka ne don me zan rayu?” Sai ta je ta tambayi Ubangiji.
23 # Rom 9.12 Sai Ubangiji ya ce mata, “Al'umma biyu suke a cikin mahaifarki, mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban zai bauta wa ƙaramin.”
24Sa'ad da kwanakin haihuwarta suka cika, sai ga shi, ashe, tagwaye ne suke a cikin mahaifarta. 25Na farin ya fito ja wur kamar riga mai gashi, saboda haka suka raɗa masa suna Isuwa. 26Daga baya kuma ɗan'uwansa ya fito, hannunsa na riƙe da diddigen Isuwa, saboda haka aka raɗa masa suna Yakubu. Ishaku yana da shekara sittin sa'ad da ya haife su.
Isuwa ya Sayar da Matsayinsa na Ɗan Fari
27Sa'ad da yaran suka yi girma, Isuwa ya zama ƙwararren maharbi, ya zama mutumin jeji, Yakubu kuwa kintsattse ne mai son zaman gida. 28Ishaku ya ƙaunaci Isuwa saboda yakan ci naman da ya farauto, amma Rifkatu ta ƙaunaci Yakubu.
29Wata rana, sa'ad da Yakubu yake dafa fate, Isuwa ya komo daga jeji, yana jin yunwa ƙwarai. 30Sai Isuwa ya ce wa Yakubu, “Ka ɗibar mini jan fatenka in sha, gama ina fama da yunwa!” Saboda haka aka kira sunansa Edom.
31Yakubu ya ce, “Sai dai ko in yau za ka sayar mini da matsayinka na ɗan fari.”
32Sai Isuwa ya ce, “Ni da nake bakin mutuwa, wane amfani matsayina na ɗan fari zai yi mini?”
33 # Ibr 12.16 Yakubu ya ce, “Yau sai ka rantse mini.” Sai ya rantse masa ya kuwa sayar wa Yakubu da matsayinsa na ɗan fari. 34Sa'an nan Yakubu ya ba Isuwa gurasa da faten wake, ya ci ya sha, ya tashi ya yi tafiyarsa. Ta haka Isuwa ya banzatar da matsayinsa na ɗan fari.

Currently Selected:

Far 25: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy