YouVersion Logo
Search Icon

Far 11

11
Hasumiyar Babila
1A lokacin, harshen mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce. 2Sa'ad da mutane suke ta yin ƙaura daga gabas, sai suka sami fili a ƙasar Shinar, suka zauna a can. 3Sai suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi aiki da tubali maimakon dutse, katsi kuma maimakon lāka. 4Sai suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni, da hasumiya wadda ƙwanƙolinta zai kai can cikin sammai domin mu yi wa kanmu suna, domin kada mu warwatsu ko'ina bisa duniya.”
5Ubangiji kuwa ya sauko ya ga birnin da hasumiyar da 'yan adam suka gina. 6Ubangiji kuwa ya ce, “Ga su, su jama'a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne, to fa, ga irin abin da suka fara yi, ba abin da za su shawarta su yi da zai gagare su. 7Zo mu sauka, mu dagula harshensu, domin kada su fahimci maganar juna.” 8Haka kuwa daga wurin Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya, sai suka daina gina birnin. 9Domin haka aka kira sunan wurin Babila, domin a nan ne Ubangiji ya dagula harshen dukan duniya, daga nan ne kuma Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya.
Zuriyar Shem
(1Tar 1.24-27)
10Waɗannan su ne zuriyar Shem. Lokacin da Shem yake da shekara ɗari, ya haifi Arfakshad bayan Ruwan Tsufana da shekara biyu. 11Shem kuwa ya yi shekara ɗari biyar bayan haihuwar Arfakshad, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
12Sa'ad da Arfakshad yake da shekara talatin da biyar ya haifi Shela. 13Arfakshad kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Shela, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
14Sa'ad da Shela yake da shekara talatin, ya haifi Eber, 15Shela kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Eber, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
16Sa'ad da Eber ya yi shekara talatin da huɗu ya haifi Feleg, 17Eber kuwa ya yi shekara arbaminya da talatin, bayan haihuwar Feleg, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
18Sa'ad da Feleg ya yi shekara talatin ya haifi Reyu. 19Feleg ya yi shekara metan da tara bayan haihuwar Reyu, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
20Sa'ad da Reyu ya yi shekara talatin da biyu ya haifi Serug. 21Reyu kuwa ya yi shekara metan da bakwai bayan haihuwar Serug, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
22Sa'ad da Serug ya yi shekara talatin ya haifi Nahor, 23Serug kuwa ya yi shekara metan bayan haihuwar Nahor, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
24Sa'ad da Nahor ya yi shekara ashirin da tara, ya haifi Tera, 25Nahor kuwa ya yi shekara ɗari da goma sha tara bayan haihuwar Tera, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
26Sa'ad da Tera ya yi shekara saba'in, ya haifi Abram, da Nahor, da Haran.
27Yanzu dai waɗannan su ne zuriyar Tera, Tera ya haifi Abram, da Nahor, da Haran, Haran kuwa shi ne ya haifi Lutu.
28Haran kuwa ya rasu a idon mahaifinsa Tera a ƙasar haihuwarsa, a Ur ta Kaldiyawa. 29Da Abram da Nahor suka yi aure, sunan matar Abram Saraya, sunan matar Nahor kuwa Milka, ita 'yar Haran ce, mahaifin Milka da Iskaya. 30Saraya kuwa ba ta haihuwa, wato ba ta da ɗa.
31Sai Tera ya ɗauki ɗansa Abram da Lutu ɗan Haran, jikansa, da Saraya surukarsa, wato matar ɗansa Abram, suka tafi tare, daga Ur ta Kalidiyawa zuwa ƙasar Kan'ana, amma da suka isa Haran, suka zauna a can. 32Kwanakin Tera shekara ce metan da biyar, Tera kuwa ya rasu a Haran.

Currently Selected:

Far 11: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy