Fit 9
9
Mutuwar Dabbobi
1Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je ka wurin Fir'auna, ka faɗa masa cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada. 2Amma idan ka ƙi sakinsu, wato kana ta riƙonsu, 3to, hannuna zai auka wa dabbobinka cikin sauruka, da dawakai, da jakai, da raƙuma, da shanu, da tumaki, da awaki, da annoba mai tsanani. 4Zan raba tsakanin dabbobin Isra'ilawa, da na Masarawa. Ko ɗaya daga cikin dabbobin Isra'ilawa ba zai mutu ba. Na riga na sa lokacin. 5Gobe ne zan aikata al'amarin nan a ƙasar.’ ” 6Kashegari kuwa Ubangiji ya aikata al'amarin. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, na Isra'ilawa kuwa, ko ɗaya bai mutu ba. 7Sai Fir'auna ya aika, ya tambaya, ashe, ko dabba guda daga cikin na Isra'ilawa ba ta mutu ba? Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saki jama'ar ba.
Marurai
8Ubangiji kuma ya ce wa Musa da Haruna, “Dibi tokar matoya cike da tafin hannuwanku, Musa kuwa zai watsa ta sama a gaban Fir'auna. 9Tokar za ta zama kamar ƙura a dukan ƙasar Masar, ta zama marurai, suna kuwa fitowa a jikin mutum da dabba a dukan ƙasar Masar.” 10#W.Yah 16.2Sa'an nan suka ɗauko toka daga matoya, suka tsaya a gaban Fir'auna. Da Musa ya watsa ta sama, sai ta zama marurai suna ta fitowa a jikin mutum da dabba. 11Amma masu sihirin suka kāsa tsayawa a gaban Musa saboda maruran, gama suka kamu da maruran kamar sauran Masarawa. 12Ubangiji kuma ya taurare zuciyar Fir'auna har ya ƙi jin Musa da Haruna kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa wa Musa.
Ƙanƙara
13Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka je ka sami Fir'auna, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada. 14A wannan karo, ni da kaina zan kawo maka, da fādawanka, da jama'arka annoba, domin ka sani babu mai kama da ni a dukan duniya. 15Gama da ni kaina na miƙa dantsena na buge ka da jama'arka da annoba, ai, da an hallakar da ku a duniya ƙaƙaf. 16#Rom 9.17 Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana ya zama abin darajantawa a dukan duniya. 17Har yanzu kana fariya a kan jama'ata, ba ka sake su ba. 18Gobe war haka zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda Masar ba ta taɓa gani ba tun kafawarta, har zuwa yanzu. 19Yanzu fa, sai ka ba da umarni a lura da awaki, da dukan abin da yake naku wanda yake a saura, gama duk mutum ko dabba wanda ya ragu a saura, wato wanda ba a kawo shi gida ba, zai mutu sa'ad da ƙanƙarar ta zo.’ ” 20Akwai waɗansu daga cikin fādawan Fir'auna waɗanda suka tsorata saboda abin da Ubangiji ya faɗa, sai suka kawo bayinsu da dabbobinsu cikin gida. 21Amma waɗanda ba su kula da abin da Ubangiji ya faɗa ba, suka bar bayinsu da dabbobinsu a waje cikin saura.
22Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa mutum da dabba da bisa dukan itatuwan saura a dukan ƙasar Masar.” 23Sai Musa ya miƙa sandansa sama, Ubangiji kuwa ya aiko da tsawa da ƙanƙara, wuta kuwa ta bi ƙasar. Ubangiji ya sa aka yi ƙanƙara a bisa ƙasar Masar. 24#W.Yah 8.7; 16.21Ƙanƙarar tana faɗowa, wuta kuma tana tartsatsi a cikin ƙanƙara. Aka yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda ba a taɓa yi ba cikin dukan ƙasar Masar tun lokacin da ta zama al'umma. 25Ƙanƙarar ta bugi ko'ina a Masar. Dukan abin da yake cikin saura, mutum duk da dabba, da tsire-tsire duka, ƙanƙara ta buge su. Duk itatuwan da yake a saura aka ragargaza su. 26Sai dai a ƙasar Goshen inda Isra'ilawa suke, ba a yi ƙanƙara ba.
27Fir'auna ya aika, aka kirawo Musa da Haruna, ya ce musu, “Lalle a wannan karo na yi laifi, Ubangiji shi ne da gaskiya. Ni da jama'ata muke da kuskure. 28Ku roƙi Ubangiji ya tsai da tsawar da ƙanƙarar. Ni kuwa na yi alkawari zan bar ku ku tafi, ba za ku ƙara tsayawa a nan ba.”
29Musa ya ce masa, “Da fitata daga cikin birnin, zan yi addu'a ga Ubangiji, walƙiya kuwa za ta tsaya, ƙanƙara kuma ta daina, don ku sani duniya ta Ubangiji ce. 30Amma dai na sani, da kai da fādawanka, har wa yau ba ku ji tsoron Ubangiji Allah ba tukuna.”
31Rama da sha'ir suka lalace, gama sha'ir ya riga ya nuna, rama kuwa tana huda. 32Amma alkama da maiwa ba su lalace ba, gama kakarsu ba ta yi ba tukuna.
33Sai Musa ya fita daga wurin Fir'auna ya rabu da birnin. Ya yi addu'a ga Ubangiji sai walƙiya da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke. 34Da Fir'auna ya ga an ɗauke ruwa, da ƙanƙara, da kuma walƙiya, sai ya sāke yin zunubi, ya taurare zuciyarsa, da shi da fādawansa. 35Zuciyar Fir'auna ta taurare, har ya ƙi sakin Isra'ilawa kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa ta bakin Musa.
Currently Selected:
Fit 9: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979