YouVersion Logo
Search Icon

Ezra 10

10
An Shirya yadda Za a Rabu da Aurayya da Arna
1Sa'ad da Ezra yake yin addu'a, yana hurta laifi, yana kuka, yana a durƙushe gaban Haikalin Allah, sai babban taron jama'a, mata, da maza, da yara daga Isra'ila suka taru wurinsa. Mutane suka yi kuka mai zafi. 2Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam, ya yi wa Ezra magana, ya ce, “Mun yi wa Allahnmu rashin aminci, gama mun auri mata baƙi daga mutanen ƙasar, amma duk da haka akwai sauran bege ga Isra'ila. 3Bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori dukan waɗannan mata da 'ya'yansu, bisa ga shawarar shugabanni da waɗanda suke rawar jiki saboda umarnin Allah. Bari mu yi alkawari bisa ga doka. 4Sai ka tashi, gama wannan hakkinka ne, mu kuwa muna tare da kai. Sai dai ka yi ƙarfin hali, ka yi shi.”
5Ezra kuwa ya tashi, ya sa firistoci da suke shugabanni, da Lawiyawa, da dukan mutanen Isra'ila su rantse, cewa za su yi abin da aka ce. Sai suka yi rantsuwar. 6Sa'an nan Ezra ya tashi daga Haikalin Allah, ya tafi gidan Yohenan ɗan Eliyashib, amma ko da ya tafi can bai ci abinci ba, bai kuma sha ruwa ba, gama yana baƙin ciki saboda rashin aminci na waɗanda suka dawo daga zaman talala.
7Sai aka yi shela a dukan Yahuza da Urushalima, cewa dukan waɗanda suka komo daga zaman talala, su hallara a Urushalima. 8Duk wanda bai zo a cikin kwana uku ba, za a washe shi, a kuma ware shi daga jama'ar da suka dawo daga zaman talala. Haka shugabanni da dattawa suka umarta. 9Sai dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, suka hallara a Urushalima kafin kwana uku, a ran ashirin ga watan tara. Mutanen suka zauna a dandalin Haikali, suna rawar jiki saboda al'amarin, da kuma saboda babban ruwan sama.
10Ezra firist kuwa ya miƙe tsaye ya ce wa jama'a, “Kun yi rashin aminci, kun auri mata baƙi, ta haka kuka ƙara zunubin Isra'ila. 11Yanzu sai ku hurta wa Ubangiji Allah na kakanninku, laifinku, ku kuma aikata nufinsa. Ku ware kanku daga mutanen ƙasar da mata baƙi.”
12Dukan taron jama'a suka amsa da babbar murya, suka ce, “Haka nan ne, haka nan ne, dole ne mu yi yadda ka faɗa. 13Amma mutane suna da yawa, a lokacin kuwa ana marka, ba za mu iya tsayawa a fili ba, aikin nan kuma ba na kwana ɗaya, ko biyu ba ne, gama mun yi laifi sosai wajen wannan al'amari. 14Bari shugabanninmu su wakilci dukan taron jama'a, bari kuma dukan waɗanda suke garuruwanmu da suka auri mata baƙi su zo a ƙayyadadden lokaci tare da dattawa da alƙalan garuruwansu, har lokacin da Allah ya huce daga fushinsa a kanmu saboda al'amarin nan.” 15Jonatan ɗan Asahel da Yazeya ɗan Tikwa ne kaɗai ba su yarda da wannan ba, Meshullam da Shabbetai suka goyi bayansu.
16Waɗanda suka komo daga zaman talala kuwa suka yi haka. Sai Ezra firist ya zaɓi mutanen da suke shugabannin gidajen kakanninsu. Aka rubuta sunan kowa. Sai suka taru ran ɗaya ga watan goma, don su bincika al'amarin. 17Suka gama binciken dukan mutanen da suka auri mata baƙi ran ɗaya ga watan fari.
Mazajen da Suke da Mata Baƙi
18Ma'aseya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya iyalin Yeshuwa ɗan Yehozadak, su ne firistocin da suka auri mata baƙi. 19Sai suka yi alkawari, cewa za su saki matansu. Suka ba da rago don yin hadaya saboda laifinsu.
20-24Na iyalin Immer, Hanani, da Zabadiya
Na iyalin Harim, Ma'aseya, da Iliya, da Shemaiya, da Yehiyel, da Uzziya
Na iyalin Fashur, Eliyehoyenai, da Ma'aseya, da Isma'ilu, da Netanel, da Yozabad, da Elasa
Na Lawiyawa, Yozabad, da Shimai, da Kelaya, wato Kelita, da Fetahiya, da Yahuza, da Eliyezer
Na mawaƙa, Eliyashib
Na masu tsaron ƙofa, Shallum, da Telem, da Uri.
25-33Akwai kuma waɗansu na Isra'ila.
Na iyalin Farosh, Ramiya, da Izziya, da Malkiya, da Miyamin, da Ele'azara, da Malkiya, da Benaiya
Na iyalin Elam, Mattaniya, da Zakariya, da Yehiyel, da Abdi, da Yeremot, da Iliya
Na iyalin Zattu, Eliyehoyenai, da Eliyashib, da Mattaniya, da Yeremot, da Zabad, da Aziza
Na iyalin Bebai, Yehohanan, da Hananiya, da Zabbai, da Atlai
Na iyalin Bani, Meshullam, da Malluki, da Adaya, da Yashub, da Sheyal, da Yeremot
Na iyalin Fahat-mowab, Adana, da Kelal, da Benaiya, da Ma'aseya, da Mattaniya, da Bezalel, da Binnuyi, da Manassa
Na iyalin Harim, Eliyezer, da Isshiya, da Malkiya, da Shemaiya, da Shimeyon, da Biliyaminu, da Malluki, da Shemariya
Na iyalin Hashum, Mattenai, da Mattatta, da Zabad, da Elifelet, da Yeremai, da Manassa, da Shimai
34-37Na iyalin Bani, Mayadi, da Amram, da Yuwel, da Benaiya, da Bedeya, da Keluhi, da Waniya, da Meremot, da Eliyashib, da Mattaniya, da Mattenai, da Yawasu
38-42Na iyalin Binnuyi, Shimai, da Shelemiya, da Natan, da Adaya, da Maknadebai, da Shashai, Sharai, da Azarel, da Shelemiya, da Shemariya, da Shallum, da Amariya, da Yusufu
43Na iyalin Nebo, Yehiyel, da Mattitiya, da Zabad, da Zebina, da Yaddai, da Yowel, da Benaiya.
44Waɗannan duk sun auro mata baƙi. Sai suka sake su da 'ya'yansu.

Currently Selected:

Ezra 10: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in