YouVersion Logo
Search Icon

Far 23

23
Ibrahim Ya Sayi Makabarta a Rasuwar Saratu
1Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya, 2sa an nan ta rasu a Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar Kan'ana. Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makoki, yana baƙin ciki domin Saratu.
3Ibrahim ya bar gawar matarsa, ya je ya ce wa Hittiyawa, 4#Ibr 11.9,13; A.M 7.16 “Ni baƙo ne, ina tsakaninku, ina zaman baƙunci. Ku sayar mini da wurin yin makabarta, domin in binne matata, in daina ganinta!”
5Hittiyawa suka amsa wa Ibrahim suka ce, 6“Ka ji mu, ya shugaba, gama kai yardajjen Allah ne a tsakaninmu. Ka binne matarka a kabari mafi kyau na kaburburanmu, ba waninmu da zai hana maka kabarinsa, ko ya hana ka ka binne matarka.”
7Ibrahim ya tashi ya sunkuya wa Hittiyawa, mutanen ƙasar. 8Sai ya ce musu, “Idan kun yarda in binne matata in daina ganinta, to, ku ji ni, ku roƙar mini Efron Bahitte ɗan Zohar, 9ya ba ni kogon Makfela nasa na can ƙarshen saurarsa. Bari ya sallama mini wurin a gabanku a cikakken kuɗinsa, ya zama mallakata domin makabarta.”
10A sa'an nan Efron yana tare da Hittiyawa. Sai Efron Bahitte ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan Hittiyawa, da gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsa, ya ce, 11“Ba haka ba ne, ya shugaba, ka ji ni. Na ba ka saurar, da kogon da yake cikinta. A gaban jama'ata na ba ka ita, ka binne matarka.”
12Ibrahim kuwa ya sunkuya a gaban jama'ar ƙasar. 13Ya ce wa Efron, a kunnuwan jama'ar ƙasar, “In dai ka yarda, ka ji ni. Zan ba da kuɗin saurar. Ka karɓa daga gare ni don in binne matata a can.”
14Efron ya amsa wa Ibrahim, 15“Ya shugabana, ka ji ni, don ɗan yankin ƙasa na shekel ɗari huɗu, a bakin me yake, a tsakaninmu? Binne matarka.” 16Ibrahim ya yarda da Efron. Ibrahim kuwa ya auna wa Efron yawan shekel da ya ambata a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu bisa ga nauyin da 'yan kasuwa suke amfani da shi a wancan lokaci.
17Don haka saurar Efron da yake cikin Makfela wadda take gabashin Mamre, da saurar, da kogon da yake ciki, da dukan itatuwan da suke cikin saurar, iyakar girmanta duka 18an tabbatar wa Ibrahim, cewa mallakarsa ce a gaban Hittiyawa, a gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsu. 19Bayan wannan, Ibrahim ya binne Saratu matarsa a kogon da yake a saurar Makfela a gabashin Mamre, wato Hebron, cikin ƙasar Kan'ana. 20Da saurar, da kogon da yake cikinta, aka tabbatar wa Ibrahim mallakarsa ce don makabarta da iznin Hittiyawa.

Currently Selected:

Far 23: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy