Eze 42
42
1Sa'an nan ya kai ni a farfajiya da yake waje, ya kuma kai ni ɗakunan da yake kusa da farfajiyar Haikali, daura da ginin da yake wajen arewa. 2Tsawon ginin da yake wajen gefen arewa kamu ɗari ne, faɗinsa kuma kamu hamsin. 3A gaban kamu ashirin na farfajiyar da yake can ciki, da kuma a gaban daɓen farfajiyar da take waje, akwai jerin ɗakuna hawa uku uku. 4A gaban ɗakunan akwai hanya mai faɗin kamu goma, tsawonta kuwa kamu ɗari. Ƙofofinsu suna fuskantar arewa. 5Ɗakunan da suke a hawa na uku ba su da fāɗi, gama hanyar benen ya cinye wuri fiye da ɗakunan da suke a hawa na ƙasa da na tsakiya. 6Ɗakunan suna da hawa uku, amma ba su da ginshiƙai kamar na farfajiyar da suke waje. Saboda haka ɗakunan da suke a hawa na uku ba su kai girman waɗanda suke a hawa na ƙasa da na tsakiya ba. 7Tsawon katangar waje wadda take gefen ɗakunan farfajiyar waje wanda yake daura da ɗakunan kamu hamsin ne. 8Tsawon ɗakunan da suke fuskantar farfajiyar waje kamu hamsin ne. Waɗanda suke fuskantar Haikalin kuwa tsawonsu kamu ɗari ne. 9Ƙasa da ɗakunan nan akwai ƙofa a gefen gabas, in za a shiga cikinsu daga farfajiyar waje. 10Akwai kuma ɗakuna a faɗin katangar farfajiyar a wajen gabas a gaban wata farfajiyar da gaban wani gini. 11Akwai hanya a gaban ɗakunan, sun kuma yi kama da ɗakunan da suke wajen arewa. Tsawonsu, da faɗinsu, da yadda aka shirya su, da ƙofofinsu duk iri ɗaya ne. 12Kamar ƙofofin ɗakunan da suke wajen kudu, haka nan kuma akwai ƙofa a hanyar da take gaban katanga a wajen gabas, in za a shiga.
13Sa'an nan ya ce mini, “Ɗakunan da suke wajen kudu da na wajen arewa gaban farfajiya, su ne tsarkakan ɗakuna inda firistoci waɗanda suke kusatar Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A nan kuma za su ajiye hadayu mafi tsarki, wato hadaya ta gari, da hadaya domin zunubi, da hadaya domin laifi, gama wurin tsattsarka ne. 14Sa'ad da firistoci suka shiga Wuri Mai Tsarki, ba za su fita daga cikinsa zuwa farfajiyar da yake waje ba, sai sun tuɓe rigunan aikinsu, gama rigunan tsarkakakku ne. Za su sa waɗansu riguna kafin su tafi inda mutane suke.”
15Sa'ad da ya gama auna cikin Haikalin, ya fito da ni ta ƙofar gabas, sa'an nan ya auna filin da yake kewaye da Haikalin. 16Ya auna kusurwar gabas da karan awo, kamu ɗari biyar. 17Sai kuma ya auna kusurwar arewa, kamu ɗari biyar. 18Kusurwar kudu kamu ɗari biyar. 19Kusurwar yamma, ita ma kamu ɗari biyar. 20Ya auna dukan kusurwoyi huɗu. Filin yana kewaye da katanga mai tsawo kamu ɗari biyar ne, fāɗi kuma kamu ɗari biyar don ya raba Wuri Mai Tsarki da sauran wurin.
Currently Selected:
Eze 42: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979