Eze 30
30
Lalacewar Masar
1Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce Ubangiji Allah ya ce maka ka yi kuka, kana cewa,
“ ‘Kaito, kaito saboda wannan rana!’
3Gama ranar ta gabato,
Ranar Ubangiji ta yi kusa,
Rana ce ta gizagizai,
Ranar halakar al'ummai.
4Takobi zai fāɗa a kan Masar,
Azaba kuma za ta sami Habasha.
Za a kashe mutane a Masar,
Za a kwashe dukiyarta,
A rushe harsashin gininta.
5“Yaƙi zai ci Habasha, da Fut, da Lud, da dukan Arabiya, da Libya, da mutanen ƙasar da suka haɗa kai da su.”
6Ubangiji ya ce,
“Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi.
Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare.
Za a kashe su da takobi tun daga Migdol zuwa Sewene.
7Za ta zama kufai fiye da sauran ƙasashe,
Biranenta kuma za su zama kufai, marar amfani, fiye da sauran birane.
8Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji,
Sa'ad da na kunna wuta cikin Masar,
Na kuma kakkarya dukan masu taimakonta.
9“A ranan nan manzanni masu sauri za su fito daga wurina a jiragen ruwa, su tsoratar da Habashawa, ba zato. Azaba za ta auko a kansu a ranar hallakar Masar. Ga ta nan, ta zo.”
10Ubangiji Allah ya ce,
“Zan sa dukiyar Masar ta ƙare
Ta hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila,
11Shi da mutanensa,
Mutane mafi bantsoro a cikin sauran al'umma,
Za a kawo su don su hallakar da ƙasar.
Za su zare takubansu a kan Masar,
Su cika ƙasar da gawawwaki.
12Zan busar da Kogin Nilu,
Zan kuma sayar da ƙasar ga mugaye.
Zan sa ƙasar ta lalace
Da dukan abin da yake cikinta,
Ta hannun baƙi,
Ni Ubangiji, na faɗa.”
13Ubangiji Allah ya ce,
“Zan hallakar da gumaka
Da siffofi a Memfis.
Ba za a ƙara samun hakimi a ƙasar Masar ba,
Saboda haka zan aukar da tsoro a ƙasar Masar.
14Zan sa Fatros ta zama kufai,
Zan kunna wa Zowan wuta,
Zan kuma shara'anta No.
15Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum,
Wato kagarar Masar,
Zan datse jama'ar No.
16Zan kunna wa Masar wuta.
Felusiyum za ta sha azaba mai tsanani,
No kuwa za a tayar mata da hankali,
Za a rurrushe garukanta.
Za a tasar wa Memfis dukan yini.
17Samarin Awen da na Fi-beset
Za a kashe su da takobi,
Matan kuma za su tafi bauta.
18A Tafanes rana za ta yi duhu,
Sa'ad da na karya mulkin ƙasar Masar,
Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare,
Za a rufe ta da gizagizai.
'Ya'yanta mata kuwa za a kai su bauta.
19Ta haka zan hukunta Masar,
Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”
20A kan rana ta bakwai ga watan fari, a shekara ta goma sha ɗaya, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 21“Ɗan mutum, na karya hannun Fir'auna, Sarkin Masar, ga shi, ba za a ɗora hannun ba, don kada ya warke ya zama da ƙarfi yadda zai iya riƙon takobi.” 22Ubangiji Allah kuma ya ce, “Ina gāba da Fir'auna, Sarkin Masar, zan karya hannuwansa duka biyu, da lafiyayyen da kuma wanda na riga na karya. Zan sa takobinsa ya faɗi daga hannunsa. 23Zan watsar da Masarawa a cikin sauran al'umma, in kuma warwatsa su a ƙasashen duniya. 24Zan ƙarfafa hannun Sarkin Babila, in sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir'auna, zai yi nishi a gaban Sarkin Babila, kamar mutumin da aka yi wa raunin ajali. 25Zan ƙarfafa hannuwan Sarkin Babila, amma hannuwan Fir'auna za su shanye. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sa takobina a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai miƙe shi a kan ƙasar Masar. 26Zan watsar da Masarawa a cikin sauran al'umma, in warwatsa su a ƙasashen duniya. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”
Currently Selected:
Eze 30: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979